Hausa Bible
Luka 4
1 Yesu ya dawo daga Kogin Yodan cike da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu kuwa ya iza shi zuwa cikin daji,
2 inda Shaiɗan ya gwada shi har kwana arbaˈin. A ƙarshen wannan lokaci, sai yunwa ta kama shi, don bai ci kome ba.
3 Sai Shaiɗan ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umarci wannan dutse yă zama burodi.”
4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake a cikin Maganar Allah cewa, “ ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”
5 Daga nan, Shaiɗan ya kai shi wani wuri mai tsayi sosai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya a cikin ɗan lokaci.
6 Shaiɗan ya ce masa, “Zan ba ka iko a kan dukan waɗannan da duk ɗaukakarsu, gama dukan waɗannan an ba ni su. Kuma zan iya bayar wa duk wanda nake so in ba shi.
7 Dukan wannan zai zama naka idan dai ka yi mini sujada.”
8 Yesu ya ce masa, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa!’ ”
9 Sai Shaiɗan ya ɗauke shi zuwa Urushalima, ya kai shi can bisa Haikali, ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan ka fāɗi ƙasa.
10 Gama a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, “ ‘Zai ba da umarni ga malaˈikunsa game da kai su tsare ka.
11 Za su kuma tare ka da hannuwansu domin kada ka buga ƙafarka a dutse.’ ”
12 Amma Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, “ ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
13 Da Shaiɗan ya gama gwada Yesu a ta kowane gefe, sai ya bar shi na ɗan lokaci.
14 Sai Yesu ya koma Galili, ikon Ruhu Mai Tsarki kuma yana tare da shi. Labarinsa ya kai koˈina a kewayen.
15 Ya yi ta koyarwa a majamiˈunsu, kowa yana ta yabonsa.
16 Daga nan sai Yesu ya zo Nazaret, inda ya yi girma. Ya shiga majamiˈa a Ranar Hutu ta Mako kamar yadda ya saba. Ya tashi zai yi karatu ke nan,
17 sai aka miƙa masa littafin annabi Ishaya. Ya kunce littafin ya nemi ya kuma sami wurin da aka rubuta cewa,
18 “Ruhun Ubangiji yana a kaina, domin ya keɓe ni in kawo wa matalauta labari mai daɗi. Ya aike ni in yi shela cewa waɗanda suke a ɗaure za a sake su, makafi za su sami ganin gari, waɗanda aka danne za su sami ˈyanci.
19 In kuma yi shelar wa kowa cewa lokaci ya yi da Ubangiji zai ceci mutanensa.”
20 Da ya gama karatun, sai ya naɗe littafin ya ba mai lura da majamiˈar, ya zauna. Dukan mutanen da suke a majamiˈar, suka zuba masa ido,
21 sai ya ce musu, “Wannan Rubutacciyar Maganar Allah ta cika a kunnenku a yau.”
22 Dukansu da suke wurin suka ji daɗinsa suna ta mamakin kalmomi masu kyau da suke fitowa daga bakinsa, suna ta tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”
23 Yesu ya ce musu, “Na sani za ku gaya mini karin maganar nan, ‘Likita, ka warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Ka yi abubuwan da muka ji ka yi a Kafarnahum a nan garinka mana.’ ”
24 Ya sāke ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da akan yarda da shi a garinsa”.
25 “Amma gaskiya ina gaya muku, a zamanin annabi Iliya, akwai matan da mazansu suka mutu da yawa a Israˈila, saˈad da ruwan sama ya ƙi zuwa har shekara uku da wata shida, aka kuma yi muguwar yunwa koˈina a ƙasar.
26 Amma ba a aiko da annabi Iliya zuwa wurin ko ɗaya daga cikinsu ba. Ai, zuwa wurin wata macen da mijinta ya mutu a Zarefat da yake a yankin Sidon ne aka aike shi.
27 A lokacin annabi Elisha kuma akwai kutare wato, masu cutar fatar jiki da yawa a Israˈila, amma ba a tsabtace ko ɗaya daga cikinsu ba, sai Naˈaman mutumin ƙasar Suriya ne kaɗai aka warkar.”
28 Da mutanen da suke cikin majamiˈa suka ji wannan magana, sai haushi ya kama su duka.
29 Suka tashi suka fitar da Yesu bayan gari, har suka kai shi kan tudun da aka gina garinsu a kai. Sun so su ture shi yă fāɗi daga kan tudun,
30 amma sai ya bi ta cikinsu ya yi tafiyarsa.
31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a cikin Galili. A nan ya shiga majamiˈa a Ranar Hutu ta Mako yana koyar da su.
32 Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin maganarsa tana da iko.
33 A cikin majamiˈar, akwai wani mutum mai ƙazamin ruhu. Sai ya tā da murya da ƙarfi ya ce,
34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu mutumin Nazaret? Ko ka zo ne ka halaka mu? Na san wane ne kai, kai ne Mai Tsarkin nan na Allah!”
35 Yesu ya tsawata wa aljanin ya ce, “Ka yi shiru, ka fita daga jikin mutumin nan!” Sai aljanin ya ɗaga mutumin, ya buga shi a ƙasa a gabansu, saˈan nan ya fita, ya bar mutumin ba wani ciwo.
36 Sai dukan mutane suka kama baki kawai, suna ce wa junansu, “Wane irin abu ne haka? Da ƙarfi da iko wannan mutum ya umarci ƙazaman ruhohi har sun fita!”
37 Wannan abin da Yesu ya yi, ya sa an baza labarinsa koˈina a ƙasar.
38 Yesu ya fita daga majamiˈar, ya tafi gidan Siman. Mamar matar Siman kuma ba ta da lafiya, zazzaɓi ya dame ta sosai. Suka roƙi Yesu yă warkar da ita.
39 Ya je ya tsaya kusa da gadonta ya umarci zazzaɓin yă bar ta. Nan take zazzaɓin ya bar ta, ta kuma tashi, ta yi musu hidima.
40 Da rana ta fāɗi, kowa da yake da aboki mai rashin lafiya da kowane irin ciwo, suka kawo su wurin Yesu. Shi kuma ya taɓa kowannensu da hannu ya warkar da su duka.
41 Aljanu kuma suka fita daga jikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma Yesu ya tsawata musu, ya hana su magana, saboda sun san cewa shi ne Almasihu.
42 Da gari ya waye sai Yesu ya bar garin ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, har suka same shi. Suka yi ƙoƙari su hana shi zuwa wani wuri kuma,
43 amma ya ce musu, “Ya kamata in kai labari mai daɗi na mulkin Allah ga waɗansu garuruwa, gama saboda wannan dalilin ne aka aiko ni.”
44 Sai ya yi ta yin waˈazi a majamiˈun yankin Yahudiya.