Hausa Bible
Romawa 7
1 To, ˈyanˈuwana, ku da kuke masu sanin Koyarwar Musa, za ku gane abin da zan faɗa. Koyarwar nan takan yi iko a kan mutum saˈad da mutumin yana da rai ne kawai.
2 Misali, mace mai aure, Koyarwar Musa ta ɗaure ta ga mijinta saˈad da mijinta yana da rai. Amma idan mijinta ya mutu ta sami ˈyanci ke nan daga Koyarwar nan da ta ɗaure ta da mijin.
3 Saboda haka idan ta auri wani dabam saˈad da mijinta yana da rai, za a ce da ita mai zina. Amma idan mijinta ya mutu tana da ˈyanci ke nan bisa ga Koyarwar ɗaurin aure. Idan kuwa ta sāke auri wani, ita ba mai zina ba ce.
4 ˈYanˈuwana, wannan misali ne game da ku. Ta wurin haɗa ku da jikin Almasihu kun zama matattu game da ikon Koyarwar Musa, domin ku zama nasa, wato, na wanda aka tā da shi daga matattu, domin ku haifar da rayuwa mai amfani ga Allah, kamar itacen da ya haifi ˈyaˈya masu kyau.
5 Gama yayin da muka kasance a ƙarƙashin ikon halin mutuntaka, Koyarwar ta yi ta zuga muguwar shaˈawarmu. Shaˈawar nan tamu kuma ta yi ta aiki a cikin jikinmu, kuma dukan ayyukanmu suna haifar mana mutuwa.
6 Amma yanzu kam, mun sami ˈyanci daga ikon Koyarwar Musa gama mun mutu ga abin da ya ɗaure mu. Saboda haka yanzu muna bauta wa Allah cikin sabuwar rayuwa ta Ruhunsa. Tsohuwar bautar da muka yi wa rubutattun dokoki ta wuce.
7 To, me za mu ce ke nan? Koyarwar Musa da kanta zunubi ce? Aˈa, ko kaɗan! Ai, ba yadda zan iya san abin da yake zunubi idan ba ta wurin Koyarwar ba. Da a ce Koyarwar ba ta faɗa cewa, “Kada ka yi kwaɗayin abin wani,” ba, ai, da ban san abin da ake ce da shi kwaɗayi ba.
8 Amma saboda umarnin nan, sai zunubi ya sami ƙofa yă zuga kowane irin kwaɗayi a cikina. Gama idan ba tare da Koyarwar ba, zunubi ya kwanta matacce.
9 A dā kam a raye nake, saˈad da ban san Koyarwar Musa ba, amma da na san umarnin, sai zunubi ya tashi da rai, ni kuwa na mutu.
10 Na kuwa gane cewa umarnin nan da aka nufe shi yă kawo rai, ya kuwa jawo mini mutuwa.
11 Zunubi ya sami ƙofarsa, kuma ta wurin umarnin ya ruɗe ni, ya kuma kashe ni.
12 Saboda haka Koyarwar da kanta mai tsarki ce, umarnin kuwa mai tsarki ne, mai adalci ne, nagari ne kuma.
13 Wato, ko za a ce Koyarwar nan da take mai nagarta ta jawo mini mutuwa ke nan? Ina! Ko kaɗan! Ta wurin Koyarwar nan da take mai nagarta zunubi ya jawo mini mutuwa, domin a bayyana ainihin yadda zunubi yake. Wato, ta wurin umarnin nan zunubi ya fita a fili da iyakar muninsa.
14 Mun dai sani cewa Koyarwar Musa abu ce ta ruhu. Ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bawa kawai a hannun zunubi.
15 Ban gane da abin da nake yi ba. Gama abin da nake so in yi, ba shi nake yi ba, kuma abin da nake ƙi, shi nake yi.
16 Idan kuwa abin da nake yi shi ne abin da ba na so in yi, na yarda ke nan cewa Koyarwar mai nagarta ce.
17 Wato, ba ni ne da kaina nake aikata wannan abu ba, sai dai zunubin nan da yake zama a cikina.
18 Na sani cewa ba wani abu mai kirki wanda yake zama a cikina, wato a halina na mutuntaka. Gama ina da niyyar yin abin da yake daidai, amma yin haka ya gagare ni.
19 Bāna yin nagarta wadda nake so in yi, sai dai ina ta yin muguntar da ba na so in yi.
20 To, idan ina yin abin da ba na so in yi, wannan ya nuna cewa ba ni ne nake yin wannan abu ba, sai dai zunubin nan da yake zama a cikina.
21 Sai na ga, ashe, ya zama mini ƙaˈida cewa idan ina so in yi nagarta, sai in ga mugunta tare da ni.
22 Gama a ciki-cikin zuciyata, na amince da Koyarwar Allah,
23 amma a cikin gaɓoɓina ina ganin wata ƙaˈida dabam wadda take yaƙi da ƙaˈidar da hankalina ya ɗauka. Wannan kuwa ta ɗaure ni ga ƙaˈidar nan ta zunubi wadda take zama a cikin gaɓoɓina.
24 Kaitona! Abin tausayi ne ni! Wane ne zai cece ni daga jikin nan mai kai ga mutuwa?
25 Godiya ta tabbata ga Allah gama ya cece ni ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Saboda haka ni da kaina Koyarwar Allah nake bauta wa da hankalina, amma da halina na mutuntaka kuwa, ƙaˈidar zunubi nake bauta wa.