Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 12

1 A lokacin nan kuwa Sarki Hirudus ya fara tsananta wa waɗansu a cikin jamaˈar masu bi.

2 Hirudus ya sa aka kashe Yakub, ɗanˈuwan Yohanna, da takobi.

3 Da ya ga Yahudawa sun ji daɗin abin da ya yi, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru a kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti ne.

4 Da Hirudus ya kama Bitrus, ya sa shi a kurkuku a hannun sojoji goma sha shida su yi gadinsa. Yana da niyya yă kawo shi gaban jamaˈa yă hukunta shi bayan Bikin Ƙetarewa.

5 Saˈad da Bitrus yake a kurkuku, jamaˈar masu bi kuwa ta nace da yin adduˈa ga Allah saboda shi.

6 A daren nan da Hirudus yana tunani zai fitar da Bitrus idan gari ya waye, Bitrus kuwa yana ɗaure da sarƙa biyu, yana barci tsakanin sojoji biyu. Masu gadin kurkuku kuma suna bakin ƙofa suna gadi.

7 Ba labari, sai ga wani malaˈikan Ubangiji ya bayyana, wani haske kuma ya haskaka ɗakin. Saˈan nan malaˈikan ya taɓa Bitrus a gefe ya tashe shi, ya ce, “Maza ka tashi.” Sai kuma sarƙoƙin suka fita daga hannun Bitrus.

8 Malaˈikan ya ce masa, “Ka sa rigarka, ka kuma sa takalmanka.” Sai ya yi haka. Malaˈikan ya ce masa, “Yafa mayafinka ka biyo ni.”

9 Sai ya fito ya bi shi, bai san cewa abin da malaˈikan nan yake yi gaskiya ba ne, ya ɗauka ruˈuya ce yake gani.

10 Da suka wuce masu gadi na farko da na biyu, suka kai ƙofar baƙin ƙarfe ta shiga gari, ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta. Sai suka fita. Sun zo ƙarshen wani titi ke nan sai nan take malaˈikan ya rabu da shi.

11 Saˈan nan Bitrus ya komo cikin hankalinsa ya ce, “Yanzu kam na tabbata Ubangiji ne ya aiko malaˈikansa yă cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan muguntar da Yahudawa suka shirya a kaina.”

12 Da Bitrus ya gane haka, sai ya je gidan Maryamu, mamar Yohanna wanda ake ce da shi Markus, inda mutane suka taru da yawa suna adduˈa.

13 Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata yarinya mai aiki a gidan mai suna Roda ta zo ta ga ko wane ne.

14 Da ta gane muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki da gudu, ta gaya musu cewa Bitrus yana tsaye a ƙofar zaure.

15 Sai suka ce mata, “Kina hauka!” Ita kuwa ta nace cewa shi ne. Su kuwa suka ce, “To, malaˈikansa ne!”

16 Bitrus dai ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta mamaki.

17 Shi kuwa ya yi musu alama da hannu su yi shiru, saˈan nan ya bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakub da sauran ˈyanˈuwa wannan abu.” Saˈan nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18 Da gari ya waye, ba ƙaramar ruɗarwa ce ta tashi tsakanin sojojin nan ba, a kan abin da ya sami Bitrus.

19 Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, sai ya bincika daga masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Bayan wannan Hirudus ya tashi daga yankin Yahudiya, ya tafi Kaisariya ya yi ˈyan kwanaki a can.

20 A lokacin nan, Hirudus yana fushi sosai da mutanen Taya da na Sidon. Sai suka zo wurin Hirudus tare domin neman salama, suka kuma nemi goyon bayan Bilastus shugaban masu hidimar sarki, shi kuwa ya yarda yă taimake su. Saˈan nan suka tafi wurin Hirudus suka nema su shirya zamansu, gama suna dogara ne ga ƙasar sarkin nan saboda abincinsu.

21 A ranar da aka shirya, Hirudus ya sa kayansa na mulki, ya zauna a kujerar mulki, ya yi musu jawabi.

22 Da taron suka ji shi sai suka tā da murya “Ku ji wannan fa!” suna cewa, “Muryar wani allah ne, ba ta mutum ba!”

23 Nan take, sai wani malaˈikan Ubangiji ya buge shi, don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.

24 Kalmar Allah kuwa ta yi ta ci gaba, tana ta yaɗuwa.

25 Sai Barnaba da Shawulu suka dawo daga Urushalima, bayan sun cika aikin da aka ba su su yi, suka kuma zo da Yohanna wanda ake ce da shi Markus.

Open Bible reader