Skip to content

Hausa Bible

Romawa 5

1 Saboda haka tun da yake mun sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin bangaskiya, muna da salama da Allah ke nan ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

2 Ta wurinsa ne muka sami shiga alherin nan da muke zama a ciki ta wurin bangaskiyarmu. Muna kuma yin farin ciki saboda muna sa zuciya cewa za mu zama masu tarayya cikin ɗaukakar Allah.

3 Ba haka kaɗai ba, har muna farin ciki cikin wahalolinmu, saboda mun san cewa wahala takan jawo jimrewa,

4 jimrewa takan jawo halin kirki, halin kirki kuma yakan jawo sa zuciya.

5 Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan, gama Allah ya zuba ƙaunarsa cikin zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da Allah ya ba mu.

6 Gama a daidai lokaci, a saˈad da ba mu iya taimakon kanmu ba, Almasihu ya mutu saboda mu, mu marasa halin Allah.

7 Da kyar ne wani yă mutu saboda mutum mai adalci, ko da yake wataƙila wani yana iya yin ƙarfin hali yă mutu saboda mutum mai halin kirki.

8 Amma Allah ya tabbatar mana yawan ƙaunarsa, da yake tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu saboda mu.

9 To, tun da yake mun sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin jinin Almasihu, balle fa yanzu, ai, za a cece mu daga fushin Allah ta wurin Almasihu.

10 To, da yake lokacin da muke masu gāba da Allah ne aka shirya tsakaninmu da Allah ta mutuwar Ɗansa, balle fa yanzu da an riga an shirya tsakaninmu da Allah, za a cece mu ta wurin rayuwar Ɗan ke nan.

11 Fiye da haka, har muna farin ciki saboda abin da Allah ya yi ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne aka shirya tsakaninmu da Allah.

12 To, kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shafi dukan ˈyan Adam, gama kowa ya yi zunubi.

13 Kafin a ba da Koyarwar Musa, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a yin lissafin zunubi inda babu Koyarwa.

14 Duk da haka mutuwa ta yi mulki a kan mutane duka daga zamanin Adam zuwa zamanin Musa, har ma ta yi iko a kan waɗanda zunubansu ba na karya doka ba ne kamar yadda na Adam ya kasance. Adam kuwa kwatancin wanda yake kyautar Allah mai zuwan nan.

15 Amma kyautar da Allah ya bayar ta wurin mai zuwan nan dabam take ƙwarai da karya dokar da Adam ya yi. Ga shi, karya doka ta mutum ɗayan nan ta jawo wa mutane da yawa mutuwa. Amma alherin Allah ya fi yawa, har kyautarsa da ya yi ta wurin alherin mutum ɗayan nan, wato Yesu Almasihu, ta sa babbar albarka ta yalwata ga mutane da yawa.

16 Ƙwarai kuwa, kyautar Allah dabam take da zunubin mutum ɗayan nan. Gama hukuncin da ya bi bayan zunubin nan shi ne hukuncin mutuwa, amma kyautar da Allah ya bayar, ita ce ta jawo mana shariˈar marar laifi a gabansa, ko da yake mun yi zunubi da yawa.

17 Ta wurin zunubin mutum ɗaya, wato Adam, mutuwa ta yi mulki a kan kowa, amma wannan yin mulki ba kome ba ne idan an gwada shi da wanda mutum ɗaya, wato Yesu Almasihu ya kawo ga masu karɓar alherin Allah da kyautarsa ta zaman adalci a gabansa. Ta wurinsa ne za su yi mulki cikin rayuwa.

18 Saboda haka, kamar yadda karya doka ta mutum ɗaya ta jawo hukuncin mutuwa a kan kowa, haka kuma aikata adalci na mutum ɗaya ya kawo albarka ga kowa, wato samun zaman marar laifi a gaban Allah da kuma sabon rai.

19 Kamar yadda mutane da yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma mutane da yawa za su zama masu adalci ta wurin biyayyar mutum ɗaya.

20 Dalilin da aka shigo da Koyarwar Musa shi ne domin laifi yă fito a fili. Amma saˈad da zunubi ya ƙaru, sai alherin Allah yă fi ƙaruwa,

21 domin kamar yadda zunubi ya yi mulkinsa ta wurin mutuwa, haka kuma alherin Allah yake mulkinsa yanzu ta wurin adalci, domin yă kai mu ga rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Open Bible reader