Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 24
1 Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya mai suna Tartulus, domin su yi ƙarar Bulus a gaban gwamna.
2 Aka shigo da Bulus, sai Tartulus ya fara kai ƙarar Bulus a gaban gwamna ya ce, “Maigirma, ta wurin hikimarka ne aka kyautata zaman jamaˈarmu, kuma saboda kana da hangen nesa, shi ya sa an yi gyare-gyare masu yawa waɗanda suka kyautata zaman jamaˈarmu.
3 Mutanenmu koˈina suna gode maka ba iyaka.
4 Amma domin kada in ɓata maka lokaci, ina roƙonka, cikin kirkinka ka saurari gajeren abin da za mu faɗa maka.
5 Muna da tabbaci cewa mutumin nan mai yawan rikici ne, yana ta kawo tashin hankali a cikin Yahudawa koˈina a cikin duniya, kuma shi ne shugaban ƙungiyar ƙaryar nan da aka ce da ita Nazarawa.
6 Har ma yana nema yă ƙazantar da Haikali, amma muka kama shi. Mun yi niyya mu hukunta shi bisa ga shariˈarmu.
7 Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu da ƙarfi da yaji,
8 ya sa masu ƙarar mutumin nan su zo gabanka. Idan kuwa ka bincike shi kai da kanka, za ka iya sani daga wurinsa dukan abubuwan da muke ƙararsa.”
9 Yahudawa ma suka goyi bayan haka, suka yarda cewa haka abin yake.
10 Da gwamna ya ba Bulus zarafi yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Zan kāre kaina da farin ciki, tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana shariˈar jamaˈar nan.
11 Ai, idan ka bincika za ka gane cewa bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima in yi sujada.
12 Waɗannan masu ƙarata kuwa ba su taɓa samuna ina muhawara da kowa ba, ko kuwa ina tā da hankalin mutane a Haikali, ko a majamiˈu, ko kuwa a cikin birnin ba.
13 Abubuwan da suke faɗa a kaina yanzu ma ba za su iya tabbatar maka ba.
14 Abu ɗaya ne na yarda da shi, shi ne ina bin Allah na kakanninmu ta Hanyar nan da waɗannan suke ce da ita ‘ƙungiyar ƙarya’, ina kuma gaskata dukan abin da yake a rubuce bisa ga Koyarwar Musa da kuma littattafan annabawa.
15 Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke yi, cewa, za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.
16 Shi ya sa kullum nake ƙoƙari a zuciyata in kasance ba ni da shakka ko wani abin damuwa a gaban Allah da mutane.
17 “To, bayan ˈyan shekaru sai na dawo Urushalima domin in kawo sadaka ga jamaˈarmu masu bukata, in kuma miƙa hadayu.
18 Ina cikin yin haka sai suka same ni a Haikali. Na gama tsabtace kaina, ba na kuwa tare da wani taro, ban kuwa tā da hankalin jamaˈa ba.
19 Amma akwai waɗansu Yahudawa daga ƙasar Asiya da suke a wurin, su ne kuwa ya kamata su zo nan gabanka su yi ƙarata idan suna da wata magana game da ni.
20 Ko kuwa bari waɗannan mutane su faɗa laifin da suka same ni da shi lokacin da na tsaya a gaban majalisa,
21 sai dai ko idan maganar nan ɗaya kawai da na faɗa a lokacin da nake tsaye a gabansu, da na ɗaga murya cewa, ‘Game da maganar tashin matattu ake yi mini shariˈa a gabanku yau.’ ”
22 Felis kuwa ya san abubuwa da ɗan dama game da Hanyar nan, sai ya tsayar da su ya ce, “Sai shugaba Lisiyas ya zo tukuna zan yanka muku shariˈa.”
23 Sai Felis ya umarci babban sojan Roma yă yi gadin Bulus, amma kada yă matsa masa da yawa, kada kuma yă hana abokansa zuwa wurinsa su biya masa bukatunsa.
24 Bayan ˈyan kwanaki, Felis tare da matarsa Durusila, wata Bayahudiya, suka zo. Sai ya aika a kawo Bulus, ya kuma saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.
25 Saˈan nan Bulus ya fara ba da bayani a kan adalci, da shan ƙarfin shaˈawar jiki, da kuma ranar hukuncin nan mai zuwa. Da jin haka sai tsoro ya kama Felis, sai ya ce wa Bulus, “Yanzu dai ka koma. Idan na sami zarafi zan kira ka.”
26 Yana sa rai Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa Felis ya yi ta kiransa a kai a kai, yana hira da shi.
27 Amma bayan shekara biyu sai Fokiyus Festus ya zama gwamna a maimakon Felis. Felis kuwa domin yana neman farin jini a gaban Yahudawa ya bar Bulus a kurkuku.