Skip to content

Hausa Bible

Luka 6

1 Wata Ranar Hutu ta Mako Yesu da almajiransa suka bi ta gonakin hatsin alkama, sai almajiran suka karya waɗansu kan alkama suna murjewa suna ci.

2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da Koyarwar Musa ta hana a yi a Ranar Hutu ta Mako?”

3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba saˈad da shi tare da mutanensa suka ji yunwa?

4 Yadda Dawuda ya shiga gidan Allah, ya ɗauki Burodin da Aka Keɓe, ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa abin da bai kamata kowa yă ci ba sai firistoci kaɗai?”

5 Sai ya gama maganar nan da cewa, “Ai, Ɗan Mutum Ubangiji ne na Ranar Hutu ta Mako.”

6 A wata Ranar Hutu ta Mako kuma, Yesu ya shiga majamiˈa yana koyarwa. Akwai wani mutum a wurin wanda hannun damansa ya shanye.

7 Sai malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa suka zuba ido, su ga ko Yesu zai yi warkarwa a Ranar Hutu, domin su same shi da laifi.

8 Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin nan, “Tashi ka zo ka tsaya a nan.” Sai mutumin ya tashi ya zo ya tsaya a wurin.

9 Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, mene ne ya dace a yi a Ranar Hutu? A yi alheri ko a yi mugunta? A ceci rai, ko a halaka shi?”

10 Sai ya duddube su duka, saˈan nan ya ce wa mutumin, “Ka miƙa hannunka.” Shi kuwa ya miƙe hannun, sai hannunsa ya warke.

11 Sai haushi ya kama Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa sosai, suka fara magana da junansu a kan abin da za su yi da Yesu.

12 A kwanakin nan, Yesu ya je ya hau babban tudu domin yă yi adduˈa. Ya kwana yana adduˈa ga Allah.

13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya ce da su manzanni. Ga sunayensu,

14 Siman, wanda Yesu ya sa masa suna Bitrus, Andarawus ɗanˈuwan Bitrus, Yakub, Yohanna, Filibus, Bartalomi,

15 Matiyu, Toma, Yakub ɗan Halfa, Siman, wanda ake ce da shi mai kishin ƙasarsa,

16 Yahuda ɗan Yakub, Yahuda Iskariyoti, wanda ya bashe shi.

17 Sai Yesu ya sauko tare da manzanninsa, ya tsaya a wani wuri mai fili sosai, tare da mutane da yawa waɗanda suke almajiransa. A nan kuma ga mutane da yawa da suka zo daga koˈina a yankin Yahudiya, da Urushalima, da kuma yankin garuruwan Taya da Sidon waɗanda suke a bakin babbar teku.

18 Sun zo domin su ji shi, su kuma sami warkewa daga dukan cututtukansu. Aka kuma warkar da mutanen da ƙazaman ruhohi suke damunsu.

19 Kowa ya yi ƙoƙari yă taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

20 Sai Yesu ya dubi almajiransa ya ce, “Masu albarka ne, ku matalauta, gama mulkin Allah naku ne!

21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu, gama za ku ƙoshi! Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu, gama za ku yi dariya!

22 Masu albarka ne ku idan mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suna zaginku, suna cewa ku mugaye ne, saboda Ɗan Mutum!

23 “In wannan ya faru, ku yi farin ciki! Ku kuma yi rawa domin farin ciki, gama ladanku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan da suka riga ku.”

24 “Amma kaitonku, ku da kuke da arziki yanzu, gama kun riga kun ji daɗinku ko!

25 Kaitonku, ku da kuka ƙoshi yanzu, gama za ku zauna da yunwa! Kaitonku, ku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi baƙin ciki, kuna kuka!

26 Kaitonku, ku da mutane suke yabonku, gama haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

27 “Ina gaya muku, ku da kuke jina, ku ƙaunaci masu gāba da ku, ku yi wa waɗanda ba sa son ganinku alheri.

28 Ku sa wa masu zaginku albarka, ku kuma yi wa masu ba ku wahala adduˈa.

29 Idan wani ya mare ka a wannan kumatu, ka juya masa ɗayan ma. Idan wani ya ƙwace maka babbar riga, ka cire rigar cikin ma ka ba shi.

30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. Wanda kuma ya yi maka ƙwace, kada ma ka nemi a mayar maka.

31 Ku yi wa mutane abin da kuke so su yi muku.

32 “Idan kuna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarku ne kawai, yaya za ku sami albarka? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu ne!

33 Idan kuma kuna yin alheri ga masu yi muku ne kawai, yaya za ku sami albarka? Ko masu zunubi ma suna yin haka.

34 In kuma mutanen da za su iya biyanku ne kuke ba su bashi, yaya za ku sami albarka? Ko masu zunubi ma suna ba da bashi ga masu zunubi don a biya su daidai!

35 Amma ku, ku ƙaunaci masu gāba da ku, ku kuma yi musu alheri, ku ba da bashi ba da nufi sai an biya ku ba. Ta yin haka ne za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ˈyaˈyan Allah Mafi Ɗaukaka. Gama shi mai alheri ne ga mutanen da ba sa godiya da kuma mugaye.

36 Ku zama masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.

37 “Kada ku shariˈanta kowa, ku kuma ba za a yi muku ba. Kada ku hukunta kowa, ku kuma ba za a hukunta ku ba. Ku yafe wa kowa, ku kuma za a yafe muku.

38 Ku bayar, ku ma za a ba ku mudu a cike, a cika har yă yi tudu yana zuba, har a juye muku sauran a hannun riga. Gama da mudun da kuke auna wa mutane da shi, da shi za a auna muku.”

39 Yesu ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho zai iya yi wa wani makaho jagora? Idan ya yi haka, to, dukansu za su fāɗi a rami.

40 Ba ɗan makarantan da ya fi malaminsa, amma kowane ɗan makaranta wanda ya gama karatunsa, zai zama kamar malaminsa.

41 “Don me kake ganin ɗan tsinken da yake a idon ɗanˈuwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake cikin idonka ba?

42 Yaya kuma za ka iya ce wa ɗanˈuwanka, ‘Kai, ɗanˈuwana, bari in cire maka ɗan tsinken nan da yake idonka,’ bayan kuma ba ka iya ganin gungumen da yake a naka idon ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da yake cikin idonka tukuna, don ka iya gani sosai yadda za ka iya cire ɗan tsinken da yake cikin idon ɗanˈuwanka.

43 “Itace mai kyau ba ya yin ˈyaˈya marasa kyau, kuma mummunan itace ba ya yin ˈyaˈya masu kyau.

44 Ana sanin kowane itace ta irin ˈyaˈyansa. Ba yadda za a tsinke ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin itacen ƙaya.

45 Mutumin kirki yana fitar da abubuwa masu kyau daga ajiyar abubuwa masu kyau waɗanda suke a zuciyarsa. Amma mugun mutum yana fitar da abubuwa marasa kyau daga ajiyar abubuwa marasa kyau waɗanda suke a zuciyarsa. Abin da yake cikin zuciya, ai, shi yake fitowa a baki.

46 “Don me kuke ce da ni ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma kun ƙi yin abin da na ce ku yi?

47 Duk wanda ya zo wurina ya saurare ni, ya kuma yi abin da na ce yă yi, zan kwatanta muku yadda mutumin nan yake.

48 Shi kamar mutum ne wanda, da zai gina gidansa, sai ya haƙa ƙasa da zurfi, ya kuma kafa tushen ginin a kan dutse. Da aka yi ambaliyar ruwa, sai ta bugi gidan, amma ba ta iya girgiza gidan ba, saboda an gina shi da kyau.

49 Amma duk wanda ya ji maganata bai kuma yi abin da na ce yă yi ba, daidai yake da mutumin da ya gina gidansa ba tare da ya yi wa gidan nan tushe mai kyau ba. Da aka yi ambaliyar ruwa, sai ta bugi gidan, sai ya fāɗi gaba ɗaya. Fāɗuwar gidan nan kuwa ta yi muni sosai.”

Open Bible reader