Hausa Bible
Yahaya 16
1 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne domin kada ku ja baya cikin bangaskiyarku.
2 Za a kore ku daga cikin majamiˈu. Babu shakka lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku zai yi tsammani yana yin aikin Allah ne.
3 Za su yi haka ne kuwa gama ba su riga sun san Uba ko ni ba.
4 Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi, ku tuna na faɗa muku. “Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba domin ina tare da ku.
5 Amma yanzu kuwa zan tafi wurin wanda ya aiko ni. Duk da haka a cikinku ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’
6 Zukatanku sun cika da baƙin ciki domin na faɗa muku waɗannan abubuwa.
7 Amma, ina faɗa muku gaskiya, tafiyata ta fi muku amfani, domin Mai Taimakon nan ba zai zo ba, idan ban tafi ba. Amma idan na tafi zan aiko muku da shi.
8 Lokacin da Mai Taimakon zai zo, zai tabbatar wa duniya cewa tunaninsu ba daidai ba ne a kan zunubi, da a kan adalci, da kuma a kan hukunci.
9 Tunaninsu a kan zunubi ba daidai ba ne saboda sun ƙi su kafa bangaskiyarsu gare ni.
10 Tunaninsu ba daidai ba ne a kan adalci, saboda zan tafi wurin Ubana, kuma ba za ku ci gaba da ganina ba.
11 Kuma tunaninsu ba daidai ba ne a kan hukunci, saboda an riga an yanke wa mai mulkin wannan duniya hukunci.
12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗauke su a yanzu ba.
13 Amma saˈad da Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba maganar kansa zai yi ba, amma zai faɗa abin da yake ji ne kawai, zai kuma faɗa muku abubuwan da za su faru.
14 Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauki abin da na faɗa ne yă gaya muku.
15 Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce Ruhun zai ɗauko abin da na faɗa ne yă gaya muku.”
16 “Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni.”
17 Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ya ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? Kuma me yake nufi da ya ce, ‘Domin za ni wurin Uba’?”
18 Suka ci gaba da cewa, “Me yake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’? To, ba mu san abin da yake nufi ba.”
19 Yesu ya sani almajiransa suna so su tambaye shi a kan wannan magana, sai ya ce musu, “Wato, kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da na ce, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?
20 Hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da baƙin ciki, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.
21 Idan mace za ta haifu takan ji zafi sosai, domin lokacin haifuwarta ya yi. Amma idan ta gama haifuwar jariri, takan manta da zafin da ta ji saboda tana cike da murna don an haifi jariri a duniya.
22 Haka yake a gare ku. Yanzu kuna baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, saˈan nan za ku yi farin ciki, kuma ba wanda zai ƙwace muku farin cikinku.
23 A ranar nan ba za ku roƙe ni wani abu ba. Hakika, ina gaya muku, Uba zai ba ku duk abin da kuka roƙa a cikin sunana.
24 Har yanzu dai ba ku roƙi ko wani abu a cikin sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku yă zama cikakke.”
25 “Na yi amfani da misalai ne don in bayyana muku wannan. Amma lokaci yana zuwa da zan yi magana da ku a fili game da Uba, kuma ba zan ƙara moran misalai ba.
26 A ranar nan za ku yi roƙo cikin sunana. Za ku roƙi Uba da kanku, ba ni ne zan roƙa a madadinku ba,
27 domin shi Uban yana ƙaunarku da kansa, saboda kun ƙaunace ni, kun kuma ba da gaskiya cewa daga wurin Allah na fito.
28 Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, yanzu kuma zan bar duniya in koma wurin Uban.”
29 Sai almajiransa suka ce, “Yawwa! Yanzu ne fa kake magana a fili, ba da misalai ba!
30 Yanzu kam mun gane cewa ka san dukan kome. Ka iya ba da amsa kafin wani yă yi maka tambaya. Wannan ya sa mun ba da gaskiya cewa daga wurin Allah ne ka fito.”
31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe! Yanzu kun ba da gaskiya?
32 To, lokaci yana zuwa, har ma ya yi, da kowanne ɗayanku zai gudu zuwa gidansa ku bar ni ni kaɗai. Amma duk da haka ba ni kaɗai nake ba, domin Uba yana tare da ni.
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne domin a cikina ku sami salama. A cikin duniyar nan kuna shan azaba, amma ku kasance da ƙarfin zuciya gama na yi nasara a kan duniya.”