Hausa Bible
Matiyu 23
1 Da mutane suka taru da yawa tare da almajiransa, sai Yesu ya ce musu,
2 “Malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa su ne aka ba su ikon koyar da Koyarwar Musa.
3 Saboda haka ku yi duk abin da suke koya muku, ku kuma bi, amma kada ku yi yadda suke yi, gama ba sa yin abin da suke koyarwa.
4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗaukawa, su sa wa mutane a kafaɗa, amma su kansu ba sa taimaka musu ko da ɗan yatsa.
5 Suna yin ayyukansu domin mutane su gani ne, suna ɗaura manya-manyan ƙunshin ayoyin Maganar Allah a goshinsu, suna yin dogayen ˈyan zare masu lilo a bakin rigunansu.
6 “Sun cika so a ba su wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama masu daraja a majamiˈu,
7 a kuma dinga gaishe su a kasuwa, a kuma dinga ce musu, ‘Malam’.
8 Amma ku dai, kada a ce muku ‘Malam’, domin malaminku ɗaya ne, dukanku kuwa ˈyanˈuwa ne.
9 Kada ku ce da kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya gare ku shi ne wanda yake cikin sama.
10 Kada kuma a ce da ku ‘Shugaba’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato Almasihu.
11 Wanda yake babba a cikinku sai yă zama mai yi muku hidima.
12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.
13 “Amma kaitonku, ku malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Kun rufe wa mutane ƙofar shiga mulkin sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kuna hana masu so su shiga damar shiga.
14 Kaitonku malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu suka mutu, saˈan nan kukan yi doguwar adduˈa domin a gan ku. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.
15 “Kaitonku malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Gama kukan ƙetare teku, kukan kai ƙasashe masu nisa domin samun mai tuba ɗaya. Idan kuwa kuka samu, sai ku mai da shi ɗan gidan wuta fiye da ku sau biyu.
16 “Kaitonku, makafin jagora! Kukan ce, ‘Duk wanda ya rantse da Haikali, ba damuwa, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, dole yă yi abin da ya rantse zai yi.’
17 Ku wawayen makafi! Wane ya fi girma, zinariyar, ko Haikalin da ya tsarkake zinariyar?
18 Kukan kuma ce, ‘Duk wanda ya rantse da bagade, ba damuwa, amma duk wanda ya rantse da baikon da aka sa a kan bagaden, dole yă yi abin da ya rantse zai yi.’
19 Ku makafi! Wane ne ya fi girma, baikon ne ko bagaden hadaya wanda yake tsarkake baikon?
20 Saboda haka duk wanda ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse da shi da duk abin da yake kansa ke nan.
21 Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin, ya rantse da shi, da kuma Allah wanda yake zaune a cikinsa.
22 Duk wanda kuma ya rantse da sama, ya rantse da kujerar mulkin Allah da kuma wanda yake zaune a kan kujerar mulkin.
23 “Kaitonku, malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da zakkar kayan yaji na ganye amma kun ƙyale abubuwan da suka fi muhimminci a cikin dokoki, wato gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi ba tare da ƙyale sauran ba.
24 Ku makafin jagora, kukan tace ɗan ƙarami ƙwaro, amma kukan haɗiye raƙumi!
25 “Kaitonku, malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da na kwano, amma a ciki suna cike da ayyuka marasa kyau na cuce-cuce da sonkai.
26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara wanke cikin kwaf da na kwano, domin bayansu ma yă zama da tsabta.
27 “Kaitonku, malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Kuna kamar kaburburan da aka shafa musu farin fenti, masu kyan gani daga waje, amma a ciki sai ƙasusuwan matattu da datti iri-iri.
28 Haka ku kuma kuke, a waje mutane sukan ga kamar ku masu adalci ne, amma daga ciki, cike kuke da munafunci da mugayen ayyuka.
29 “Kaitonku, malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Gama kukan gina kaburbura masu kyau domin annabawa, ku kuma yi wa kaburburan masu adalci ado.
30 Kukan ce, ‘Da muna nan kwanakin kakanninmu, da ba mu taimake su zub da jinin annabawa ba.’
31 Ta haka kuka nuna cewa ku ne ˈyaˈyan waɗanda suka kashe annabawa.
32 To, sai ku cika mudun mugayen ayyukan da kakanninku suka fara!
33 Ku macizai, ku ƙungiyar mugayen macizai! Yaya za ku iya guje wa hukuncin gidan wuta?
34 Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima, da malaman Koyarwar Musa. Za ku kashe waɗansu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majamiˈunku, kuna binsu gari-gari kuna tsananta musu.
35 Zan aiko da waɗannan mutane domin alhakin jinin masu adalci waɗanda aka kashe a duniya yă koma kanku, tun daga jinin Habila mai adalci, har zuwa na Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin Wuri Mai Tsarki da bagaden hadaya.
36 Hakika ina gaya muku, duk wannan zai faru da mutanen wannan zamani.”
37 “Ayya Urushalima, Urushalima! Masu kashe annabawa, masu jifar waɗanda aka aiko a gare ki! Sau nawa na so in tattara ku kamar yadda kaza take tattara ˈyaˈyanta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi.
38 Ga shi yanzu, an bar muku gidanku kufai!
39 Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”