Skip to content

Hausa Bible

Romawa 13

1 Dole ne kowa yă yi biyayya ga shugabannin gwamnati, gama babu wani ikon shugabanci sai dai daga wurin Allah. Kuma duk masu ikon shugabancin da muke da su, Allah ne ya kafa su.

2 Saboda haka duk wanda ya ƙi yin biyayya ga shugabannin gwamnati, ya ƙi yin biyayya da abin da Allah ya kafa ne. Masu aikata haka kuwa za su jawo wa kansu hukunci ne.

3 Gama shugabanni ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke yin abin da yake mugu. Kana so ka rabu da tsoron mutumin da yake da ikon shugabanci? To, sai ka aikata abin da yake daidai, shi kuwa zai yabe ka,

4 gama shi mai hidimar Allah ne saboda amfaninka. Amma idan kai mai yin mugunta ne, sai ka ji tsoro, domin ba a banza ne shugaban nan yake riƙe da takobin hukunci ba. Shi mai hidimar Allah ne, kuma ta wurinsa fushin Allah yakan tabbata domin a hukunta mai mugunta.

5 Saboda haka dole ne ku yi biyayya ga shugabannin gwamnati. Ba don ku guje wa fushin Allah kaɗai ba, amma don tunaninku yă kasance babu laifi.

6 Wannan ne kuma ya sa kuke biyan haraji, don shugabannin gwamnati maˈaikatan Allah ne waɗanda suke ba da duk lokacinsu saboda aikin shugabanci.

7 Ku biya wa kowa duk abin da yake binku. Idan harajin kanku ne ya kamata ku biya, sai ku biya, idan ma harajin kayanku ne, sai ku biya. Ku ji tsoron wanda ya isa a ji tsoronsa, ku kuma girmama wanda ya isa a girmama shi.

8 Kada ku riƙe hakkin kowa, sai dai hakkin nan wanda ya zama muku dole ku yi, wato, hakkin ƙaunar juna, gama wanda yake ƙaunar wani ya cika Koyarwar Musa ke nan.

9 Waɗannan umarnai, wato, “Ba za ka yi zina ba, ba za ka yi kisan kai ba, ba za ka yi sata ba, ba za ka yi kwaɗayi ba,” da duk sauran umarnan da ake da su, duk sun sami cikawa cikin maganar nan da ta ce, “Ka ƙaunaci kowa kamar kanka.”

10 Idan kana ƙaunar wani, ba za ka taɓa yi masa mugunta ba. Saboda haka ƙauna ita ce cikawar Koyarwar.

11 To, ku aikata wannan domin kun gane irin zamanin da muke ciki. Lokaci ya yi da za ku tashi daga barcinku, don lokacin da za a cece mu ya yi kusa yanzu fiye da a lokacin da muka tuba.

12 Dare ya kusan ƙārewa, kuma sauran lokaci kaɗan gari yă waye. Saboda haka bari mu watsar da ayyukan da suke na duhu, mu sa kayan yaƙinmu na haske.

13 Bari mu yi rayuwa ta kirki yadda ya dace da waɗanda suke zama a cikin haske, ba tare da bukukuwan shaye-shaye, da buguwa, da halin lalata, da halin neman jin daɗi na rashin kunya, da faɗa, da kuma kishi ba.

14 A maimakon haka sai ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuma ku yarda da halin mutuntakar da zai bi da ku bisa ga muguwar shaˈawarsa.

Open Bible reader