Hausa Bible
Yahaya 1
1 Tun farko akwai Kalma, Kalman kuwa tare da Allah yake, Kalman kuwa Allah ne.
2 Shi ne wanda tun farko yake tare da Allah.
3 Ta wurinsa ne aka yi dukan abubuwa, kuma babu wani abu a cikin dukan halittar da aka yi wanda ba tare da shi aka yi ba.
4 Kalman ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne haske ga mutane.
5 Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhu bai iya yă sha kansa ba.
6 Akwai wani mutum mai suna Yohanna wanda Allah ne ya aiko shi.
7 Ya zo yă shaida wa mutane gaskiya game da hasken, don ta wurin shaidarsa dukan mutane su ji labarin hasken su kuma ba da gaskiya.
8 Ba Yohanna ne hasken ba, amma ya zo ne domin yă yi shaida game da hasken.
9 Haske na gaskiya wanda yake ba da haske ga dukan mutane yana zuwa cikin duniya.
10 A dā Kalman yana cikin duniya, kuma ko da yake ta wurinsa ne aka yi duniya, duk da haka duniya ba ta san shi ba.
11 Ya zo ƙasarsa, amma mutanensa ba su karɓe shi ba.
12 Amma dukan waɗanda suka karɓe shi, suka kuma ba da gaskiya gare shi, ya ba su iko su zama ˈyaˈyan Allah.
13 Ba su zama ˈyaˈyansa ta hanya irin ta ˈyan Adam ba, ba kuwa ta wurin nufin jiki ko kuma nufin mutum ba, amma ta wurin nufin Allah ne.
14 Kalman nan ya zama mutum, ya kuwa yi wurin zamansa a cikinmu. Mun ga ɗaukakarsa, ɗaukakar da take ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Uba, yana kuma cike da alheri da gaskiya.
15 Yohanna ya yi shaida a kansa, ya kuma ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne mutumin da nake magana a kansa a lokacin da na ce, ‘Shi wanda zai zo bayana ya fi ni, gama kafin ni yana nan.’ ”
16 Saboda yawan alherinsa ne ya albarkace mu duka, yana kuma ba mu albarku babu fasawa.
17 Allah ya ba da Koyarwa ta wurin Musa, amma ya ba da alheri da gaskiya ta wurin Yesu Almasihu.
18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah. Makaɗaicin Ɗansa wanda shi Allah ne, yake kuma tare da Uba, ya bayyana mana shi.
19 Ga shaidar da Yohanna ya bayar a lokacin da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, “Wane ne kai?”
20 Yohanna bai yi musū ba, amma ya faɗa a fili cewa, “Ba ni ne Almasihu ba”.
21 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Sai ya amsa musu ya ce, “Aˈa, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya sāke amsa ya ce, “Aˈa.”
22 Sai suka ce masa, “To, wane ne kai? Ka ba mu amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu. Me kake ce da kanka?”
23 Yohanna ya amsa musu bisa ga annabcin Ishaya ya ce, “Ni ne murya mai kira a daji cewa, ‘Ku gyara hanya domin Ubangiji!’ ”
24 Sai waɗansu Farisiyawa waɗanda aka aiko
25 suka tambayi Yohanna suka ce, “Idan kai ba Almasihu ba ne, kai ba Iliya ba ne, kai kuma ba Annabin nan ba, to, don me kake yin baftisma?”
26 Sai Yohanna ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yin baftisma, amma akwai wani a cikinku, wanda ba ku san shi ba.
27 Shi ne mai zuwa a bayana, wanda ni ban isa in kunce igiyar takalminsa ba.”
28 Dukan wannan ya faru ne a Betani, a ƙetaren Kogin Yodan, inda Yohanna yake yi wa mutane baftisma.
29 Washegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wurinsa. Sai Yohanna ya ce, “Duba, ga Ɗan Rago na Allah wanda yake ɗauke da zunubin duniya!
30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Akwai wani wanda yake zuwa bayana wanda ya fi ni, gama yana nan kafin a haife ni.’
31 A dā ni ma ban san shi ba, amma na zo ina yin baftisma da ruwa ne domin a bayyana shi ga mutanen Israˈila.”
32 Sai Yohanna ya ba da wannan shaida cewa, “Na ga Ruhu yana saukowa a kamannin kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.
33 A dā ni ma ban san shi ba, sai dai Allah wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Mutumin da ka ga Ruhu yana sauko masa ya kuma zauna a kansa, to, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
34 Na kuwa ga haka ya faru, na kuma yi shaida cewa wannan mutum Ɗan Allah ne.”
35 Washegari kuma Yohanna yana tsaye a wurin tare da mutum biyu daga cikin almajiransa.
36 Sai Yohanna ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Duba, ga Ɗan Rago na Allah!”
37 Da almajiran nan biyu suka ji maganar Yohanna, sai suka bi Yesu.
38 Da Yesu ya juya ya ga suna binsa, sai ya tambaye su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Rabbi” wato, Malam, “Ina kake da zama?”
39 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku zo ku gani.” Wajen ƙarfe huɗu ke nan na yamma, sai almajiran nan suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa zauna a wurin tare da shi a dukan yini.
40 Andarawus, ɗanˈuwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin mutane biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.
41 Sai Andarawus ya fara nemi ɗanˈuwansa Siman, ya ce masa, “Ai, mun sami Almasihun,” wato, Kiristi.
42 Sai ya kai Siman a wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna? Za a ce da kai Kefas.” Ko kuma Bitrus mai maˈana “dutse”.
43 Washegari kuma Yesu ya yi niyyar zuwa Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Ka bi ni.”
44 Filibus mutumin Betsaida ne, garin su Andarawus da Bitrus.
45 Filibus ya sami Nataniyel, ya ce masa, “Mun sami mutumin da aka rubuta labarinsa a Koyarwar Musa da littattafan annabawa wato, Yesu Banazaret, ɗan Yusuf.”
46 Sai Nataniyel ya yi tambaya ya ce, “Wani abin kirki zai iya fitowa daga Nazaret kuwa?” Filibus ya ce masa, “Ka zo ka gani.”
47 Yesu ya ga Nataniyel yana zuwa wurinsa, sai ya ce, “Ku ga mutumin Israˈila na gaske, wanda ba shi da ƙarya a cikinsa.”
48 Sai Nataniyel ya tambayi Yesu ya ce, “Ta yaya ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Na gan ka tun kana gindin itacen ɓaure, kafin ma Filibus yă kira ka.”
49 Sai Nataniyel ya ce wa Yesu, “Malam, kai ne Ɗan Allah! Kai ne Sarkin Israˈila!”
50 Yesu ya ce wa Nataniyel, “Ka ba da gaskiya ne gama na gaya maka cewa na gan ka a gindin itacen ɓaure? Ai, za ka ga abubuwan da suka fi waɗannan.”
51 Sai Yesu ya ƙara faɗa musu cewa, “Hakika ina gaya muku, za ku ga sama a buɗe, malaˈikun Allah kuma suna hawa suna sauka a kan Ɗan Mutum.”