Skip to content

Hausa Bible

Kolosiyawa 1

1 Daga Bulus, wanda ya zama manzon Yesu Almasihu bisa ga nufin Allah, tare da Timoti, ɗanˈuwanmu,

2 zuwa ga tsarkaka da ˈyanˈuwa masu aminci cikin Almasihu waɗanda suke zama a Kolosi. Alherin Allah Ubanmu da salamarsa su kasance tare da ku.

3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, a duk lokacin da muke adduˈa dominku.

4 Gama mun ji yadda kuka gaskata cikin Almasihu Yesu, da kuma yadda kuke ƙaunar dukan tsarkaka.

5 Dalilin da kuke yin haka kuwa shi ne, kuna sa zuciya a kan abin aka yi muku ajiyarsa a sama. Labarin sa zuciyar nan kun ji shi cikin kalmar gaskiya, wato labari mai daɗi.

6 Labari mai daɗin nan yana ta haifar da rayuwa mai kyau, yana kuma ƙara yaɗuwa cikin dukan duniya, kamar yadda ya yi a cikinku tun lokacin da kuka fara jin labarin alherin Allah, kuka kuma gane yadda yake.

7 Wannan labarin alherin Allah kuwa, Abafaras, abokinmu cikin hidima, wanda muke ƙauna, ya fara kawo muku. Shi mai aminci ne cikin hidimar Almasihu, yana kuma yin hidima a cikinku a madadinmu ne.

8 Shi ne kuma ya ba mu labarin irin ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

9 Shi ya sa tun lokacin da muka ji labarin, ba mu fasa yin adduˈa dominku ba, muna roƙon Allah yă cika ku da sanin nufinsa tare da cikakkiyar hikima ta Ruhu da fahimta.

10 Ta haka ne za ku yi tafiyar da ta cancanta da masu bin Ubangiji, kuna faranta masa rai, kuna haifar da rayuwa mai kyau cikin kowane irin aiki, kuna kuma dinga ƙaruwa cikin sanin Allah.

11 Bari Allah yă ƙarfafa ku da dukan ƙarfin da ya fito daga ƙarfinsa mai ɗaukaka, domin ku jimre a kan kowane abin da ya faru, kuna haƙuri cikin farin ciki,

12 kuna dinga gode wa Uba a kowane lokaci, gama shi ne ya sa muka isa samun rabo cikin gādon nan da ya shirya wa tsarkakansa, waɗanda suke a cikin mulkin haske.

13 Gama shi ya kuɓutar da mu daga mulkin duhu, ya kai mu mulkin Ɗansa wanda yake ƙauna,

14 wanda ta wurinsa ne muka sami fansa, wato gafarar zunubanmu.

15 Almasihu shi ne kamannin Allah wanda ba a iya gani, shi ne Ɗan fari gaban dukan halitta.

16 Gama ta wurinsa ne aka yi kome da kome, abubuwan da suke a sammai da kuma a nan duniya, da abubuwan da ake gani da waɗanda ba a iya gani, ko kujerun mulki, ko mulkoki, ko masu sarauta, ko ikoki. Dukan abubuwan da aka halitta, an halicce su ne ta wurinsa da kuma dominsa.

17 Almasihu shi ne a gaba da dukan kome, ta wurinsa ne kuma dukan halitta ta kasance a harhaɗe.

18 Shi ne kai na jiki, wato jamaˈar masu bi. Shi ne farko, shi ne kuma na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin cikin kome da kome yă zama shi ne na fari.

19 Gama ya faranta wa Allah rai yă kasance a cikinsa da cikakkiyar Allahntakarsa,

20 ta wurin Almasihu kuma yă mai da dukan halittarsa wurinsa. Wato, ta wurin zub da jinin Ɗan a kan gicciye, yă kafa zumunci tsakaninsa da dukan abubuwa waɗanda suke a sama da kuma waɗanda suke a ƙasa.

21 A dā dai kun yi nesa da Allah, har kun zama masu gāba da shi a zuciyarku masu aikata mugayen abubuwa.

22 Amma yanzu, Allah ya shirya tsakaninku da shi kansa a cikin jikin Almasihu na nama da jini ta wurin mutuwarsa. Yanzu kuma Almasihu ya miƙa ku masu tsarki, marasa laifi, marasa zargi kuma a gaban Allah.

23 Sai dai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsayawa daram a kan tushen nan. Kada kuma a jijjiga ku ku bar sa zuciyar nan da kuka samu a lokacin da kuka ji labarin nan mai daɗi. Wannan labarin da aka yi shelarsa ga kowace halitta a ƙarƙashin sama ne, ni Bulus, na zama mai hidimarsa.

24 Yanzu, ina farin ciki saboda wahalar da nake sha dominku, domin ta wurin wahalar nan zan cika abin da ya ragu na azabar da Almasihu ya sha saboda jikinsa, wato jamaˈar masu binsa.

25 Na zama mai hidimar labarin mai daɗin nan bisa ga riƙon amana daga wurin Allah saboda ku, domin in bayyana muku cikakkiyar kalmar Allah.

26 Wannan labarin da nake sanar muku, asiri ne wanda yake a ɓoye tun zamanai da tsara masu yawa, amma yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.

27 Allah ya yi nufi yă sanar wa tsarkakansa cewa waɗanda ma ba Yahudawa ba, wadatar ɗaukakar asirin nan nasu ne. Wannan asiri kuwa shi ne Almasihu, wanda yake raye a cikinku, wanda kuma shi ne sa ranku ga rabo a cikin ɗaukakarsa.

28 Shi ya sa muke sanar wa kowa game da Yesu Almasihu, muna jan kunnen kowane mutum, muna kuma koyar da waɗannan abubuwa da dukan hikimarmu domin mu miƙa kowa cikakke cikin Almasihu.

29 Saboda wannan ne ina fama ina kuma ƙoƙari da iyakar ƙarfin nan da Almasihu yake ba ni, wanda yake aiki a cikina.

Open Bible reader