Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 26
1 Daga nan sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izni ka kāre kanka.” Saˈan nan Bulus ya ɗaga hannu, ya fara magana ya ce,
2 “Lallai na yi saˈa, Sarki Agiriffa, tun da a gabanka ne zan kāre kaina yau game da duk maganganun da Yahudawa suka faɗa a kaina,
3 musamman da yake kai gwani ne cikin sanin alˈadun Yahudawa da abubuwan da suke gardama a kai. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.
4 “Dukan Yahudawa sun san irin zaman da na yi tun ina saurayi, wato tun da farko a ƙasata da kuma a Urushalima har zuwa yau.
5 Sun san ni tun tuni, har ma idan suna so za su iya ba da shaida cewa bisa ga ƙungiyar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu, na yi rayuwata a matsayin Bafarisiye.
6 Yanzu ina tsaye a gabanku domin a yi mini shariˈa saboda na sa zuciya a kan cikar alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu.
7 Alkawarin nan ne zuriyarmu goma sha biyu suka sa rai za su ga cikarsa, har suna ƙoƙari suna bauta wa Allah dare da rana. Ya sarki, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne Yahudawa suke ganin laifina fa!
8 Me ya sa a ganinku ba ya yiwuwa Allah yă tā da matattu?
9 “To, ni da kaina ma a dā na ga kamar daidai ne in yi abubuwa da yawa in hana ci gaban maganar Yesu Banazaret.
10 Abin da na yi ke nan a Urushalima, har na sami izni daga wurin manyan firistoci domin in kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma lokacin da ake kashe su ina goyon bayan haka.
11 Na kuma bi dukan majamiˈu ina hukunta su ina ƙoƙarin sa su su yi maganganun saɓo ga sunan Yesu. Gama kuma ina fushi da su sosai, sai ina ta binsu har zuwa garuruwa na waɗansu ƙasashe in tsananta musu.”
12 “Ana cikin haka ne, wata rana ina tafiya zuwa Dimashƙu, da iznin manyan firistoci da kuma takardar ikon da suka ba ni.
13 Da tsakar rana a hanya, ranka yă daɗe, na ga wani haske fiye da hasken rana ya haskaka daga sama, ya kewaye ni da abokan tafiyata.
14 Da dukanmu muka fāɗi a ƙasa, sai na ji wata murya tana ce mini da yaren Ibraniyanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Kana ba kanka wahala ne da kake gāba da ni.’
15 “Sai na ce, ‘Wane ne kai maigirma?’ “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
16 Amma tashi ka miƙe a tsaye. Na bayyana a gare ka ne in sa ka zama mai hidimata, ka kuma yi shaidar abubuwan da ka gani game da ni, da kuma abubuwan da zan bayyana maka nan gaba.
17 Zan cece ka daga mutanenka da kuma waɗanda ba Yahudawa ba. Zan aike ka zuwa wurinsu,
18 domin ka buɗe musu idanu, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma ikon Shaiɗan zuwa ikon Allah. Ta haka za su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan waɗanda suka zama masu tsarki saboda sun ba da gaskiya gare ni.’ ”
19 “Saboda haka, ya Sarki Agiriffa, ban ƙi yin biyayya da ruˈuyar nan da ta zo mini daga sama ba.
20 Na fara yi wa mutanen Dimashƙu waˈazi, saˈan nan na yi ga mutanen Urushalima da koˈina a yankin Yahudiya, saˈan nan kuma na yi wa waɗanda ba Yahudawa ba cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi abubuwan da za su nuna sun tuba.
21 Shi ne ya sa Yahudawa suka kama ni a cikin Haikali suna ƙoƙari su kashe ni.
22 Amma Allah ya taimake ni har zuwa yanzu, shi ya sa ina nan ina yin shaida ga manya da ƙanana. Ba wani abu dabam da nake faɗa, sai dai abin da annabawa da Musa suka ce zai faru,
23 wato, lallai ne Almasihu yă sha wahala, yă zama na farkon da zai tashi daga matattu domin yă kawo haske ga dukan mutane, Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba duka.”
24 Bulus yana cikin kāre kansa ke nan, sai Festus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kana hauka! Yawan karatunka ya juya maka kai!”
25 Amma Bulus ya ce, “Maigirma Festus, ba na hauka. Gaskiya nake faɗa cikin natsuwa.
26 Ai, sarki ya san alˈamuran nan, ina kuma yi masa magana ba tsoro. Na tabbata ya lura da waɗannan alˈamura duka, gama wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.
27 Sarki Agiriffa, ka gaskata da annabawa? Na sani ka gaskata.”
28 Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Wato, a ɗan gajeren lokacin nan kake so ka rinjaye ni in zama Kirista?”
29 Bulus kuwa ya ce, “Ko a ɗan gajeren lokaci, ko a dogo, ina adduˈa cewa Allah yă sa ba kai kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suke saurarona a yau, su zama kamar yadda nake, sai dai ban da sarƙar nan.”
30 Sai sarki ya tashi, haka ma gwamna da Banis, da waɗanda suke zaune tare da su.
31 Da sun fita daga wurin shariˈa suka ce wa juna, “Ai, mutumin nan bai yi wani abin da ya isa a kulle shi, ko a kashe shi ba.”
32 Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don dai mutumin nan ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Kaisar ba, da sai a sake shi.”