Hausa Bible
Romawa 3
1 To, ina amfani na cewa kai Bayahude ne? Ina ribar kaciya?
2 Akwai kam, ta kowace hanya! Da farko, su Yahudawa ne Allah da kansa ya ba su amanar kalmar nan da take ta Allah.
3 Amma idan waɗansunsu sun nuna rashin bangaskiya fa? Rashin amincinsu zai sa amincin Allah yă zama banza ke nan?
4 Ina! Ko kaɗan! Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum mai ƙarya ne. Kamar yadda yake a rubuce cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Domin a tabbata maganarka gaskiya ce, ka kuma sha kan kowa idan ana yin bincike a kanka.”
5 To, idan rashin adalcinmu ya zama hanyar bayyana adalcin Allah fa, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah marar adalci ne in ya hukunta mu? Ina dai yin magana yadda ɗan Adam zai yi ne.
6 Ina! Ko kaɗan! In haka ne, ta yaya Allah zai yi shariˈar duniya?
7 Idan rashin gaskiyata ya sa gaskiyar Allah ta fita a fili sosai, ya kuma zama abin ƙara ɗaukakar Allah, to, don me har yanzu za a hukunta ni a kan cewa ni mai zunubi ne?
8 In haka ne, ba sai mu ci gaba da yin mugunta domin yă zama hanyar samun nagarta ba? Waɗansu mutane kuwa masu maganar ɓata sunanmu suna cewa wai haka muke faɗa. Za a hukunta waɗannan kamar yadda ya yi daidai a yi musu.
9 To, yaya ke nan? Ko mu Yahudawa mun fi sauran mutane ne? Ina! Ko kaɗan! Mun riga mun nuna cewa da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba duka suna da laifi, kuma duka suna ƙarƙashin ikon zunubi.
10 Kamar yadda yake a rubuce cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya.
11 Babu wani mai ganewa, ko wani mai neman Allah.
12 Duk sun juya wa Allah baya, sun zama marasa amfani gaba ɗaya. Babu wani mai aikata nagarta, babu, ko ɗaya.
13 Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, harsunansu sun zama kayan ruɗu. Maganganunsu kamar dafin mugun maciji.
14 Bakinsu cike suke da baƙar magana da zage-zage.
15 Sukan yi saurin zub da jini,
16 duk inda suka bi, sai halaka da baƙin ciki.
17 Ba su kuwa san hanyar salama ba.
18 Babu ko tsoron Allah a idanunsu.”
19 Mun dai sani cewa duk abin da Koyarwar Musa take faɗa, tana faɗa wa waɗanda suke ƙarƙashinta ne. Wannan ya kasance haka don a hana duk masu neman hujja, a kuma nuna cewa dukan duniya a ƙarƙashin hukuncin Allah take.
20 Gama ba wanda zai sami zaman marar laifi a gaban Allah ta hanyar kiyaye abin da Koyarwar ta ce a yi. Abin da Koyarwar take yi shi ne ta nuna wa mutum zunubinsa.
21 Amma yanzu kam an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah dabam. Wannan adalci kuwa ba ta wurin Koyarwar Musa ake samunsa ba, ko da yake Koyarwar Musa da littattafan annabawa sun ba da shaida game da shi.
22 Adalcin nan wanda daga wurin Allah yake, ana samunsa ne ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu, Allah ya ba da adalcin nan ga dukan masu ba da gaskiya. Ba kuwa wani bambanci,
23 gama kowa ya yi zunubi, kuma kowa ya kāsa kai ga darajar Allah.
24 Amma bisa ga alherin da Allah ya yi wa kowa a kyauta, kowa ya sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.
25 Allah ya miƙa Yesu yă zama hadaya ta ɗaukar alhakin zunubanmu, domin ta wurin jinin hadayarsa za a gafarta wa mutane zunubansu ta wurin bangaskiyarsu. Allah ya yi wannan domin yă nuna adalcinsa, don a cikin haƙurinsa ya ƙyale zunuban da aka yi a dā.
26 Ta haka Allah ya nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda shi da kansa mai adalci ne, kuma yana sa duk mai ba da gaskiya ga Yesu yă sami zaman marar laifi a gaban Allah.
27 To, a kan mene ne za mu yi taƙama? Ai, ba wani abu! Ta wane dalili aka kawar da taƙama? Ta hanyar kiyaye Koyarwar Musa? Aˈa, sai dai ta bangaskiya.
28 Gama mun amince cewa ta wurin bangaskiya ne akan sami zaman marar laifi a gaban Allah, ba ta wurin bin ayyukan Koyarwar Musa ba.
29 Ko kuwa Allah, Allah na Yahudawa ne, su kaɗai? Ashe, ba na mutanen da ba Yahudawa ba ne kuma? Ƙwarai kuwa, shi ma na waɗanda ba Yahudawa ba ne kuma,
30 gama Allah ɗaya ne. Zai sa masu kaciya su sami zaman marasa laifi a gare shi ta wurin bangaskiya, haka ma marasa kaciya za su sami zaman marasa laifi ta wurin wannan bangaskiya.
31 Shin, mun kawar da Koyarwar Musa ke nan bisa ga wannan bangaskiya? Ko kaɗan! A maimakon haka, tabbatar da ita ne muke yi.