Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 10

1 Akwai wani mutum a Kaisariya mai suna Koneliyus. Shi wani babban sojan Roma ne na ƙungiyar sojan da ake ce da ita Ƙungiyar Italiya.

2 Shi kuwa mai bautar Allah, mai tsoronsa kuma, shi da iyalinsa duka. Yana ƙoƙari sosai wajen ba da sadaka hannu sake ga mutane, yana kuma yin adduˈa ga Allah kullum.

3 Wata rana, wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani malaˈikan Allah a fili a cikin ruˈuya, ya zo wurinsa, ya ce, “Koneliyus!”

4 Shi kuwa ya zuba masa ido cikin tsoro ya ce, “Ubangiji, mene ne?” Malaˈikan kuma ya ce masa, “Adduˈarka da sadakar da kake yi sun kai har gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5 Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su kirawo Siman, wanda ake ce da shi Bitrus.

6 Ya sauka a wurin Siman mai aikin fata, wanda gidansa yake a bakin teku.”

7 Da malaˈikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Koneliyus ya kira bayinsa biyu, da kuma wani soja mai bin Allah daga cikin waɗanda suke yi masa aiki kullum.

8 Bayan da ya faɗa musu kome duka, sai ya aike su zuwa Yoffa.

9 Washegari, kusan tsakar rana, bayin Koneliyus suna cikin tafiya, sun zo kusa da garin ke nan, sai Bitrus ya hau kan ɗakin sama domin yă yi adduˈa.

10 Yunwa ta kama shi, har ya so yă ci wani abu. Amma da yake ana cikin shirya abincin, sai ya ga ruˈuya.

11 Ya ga sama ya buɗe, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana sauko da shi ƙasa ta kwanarsa huɗu.

12 A cikinsa akwai kowace irin dabba. Akwai masu ƙafa huɗu, da dangin macizai da ƙadangaru, da tsuntsaye.

13 Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi ka yanka ka ci.”

14 Amma Bitrus ya ce, “Sam! Ubangiji, ban taɓa cin wani abin ƙazanta ko marar tsabta bisa ga doka ba.”

15 Sai ya sāke jin murya, sau na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsabtace, kada ka ce da shi mai ƙazanta.”

16 Wannan ya faru sau uku, sai nan da nan aka ɗauki abin zuwa sama.

17 Bitrus yana cikin damuwa ƙwarai a kan ko mece ce maˈanar ruˈuyar da aka nuna masa, sai ga mutanen da Koneliyus ya aiko, suna tsaye a ƙofa, sun riga sun tambayi gidan Siman.

18 Suna sallama, suna tambaya ko Siman da ake ce da shi Bitrus ya sauka a wurin.

19 Tun Bitrus yana tunani a kan ruˈuyar nan, Ruhu ya ce masa, “Ga mutum uku nan suna nemanka.

20 Tashi, ka sauka, ka bi su. Kada ka yi shakka, don ni ne na aiko su.”

21 Sai Bitrus ya sauka zuwa wurin mutanen, ya ce musu, “Ni ne kuke nema? Wane dalili ne ya kawo ku?”

22 Sai suka ce, “Wani babban sojan Roma ne, mai suna Koneliyus, ya aike mu. Shi mutumin adalci ne, mai tsoron Allah, wanda duk jamaˈar Yahudawa suke faɗin abin kirki a kansa. Shi ne wani malaˈika mai tsarki ya umarce shi yă aiko ka je gidansa, yă ji abin da za ka ce.”

23 Sai Bitrus ya shigo da su, ya ba su wurin kwana. Washegari ya tashi, suka tafi tare, waɗansu masu bi daga birnin Yoffa kuma suka raka shi.

24 Washegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Koneliyus yana sa rai za su zo, har ya kirawo ˈyanˈuwansa duka da abokansa.

25 Bitrus yana shiga gidan ke nan, sai Koneliyus ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.

26 Amma Bitrus ya sa yă tashi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma mutum ne.”

27 Bitrus yana magana da shi, sai ya shiga ya sami mutane da yawa sun taru.

28 Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun sani cewa bai kamata Bayahude yă haɗa kai ko yă ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsabta, ko mai ƙazanta.

29 Saboda haka, da aka aika in zo, ban ce aˈa ba. To, yanzu ina so in san abin da ya sa kuka kira ni.”

30 Sai Koneliyus ya ce, “Wajen kwana huɗun da suka wuce, kamar wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma, ina adduˈa a gidana, sai ga wani mutum ya tsaya a gabana. Kayan da ya sa kuwa masu haske ne sosai.

31 Mutumin ya ce, ‘Koneliyus, an amsa adduˈarka da sadakar da kake yi kuma ya zama abin tunawa ga Allah.

32 Saboda haka sai ka aika zuwa Yoffa a kirawo Siman, wanda ake ce da shi Bitrus, ya sauka a gidan Siman mai aikin fata, wanda gidansa yake a bakin teku.’

33 Shi ya sa na aika a kira ka, ka kuma kyauta da ka zo. To, ga mu duk mun taru a gaban Allah, don mu saurari duk abin da Ubangiji ya umarce ka.”

34 Sai Bitrus ya fara yi musu magana ya ce, “Lallai, na gane Allah ba ya nuna bambanci,

35 amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace alˈumma.

36 Kun san saƙon da ya aiko wa jamaˈar Israˈila, ana ba su labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

37 Kun san yadda labarin nan ya bazu a dukan yankin Yahudiya, abin da ya fara tun daga cikin Galili, bayan baftismar da Yohanna ya yi waˈazinsa.

38 Kun san labarin Yesu Banazaret, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki, da kuma iko. Domin Allah yana tare da shi, ya dinga zagawa yana yin aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Shaiɗan ya matsa musu.

39 Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da Yesu ya yi a yankin Yahudiya, da kuma cikin Urushalima. Shi ne kuma suka kashe shi ta wurin gicciye shi a kan gungumen itace.

40 Amma Allah ya tā da shi a rana ta uku, ya kuma sa yă bayyana ga mutane.

41 Bai bayyana ga dukan jamaˈa ba, sai dai gare mu, wato mu da Allah ya zaɓa tun dā don mu zama shaidu. Mu ne muka ci, muka sha tare da shi, bayan da ya tashi daga matattu.

42 Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane waˈazi, mu kuma yi shaida cewa shi ne wanda Allah ya sa yă zama mai yi wa masu rai da matattu shariˈa.

43 Duk annabawa sun yi shaida a kansa cewa ta wurin sunansa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai.”

44 Bitrus yana cikin magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan waɗanda suke jin maganarsa.

45 Yahudawa masu bi, waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin yadda waɗanda ba Yahudawa ba su ma sun sami baiwar Ruhu Mai Tsarki.

46 Gama sun ji suna magana da yare dabam-dabam, suna ɗaukaka Allah. Saˈan nan Bitrus ya ce,

47 “Akwai wani da zai hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Ai, su ma sun sami Ruhu Mai Tsarki kamar yadda mu ma muka samu.”

48 Sai Bitrus ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Almasihu. Saˈan nan suka roƙe shi yă zauna da su na ˈyan kwanaki.

Open Bible reader