Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 2

1 Ana nan saˈad da aka haifi Yesu a garin Betelehem ta yankin Yahudiya a zamanin Sarki Hirudus, sai waɗansu masu ilimin gane taurari daga gabas suka zo Urushalima. Sai suka yi tambaya suka ce,

2 “Ina sabon sarkin Yahudawa da aka haifa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, kuma mun zo ne mu yi masa sujada.”

3 Da Sarki Hirudus ya ji haka, sai hankalinsa ya tashi, haka kuma dukan mutanen Urushalima.

4 Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu.

5 Suka ce masa, “A garin Betelehem ne, ta yankin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta cewa,

6 “ ‘Ke ma Betelehem ta yankin Yahuda, ke ba ƙarama ba ce a cikin masu mulkin Yahuda. Gama daga cikinki wani mai mulki zai fito, wanda zai zama makiyayin jamaˈata Israˈila.’ ”

7 Sai Hirudus ya kira masu ilimin nan a ɓoye domin yă san daidai lokacin da suka ga tauraron.

8 Sai ya aike su zuwa Betelehem ya ce, “Ku je ku bincika mini game da ɗan yaron nan a hankali. Idan kun same shi, sai ku zo ku faɗa mini domin ni ma in je in yi masa sujada.”

9 Su kuwa da suka gama jin maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Tauraron da suka gani a gabas kuwa yana gabansu suna binsa har ya zo ya tsaya a kan inda ɗan yaron yake.

10 Da suka ga tauraron sai suka cika da murna sosai.

11 Da suka shiga gidan kuwa sai suka ga ɗan yaron da mamarsa Maryamu, suka durƙusa a gabansa, suka yi masa sujada. Saˈan nan suka kunce kayansu suka ba shi kyautar zinariya, da turaren lubban, da mur.

12 Suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam, gama Allah ya ja musu kunne a mafarki kada su koma wurin Hirudus.

13 Bayan da suka tafi sai wani malaˈikan Ubangiji ya bayyana wa Yusuf a mafarki, ya ce, “Tashi, ka ɗauki ɗan yaron nan da mamarsa ku gudu zuwa ƙasar Masar. Ku zauna a can sai na faɗa muku ku dawo, gama Hirudus zai nemi ɗan yaron domin yă kashe shi.”

14 Yusuf kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da mamarsa da dare, ya tafi ƙasar Masar,

15 ya zauna a can har sai da Hirudus ya mutu. Wannan kuwa ya faru domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”

16 Da Hirudus ya gane cewa masu ilimin nan sun yi masa wayo ne, sai ya yi fushi sosai. Ya aika a kakkashe dukan ˈyan yara maza waɗanda suke cikin Betelehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da masu ilimin nan suka faɗa masa game da yaron.

17 A lokacin ne aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya cewa,

18 “An ji murya a Rama, muryar baƙin ciki da ta kuka mai zafi, Rahila ce take kuka domin ˈyaˈyanta, ta ƙi karɓar taˈaziyya domin ˈyaˈyanta ba sa nan.”

19 Bayan mutuwar Hirudus, sai malaˈikan Ubangiji ya bayyana wa Yusuf a cikin mafarki a Masar, ya ce,

20 “Tashi ka ɗauki ɗan yaron nan da mamarsa ka koma ƙasar Israˈila, gama masu nema su kashe yaron sun mutu.”

21 Sai ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da mamarsa ya tafi ƙasar Israˈila.

22 Amma da ya ji ɗan Hirudus, wato Arkilayus ya ci gādon babansa, yana mulkin yankin Yahudiya, sai ya ji tsoro yă tafi can. Amma da aka ja masa kunne a mafarki, sai ya ratse zuwa yankin Galili.

23 Ya je ya zauna a wani garin da ake ce da shi Nazaret, domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazaret.”

Open Bible reader