Skip to content

Hausa Bible

Markus 8

1 A kwanakin nan, sai taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa. Tun da ba su da abin da za su ci, Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce musu,

2 “Ina jin tausayin jamaˈar nan, don yau kwana uku ke nan suna tare da ni, kuma ba su da abinci.

3 In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kāsa a hanya. Ga shi kuwa, waɗansunsu sun zo daga nesa.”

4 Almajiransa suka amsa, suka ce, “A daji haka, ina za a sami abincin da zai iya ciyar da mutanen nan?”

5 Yesu ya tambaye su cewa, “Burodi nawa ne kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”

6 Sai ya sa taron mutane su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya rarraba, ya yi ta ba almajiransa domin su ba mutanen, suka kuwa rarraba musu.

7 Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Ya yi godiya dominsu kuma, ya ce su ma a raba wa taron.

8 Mutanen suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar cike da kwanduna bakwai.

9 Yawan waɗanda suka ci kuwa sun kai wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su.

10 Nan da nan kuwa ya shiga jirgin ruwa da almajiransa, ya tafi yankin Dalmanuta.

11 Farisiyawa suka zo suka fara gardama da shi. Sun so su gwada Yesu, sai suka roƙe shi yă nuna musu wata babbar alamar da za ta bayyana ikonsa.

12 Sai ya yi numfashi mai zurfi, ya ce, “Don me ku mutanen zamanin nan kuke neman ganin alama? Hakika ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.”

13 Saˈan nan ya bar su, ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare zuwa wancan hayin.

14 Almajiran Yesu sun manta ba su kawo burodi ba, sai guda ɗaya kawai wanda suke da shi a jirgin ruwan.

15 Yesu ya ja musu kunne, ya ce, “Ku kula fa, kuma ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”

16 Sai almajiran suka fara taɗi da juna suna cewa, “Ko saboda ba mu da burodi ne ya faɗa haka?”

17 Da ya gane maganar da suke yi, sai Yesu ya tambaye su, “Me ya sa kuke magana a kan ba ku da burodi? Ashe, har yanzu ba ku gane ba? Ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take?

18 Kuna da idanu, ba ku gani ba? Kuna da kunnuwa, ba ku ji ba? Ba ku tuna ba ne?

19 A lokacin da na kakkarya wa mutum dubu biyar burodin nan biyar fa? Kwanduna nawa kuka ɗauka cike da abin da ya ragu?” Suka amsa cewa, “Sha biyu.”

20 “To, burodi bakwai ɗin nan da na kakkarya wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka tattara cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.”

21 Sai Yesu ya ce musu, “To, har yanzu ba ku gane maganata ba?”

22 Suka zo Betsaida, sai aka kawo wa Yesu wani makaho, aka roƙe shi yă taɓa makahon.

23 Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa miyau a idanun mutumin, ya taɓa shi domin yă warkar da shi. Sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”

24 Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa nake ganinsu, suna yawo.”

25 Sai Yesu ya sāke taɓa idanun mutumin. Mutumin ya zuba ido, idanunsa kuwa suka warke, sai ya ga kome sarai.

26 Yesu ya sallame shi yă tafi gida, ya ce masa, “Kada ka koma ta cikin gari, ko ka bi ta cikin ƙauyen.”

27 Yesu da almajiransa suka tafi, suka shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa ya ce, “Bisa ga faɗin mutane, ni wane ne?”

28 Suka amsa suka ce, “Waɗansu sun ce kai Yohanna Mai Baftisma ne, waɗansu kuwa suna cewa, kai ne annabi Iliya, waɗansu kuwa sun ce kai wani ne daga cikin sauran annabawa.”

29 Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu.”

30 Yesu ya ja musu kunne kada su gaya wa kowa labarinsa.

31 A lokacin nan, Yesu ya fara koya musu yadda Ɗan Mutum zai sha wuya iri-iri. Shugabannin jamaˈa da manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa za su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi da rai.

32 Ya faɗa wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi gefe ɗaya, ya fara tsawata masa.

33 Amma Yesu ya juya ya dubi sauran almajiran, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka rabu da ni, kai Shaiɗan! Kana tunani kamar mutum ne, ba kamar Allah ba.”

34 Saˈan nan ya kira mutanen kusa, tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai so yă bi ni, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

35 Gama duk wanda yake so yă ceci ransa, zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma saboda labari mai daɗi, zai cece shi.

36 Ina amfani mutum yă sami dukan duniya a bakin ransa?

37 Me kuma mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa?

38 Duk wanda yake jin kunyata da kunyar maganata a wannan zamani marar aminci da kuma mai yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da zai zo cikin ɗaukakar Ubansa tare da malaˈiku masu tsarki.”

Open Bible reader