Hausa Bible
Romawa 4
1 To, me za mu ce game da Ibrahim, kakan kakanninmu bisa ga jiki? Mene ne ya fahimci game da zancen bangaskiya?
2 Idan Ibrahim ya sami zaman marar laifi a gaban Allah ta ayyukansa ne yana da abin da zai yi taƙama da shi ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba.
3 Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Saboda Ibrahim ya ba da gaskiya ga Allah, sai Allah ya lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
4 Mutumin da yake yin aikin lada, albashinsa ba kyauta ba ne, ladan aikinsa ne.
5 To, mutumin da bai dogara ga ayyukansa ba, amma ya dogara ga Allah wanda shi ne yake sa marasa halin Allah su sami zaman marasa laifi a gare shi, za a ɗauki bangaskiyar mutumin nan kamar adalcinsa ke nan.
6 Wannan shi ne abin da Dawuda yake nufi da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya ce da shi mai adalci, ba ta dalilin ayyukan da mutumin ya yi ba cewa,
7 “Mai albarka ne mutumin da aka gafarta masa zunuban gangancinsa, wanda aka yafe masa zunubansa.
8 Mai albarka ne mutumin da Ubangiji bai lissafta laifofinsa ba.”
9 Wannan albarka ta shafi masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da arna marasa kaciya? Ai, abin da muke faɗa daga cikin Rubutacciyar Maganar Allah ne cewa, “Ga Ibrahim aka lissafta bangaskiyarsa adalci.”
10 To, a wane lokaci ne aka ce da shi mai adalci? Bayan da aka yi masa kaciya ko tun ba a yi masa ba? Ai, tun ba a yi masa kaciya ba ne.
11 Amma da ya karɓi alamar kaciya, wannan ta zama alamar shaida game da adalcin da yake da shi bisa ga bangaskiyarsa, tun ba a yi masa kaciya ba. Saboda haka Ibrahim ya zama uban masu ba da gaskiya ga Allah, domin a lissafta su masu adalci ne, ko da yake ba su da kaciya.
12 Haka ma Ibrahim ya zama uba ga masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba, amma har ma suna bin misalin irin bangaskiyar da Ibrahim yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba.
13 Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa cewa zai ci gādon duniya, ai, ba ta wurin Koyarwar Musa aka yi masa ba, sai dai ta adalcin nan da ake samu ta wurin bangaskiya.
14 Gama idan masu bin Koyarwar Musa su ne waɗanda za su ci gādon duniya, ai, bangaskiyar mutum ta zama banza, kuma alkawarin Allah ya zama wofi ke nan.
15 Gama Koyarwar takan jawo fushin Allah ne, amma inda babu doka, ba yadda za a yi rashin biyayya.
16 Saboda haka, a kan bangaskiya ne alkawarin nan ya dogara. Wannan kuwa domin yă zama bisa ga alherin Allah, domin kuma a tabbatar da shi ga dukan zuriyar Ibrahim, wato, ba ga waɗanda suke ƙarƙashin Koyarwar Musa kaɗai ba, amma har ga waɗanda suke ba da gaskiya yadda Ibrahim ya yi. Ibrahim kuwa shi ne babanmu duka.
17 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka ka zama uban kabilu masu yawa.” Wato, an tabbatar da alkawarin nan. Ibrahim ubanmu ne a gaban Allah wanda ya ba da gaskiya gare shi, wanda kuma shi ne mai ba da rai ga matattu. Shi ne kuma mai ikon kiran abubuwan da ba su kasance ba su kasance.
18 Ko da yake sa zuciyar Ibrahim ta zama kamar a banza ne, duk da haka ya ci gaba da sa zuciya, yana ba da gaskiya har ya zama “uban kabilu masu yawa.” Wannan kuwa bisa ga alkawarin da aka yi masa ne, cewa “haka zuriyarka za su yi yawa.”
19 A lokacin kuwa Ibrahim yana da shekara wajen ɗari ne, amma bai yi sanyi cikin bangaskiyarsa ba, ko da yake yana ganin yadda ƙarfin jikinsa ya ƙāre don tsufa, da kuma yadda Saratu ta wuce lokacin da za ta iya haifuwa.
20 Bai yi shakkar alkawarin Allah ta nuna rashin bangaskiya ba, amma ya ƙara ƙarfi cikin bangaskiyarsa, yana ɗaukaka Allah.
21 Ya kuma kasance da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika alkawarinsa.
22 Shi ya sa aka lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi.
23 Wannan magana mai cewa, “aka lissafta bangaskiya adalci ne a gare shi,” ba saboda shi kaɗai ne aka rubuta ba.
24 Amma an rubuta wannan magana saboda mu, mu ma, mu da Allah zai lissafta mu masu adalci, wato mu da muka ba da gaskiya ga wanda ya tā da Yesu Ubangijinmu daga matattu.
25 Saboda zunubanmu ne aka ba da Yesu ga mutuwa, kuma an tā da shi da rai domin mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah.