Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 8

1 Da Yesu ya sauko daga tudun, mutane da yawa suka bi shi.

2 Sai wani mai cutar fatar jiki, ya zo wurinsa ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, idan ka yarda kana iya ka tsabtace ni in zama marar ƙazanta.”

3 Sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa shi yana cewa, “Na yarda, na tsabtace ka, ka zama marar ƙazanta.” Nan da nan cutar fatar jikinsa ta warke.

4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura fa, kada ka faɗa wa kowa abin da ya faru, amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, ka kuma ba da baiko yadda Koyarwar Musa ta ce. Ka yi haka domin a tabbatar wa jamaˈa cewa ka warke.”

5 Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani babban sojan Roma ya zo wurinsa yana roƙonsa yana cewa,

6 “Ubangiji, mai yi mini hidima yana kwance a gida, ba ya iya motsi ma, yana shan wahala sosai.”

7 Yesu kuwa ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”

8 Sai babban sojan Roman ya amsa ya ce, “Ubangiji, ban isa ka zo gidana ba, amma ka yi magana kawai, shi mai yi mini hidimar zai warke.

9 Gama ni ma a ƙarƙashin ikon wani nake, kuma ina da sojoji a ƙarƙashina, nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai yă zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”

10 Da Yesu ya ji haka sai ya yi mamaki, sai ya ce wa masu binsa, “Hakika ina gaya muku, a cikin Israˈila ban taɓa samun mai bangaskiya mai ƙarfi kamar wannan ba.

11 Ina gaya muku, da yawa cikin masu bangaskiya irin wannan za su zo daga gabas da yamma su zauna su ci biki tare da Ibrahim da Ishaku da Yakub a mulkin sama.

12 Amma waɗanda ya kamata su zama mutanen Allah, suka kuwa ƙi, za a jefa su a cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

13 Sai Yesu ya ce wa babban sojan Roman, “Ka je, za a yi maka bisa ga bangaskiyarka.” Nan da nan mai yi masa hidimar ya warke.

14 Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga mamar matar Bitrus a kwance, zazzaɓi yana damunta.

15 Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin kuwa ya bar ta, sai ta tashi ta yi masa hidima.

16 Da yamma ta yi, mutane suka kawo wa Yesu masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da aljanun ta wurin yin magana kawai. Ya kuma warkar da duk marasa lafiya.

17 Ya yi wannan domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗauki cututtukanmu, ya kawar da duk rashin lafiyarmu.”

18 Da Yesu ya ga babban taron mutane kewaye da shi, sai ya sa a haye zuwa wancan gefen tekun.

19 Sai wani malamin Koyarwar Musa ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”

20 Sai Yesu ya ce masa, “Karnukan daji suna da ramukansu, tsuntsaye kuma suna da wurin kwanansu. Amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

21 Wani daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, bari in je in binne babana tukuna.”

22 Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni, bari matattu su binne ˈyanˈuwansu matattu.”

23 Da ya shiga jirgin ruwa, sai almajiransa suka bi shi.

24 Sai babban hadari mai iska ya taso a tekun har ruwan yana tashi yana shiga cikin jirgin, amma Yesu yana nan yana barci.

25 Sai suka je suka tashe shi suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu halaka!”

26 Sai ya ce musu, “Don me kuka ji tsoro haka, ya ku masu ƙaramar bangaskiya?” Sai ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma tekun, sai wurin duk ya yi tsit!

27 Mutane suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska ma da teku suna yi masa biyayya?”

28 Da Yesu ya kai ɗaya hayin, zuwa yankin Garasinawa, sai mutum biyu masu aljanu suka fito daga wurin da ake binne mutane suka sadu da shi. Sun zama abin tsoro sosai har ma ba mai iya bin wannan hanyar.

29 Nan da nan sai suka yi ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, ya Ɗan Allah? Ko ka zo ne domin ka ba mu wahala tun kafin lokaci yă yi?”

30 Gaba kaɗan kuwa akwai wani babban garken aladu suna kiwo.

31 Aljanun suka roƙe shi suka ce, “Idan ka fitar da mu, ka sa mu shiga cikin garken aladun nan.”

32 Sai ya ce musu, “To, ku tafi.” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, sai garken aladun gaba ɗaya suka tashi a guje suka gangara, suka fāɗi cikin tekun, suka mutu cikin ruwan.

33 Makiyayan aladun kuwa suka gudu, da suka shiga gari sai suka ba da labarin abin da ya faru da masu aljanun.

34 Sai duk mutanen garin suka fito domin su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi yă bar yankinsu.

Open Bible reader