Skip to content

Hausa Bible

Kolosiyawa 2

1 Gama ina so ku san irin famar da nake yi dominku da mutanen da suke Lawudikiya, da kuma dukan waɗanda ba su taɓa ganina ba.

2 Sona shi ne ƙauna ta haɗa su, su kuma sami ƙarfafawa a zuciyarsu, domin su sami wadatar tabbatacciyar fahimta, domin su kai ga sanin zurfin asirin Allah, wato Almasihu da kansa ke nan.

3 A cikinsa ne dukan darajar hikima da ta sani suke a ɓoye.

4 Ina gaya muku wannan ne domin kada wani yă ruɗe ku da maganar yaudara.

5 Ko da yake a jiki ba na nan tare da ku, amma a ruhu ina nan tana tare da ku. Ina farin ciki sosai da jin yadda kuke tsaye daram, kuna kuma dagewa cikin bangaskiyarku cikin Almasihu.

6 Tun da kun yarda cewa Yesu Almasihu shi ne Ubangijinku, sai ku ci gaba da yin tafiyarku a cikinsa.

7 Kuna iya yin haka idan kun kafu sosai a cikinsa, kuna kuma gina kanku a tushen nan, kuma kuna tsayawa a kan bangaskiyarku, kamar dai yadda muka koya muku, kuna kuma yalwata cikin godiya.

8 Ku lura fa, kada wani yă kama hankalinku ta wurin ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza, waɗanda suka fito daga wurin alˈadar ˈyan Adam, bisa ga ikon ruhohi na duniya ne, ba daga Almasihu ba.

9 Gama a cikin Almasihu ne, dukan cikar Allahntaka take zaune a jikinsa.

10 Haka ma a cikinsa, kun zama cikakku, shi wanda yake mai mulki a kan mulkoki da ikoki.

11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, kaciya ba irin da ake yi da hannu ba, amma kaciyar da Almasihu ne ya yi muku, ta wurin tuɓe muku halin mutuntaka.

12 Gama saˈad da aka yi muku baftisma daidai ne da binnewarku tare da Almasihu. A cikin baftisma aka kuma tā da ku tare da Almasihu ta wurin bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tā da shi daga matattu.

13 A dā ku matattu ne saboda zunubi da kuma saboda rashin kaciyarku ta tuɓe halinku na mutuntaka, amma Allah ya tā da ku rayayyu tare da Almasihu, tun da yake ya yafe mana dukan zunubanmu.

14 Ya yi wannan ta wurin yanke igiyar nan ta rubutacciyar shaida a kanmu cewa mun karya Koyarwa da ƙaˈidodinta. Amma Allah ya kawar da ita, har ana iya cewa ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyen Almasihu.

15 Ya ƙwace kayan yaƙi na mulkoki da ikoki, ya ba su kunya a fili ta wurin cin nasara a kansu a kan gicciye.

16 Saboda haka, kada ku bar wani yă ba ku laifi a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuma a kan rashin kiyayewar wani biki, ko Bikin Sabon Wata, ko hutu a Ranar Hutu ta Mako.

17 Waɗannan abubuwa kamar hoto ne kawai na abin da zai zo, amma Almasihu shi ne ainihin abin.

18 Saboda haka, kada ku bar wani yă raba ku da nasararku ta wurin nacewa a kan hana wa kansu jin daɗi domin neman lada, da yi wa malaˈiku sujada, da dogara ga ganin ruˈuyoyi, da kuma ɗaga kai babu dalili. Zuciyarsu ta halin mutuntaka ta sa su yi haka.

19 Ai, irin wannan mutum bai manne wa Almasihu ba, wanda shi ne kai na jiki. Gama shi yana riƙe da dukan jamaˈar masu bi, wato jikinsa, wanda yake a haɗe ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma yin girma da girman da Allah yake sawa.

20 Ga shi, kun mutu tare da Almasihu, ya kuma ˈyantar da ku daga ikokin duniyar nan. Don me kuke yin rayuwa kamar har yanzu ku na duniya ne? Don me kuke miƙa kanku ga ƙaˈidodin duniyar nan, wato,

21 kamar ƙaˈidodi masu cewa, “Kada ka yi amfani da wannan, kada ka ɗanɗana, kada ka taɓa?”

22 Irin waɗannan ƙaˈidodi kuwa sun shafi abubuwan da za su ruɓa ne, saboda an kafa su ne bisa ga ƙaˈidodi da koyarwar mutum.

23 Hakika, irin ƙaˈidodin nan suna da alamar hikima yadda sukan kawo ƙwazo cikin addinin da mutane suka ƙirƙiro, da nacewa a kan hana wa kansu jin daɗi domin neman lada, da kuma ba wa jiki wahala. Amma gaskiya, ƙaˈidodin nan ba su da wani iko wajen hana shaˈawar jiki.

Open Bible reader