Hausa Bible
Matiyu 26
1 Da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa duka, sai ya ce wa almajiransa,
2 “Kun san Bikin Ƙetarewa ya rage sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”
3 Sai manyan firistoci da shugabannin mutane suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.
4 Suka yi shawara su kama shi a ɓoye su kashe shi.
5 Amma suka ce, “Ba dai a lokacin bikin ba, domin kada mutane su tā da rikici.”
6 To, da Yesu yana Betani a gidan Siman, wanda dā mai cutar fatar jiki ne,
7 sai wata mace ta zo wurin Yesu da ˈyar kwalabar da aka yi da dutsen onis cike da man ƙanshi mai tsada sosai. A lokacin da yake cin abinci, sai ta zuba masa man a kai.
8 Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce wa junansu, “Ai, wannan ɓarna ce.
9 Gama da an sayar da man nan da an sami kuɗi mai yawa an ba talakawa.”
10 Amma tun da yake Yesu ya san abin da suke faɗa sai ya ce musu, “Don me kuke damun macen nan? Ai, abu mai kyau ne ta yi mini.
11 Masu bukata suna tare da ku kullum, amma ba kullum ne nake tare da ku ba.
12 Zuba mini man nan da ta yi kuwa tana shirya ni ne domin binnewa.
13 Hakika ina gaya muku, duk inda za a yi shelar labari mai daɗin nan, a duniya duka, za a dinga faɗin abin da macen nan ta yi don tunawa da ita.”
14 Sai ɗaya daga cikin sha biyun, mai suna Yahuda Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci,
15 ya ce, “Me za ku ba ni, idan na ba ku shi?” Suka ba shi kuɗin azurfa talatin.
16 Tun daga lokacin nan ya fara neman hanyar da zai ba da Yesu.
17 To, a ranar farko ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce masa, “Ina kake so mu shirya maka ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18 Ya ce, “Ku je cikin gari wurin wani mutum, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacinsa ya yi kusa, zai ci Bikin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ”
19 Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya ce su yi, suka kuma shirya abincin Bikin Ƙetarewa.
20 Da yamma ta yi, sai ya zauna domin yă ci abinci tare da almajiransa sha biyu.
21 Suna cikin cin abincin ke nan sai Yesu ya ce musu, “Hakika ina gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni.”
22 Sai suka damu sosai, suka fara tambayarsa da ɗaya-ɗaya suna cewa, “Anya, ni ne, Ubangiji?”
23 Sai ya amsa ya ce, “Wanda yake cin abinci a kwano ɗaya tare da ni, shi ne zai ba da ni.
24 Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka rubuta a cikin Maganar Allah game da shi. Amma kaiton wanda zai ba da Ɗan Mutum! Zai fiye wa mutumin nan da ma ba a haife shi ba.”
25 Sai Yahuda wanda ya bashe shi ya ce, “Malam, ko ni ne?” Yesu ya ce masa, “Kai ma ka faɗa.”
26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya burodin ya ba almajiransa ya ce, “Ku karɓa ku ci, wannan jikina ne.”
27 Sai ya ɗauki kwaf na ruwan inabi. Bayan da ya yi godiya ga Allah, sai ya ba su ya ce, “Dukanku ku sha.
28 Gama wannan jinina ne na cikar yarjejeniyar, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.
29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba, sai dai a ranar nan da zan sha wani sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30 Da Yesu da almajiransa suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Tudun Itatuwan Zaitun.
31 Sai Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku gudu ku bar ni a daren nan, don abin da zai faru da ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuma za su watse.’ ”
32 “Amma fa bayan an tashe ni daga matattu, zan riga ku zuwa Galili.”
33 Sai Bitrus ya ce masa, “Ko dukansu sun gudu domin abin da zai faru da kai, ni ba zan gudu ba sam.”
34 Sai Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina gaya maka, a daren nan, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musūn sanina har sau uku.”
35 Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni, ba zan yi musūn saninka ba.” Haka ma dukan almajiran suka ce.
36 Saˈan nan Yesu da almajiransa suka je wani wurin da ake ce da shi Getsemani, wato, wurin matsa ˈyaˈyan zaitun. Ya ce wa almajiran, “Ku zauna a nan, zan je can in yi adduˈa.”
37 Sai ya tafi da Bitrus da ˈyaˈyan nan na Zabadi guda biyu wato, Yakub da Yohanna, sai ya fara baƙin ciki da damuwa sosai,
38 ya kuma ce musu, “Baƙin cikin da yake a raina zai iya kashe ni. Ku zauna a nan, ku yi tsaro tare da ni.”
39 Da ya je gaba kaɗan sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa ya yi adduˈa ya ce, “Ubana, idan zai yiwu, ka ɗauke mini kwaf na wahalar nan. Duk da haka dai, ba abin da nake so za a yi ba, sai dai abin da kake so.”
40 Ya dawo wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ba ko na awa guda?
41 Ku yi tsaro, ku kuma yi adduˈa domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Lallai ruhu ya yarda, amma jikin ba ƙarfi.”
42 Sai ya sāke komawa sau na biyu, ya je ya yi adduˈa ya ce, “Ubana, idan wannan wahalar ba za ta wuce ba sai na sha ta, bari a aikata nufinka.”
43 Ya sāke dawowa ya same su suna barci, don idanunsu sun cika da barci.
44 Sai ya sāke barinsu, ya je ya yi adduˈa sau na uku, ya sāke faɗa maganar da ya yi a dā.
45 Sai ya dawo wurin almajiran ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? To, ga shi lokaci ya yi da za a ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.
46 Ku tashi mu tafi. Ga mai bashe ni nan, ya iso.”
47 Kafin ya rufe baki sai ga Yahuda ɗaya daga cikin sha biyun nan, tare da taron mutane da yawa, suna riƙe da takuba, da sanduna. Manyan firistoci da shugabanni ne suka aiko su.
48 To, dā ma shi mai bashe shi ɗin ya riga ya ba su alama cewa, “Wanda zan sumbace shi, shi ne mutumin. Ku kama shi.”
49 Da zuwansa sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce masa, “Sallama dai, malam!” Sai Yahuda ya sumbace shi.
50 Yesu ya ce masa, “Abokina, yi abin da ya kawo ka.” Sai mutanen suka zo suka kama Yesu suka riƙe shi.
51 Da ganin haka sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zare takobinsa, ya sari bawan babban firist, ya yanke kunnensa.
52 Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka, gama duk wanda ya ɗauki takobi, takobi ne zai kashe shi.
53 Kuna tsammani ba ni da iko in nemi taimako daga wurin Ubana, kuma nan da nan yă aiko mini da malaˈiku fiye da ƙungiyar sojoji goma sha biyu?
54 To, ta yaya ke nan za a cika abin da Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa cewa lallai wannan abu yă faru?”
55 A lokacin nan Yesu ya ce wa mutanen, “Kun fito ne da takuba, da sanduna ku kama ni sai ka ce ɗan fashi? Kowace rana ina zama a Haikali ina yin koyarwa ba ku kama ni ba.
56 Amma duk wannan ya faru ne domin a cika abin da annabawa suka rubuta a cikin Rubutacciyar Maganar Allah.” Da jin haka dukan almajiransa suka bar shi, suka gudu.
57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka kai shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Koyarwar Musa da shugabanni sun riga sun haɗu.
58 Amma Bitrus ya bi su daga nesa-nesa, har zuwa filin gidan babban firist. Ya shiga ya zauna da masu gadi domin yă ga yadda za a gama.
59 To, manyan firistoci da ˈyan majalisa, duk suka nemi shaidar ƙarya da za a yi wa Yesu domin su sami damar kashe shi.
60 Amma ba su samu ba, ko da yake waɗansu da yawa sun ba da shaidar ƙarya. Daga ƙarshe waɗansu mutum biyu suka fito
61 suka ce, “Wannan mutum ya ce wai zai iya rushe Haikalin Allah, yă kuma sāke gina shi cikin kwana uku.”
62 Sai babban firist ya tashi ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da suke bayar a kanka fa?”
63 Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah Mai Rai, ka gaya mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”
64 Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Amma ina gaya muku, daga yanzu za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun daman Mai Iko, yana kuma zuwa cikin girgije na sararin sama.”
65 Sai babban firist ya yage rigunansa saboda ɓacin rai ya ce, “Ya yi wa Allah saɓo! Wace shaida ce kuma muke nema? Kun ji ya yi wa Allah saɓo.
66 Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya isa a kashe shi!”
67 Sai suka tottofa masa miyau a fuska, suka dudduke shi, waɗansu kuma suka mammare shi,
68 suna cewa, “Yi mana annabci, in kai Almasihu ne! Faɗa wanda ya mare ka!”
69 A lokacin nan Bitrus yana zaune a cikin filin gidan, sai wata yarinya mai aiki a gidan ta zo wurinsa ta ce masa, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu mutumin Galilin nan!”
70 Amma Bitrus ya yi musū a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike magana a kai ba!”
71 Da ya fito zaure, sai wata yarinya mai aiki a gidan kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaye a wurin, “Wannan mutum yana tare da Yesu Banazaret!”
72 Bitrus ya sāke yin musū har da rantsuwa yana cewa, “Ban ma san mutumin ba.”
73 An jima kaɗan sai waɗanda suke tsaye a wurin suka zo suka ce wa Bitrus, “Ba shakka kai ma ɗayansu ne. Yadda kake magana ya tone ka.”
74 Sai ya fara laˈanta kansa, yana rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin ba!” Nan take zakara ya yi cara.
75 Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi musūn sanina sau uku.” Sai Bitrus ya fita waje ya yi kuka mai zafi.