Hausa Bible
Galatiyawa 4
1 Wato, magāji lokacin da yake ɗan yaro, shi da bawa duk ɗaya ne, ko da yake dukan abin da yake a gidansu nasa ne.
2 Yana hannun iyayen goyonsa da wakilai har zuwa lokacin da ubansa ya sa.
3 Haka yake a gare mu kafin hanyar Almasihu ta bayyana. Muna nan kamar yara, mu bayi ne ga ikokin da suke mulkin wannan duniya.
4 Amma saˈad da lokacin da Allah ya shirya ya cika, sai Allah ya aiko da Ɗansa, ta wurin haifuwar mace. An sa shi ƙarƙashin ikon Koyarwar Musa tun daga haifuwa,
5 domin yă fanso waɗanda suke ƙarƙashin Koyarwar, yă kuma mai da su a matsayin ˈyaˈyan Allah.
6 Domin a nuna ku ˈyaˈyansa ne, Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zuciyarku, yana kira ga Allah cewa, “Abba! Uba!”
7 Domin haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne. Da yake kai ɗa ne kuma, Allah ya mai da kai mai cin gādo ne.
8 Dā ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu alloli waɗanda ainihi ba kome suke ba.
9 Amma yanzu kun san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya za ku sāke komawa ƙarƙashin mulkin ikokin duniyar nan marasa ƙarfi? Abin banza ne su. Me ya sa kuke so ku sāke zama bayinsu kuma?
10 Ga shi kukan ba da kanku ga kiyayewar waɗansu ranaku da watanni, da lokatai, da shekaru.
11 Abin da kuke yi ya ba ni tsoro, gama ya zama kamar duk wahalar da na sha a kanku banza ne!
12 Ina roƙonku ˈyanˈuwana, ku zama kamar yadda nake. Gama ni ma na zama kamarku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
13 Kun sani cewa rashin lafiyar da na yi, ya buɗe hanyar da na kawo muku labari mai daɗi da farko.
14 Ko da yake rashin lafiyata ta zama babbar damuwa a wurinku, duk da haka ba ku yi mini reni ko ku ƙi ku kula da ni ba. Kun dai karɓe ni kamar malaˈika daga sama, ko kuwa kamar yadda kuka karɓi Almasihu Yesu da kansa.
15 Kun yi murna sosai a lokacin! To, yanzu fa, ina farin cikin da kuka ji saboda ni? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni!
16 Ashe, yanzu kun mai da ni abokin gābanku ne saboda na gaya muku gaskiya?
17 Waɗannan mutane sun riƙe ku da aniya sosai, amma abin da suke nufi ba shi da kyau. Suna so su raba ku da ni, don duk niyyarku ta koma gare su.
18 Ai, yana da kyau a kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne. Wannan yă kuma kasance haka koyaushe, ba wai sai lokacin da nake tare da ku kawai ba.
19 Ya ku ˈyaˈyana, yanzu ya zama sau biyu ke nan da nake jin zafin haifuwarku. Kuma zan ci gaba da wannan wahala sai halin Almasihu ya kafu a zukatanku.
20 Ayya! Da a ce ina tare da ku yanzu, da sai in canja muryata. Kai, na damu ƙwarai saboda ku!
21 Ku gaya mini, ku da kuke so ku bi Koyarwar Musa, kun gane da abin da Koyarwar take nufi ne?
22 Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ˈyaˈya biyu maza, ɗaya ɗan an haife shi ne ta wurin macen da take baiwa, ɗayan kuma ta wurin macen da take mai ˈyanci.
23 Ɗan nan na baiwa, Ibrahim ya samu ne ta hanyar da aka saba samun ˈyaˈya. Amma ɗaya ɗan nan na mace mai ˈyanci an haife shi ne ta wurin alkawarin da Allah ya yi masa.
24 Wannan misali ne, matan nan biyu sun kwatanta yarjejeniya biyu. Hagar ita ce mai haifuwar bayi.
25 Wato, Hagar ta zama misalin Babban Tudun Sinai wanda yake a ƙasar Arabiya. Ita ce kwatancin birnin Urushalima ta yanzu, gama ita da ˈyaˈyanta duk bayi ne.
26 Amma Urushalima ta sama tana da ˈyanci, kuma ita ce mamarmu.
27 A rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki ya ke macen da ba ki da haifuwa, Ki yi ihu na murna ke da ba ki taɓa jin zafin haifuwa ba, gama yaran macen da mijinta ya bar ta sun yi yawa. Sun fi yaran mace mai miji.”
28 To, ˈyanˈuwa, mu ma mun zama ˈyaˈyan Allah ta wurin alkawari kamar Ishaku.
29 A wancan lokaci kuwa ɗan nan da aka haifa ta hanyar da aka saba ya tsananta wa ɗan nan da aka haifa ta wurin ikon Ruhun Allah. Haka kuma yake har yanzu.
30 Amma a rubuce yake cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Kori baiwar nan da ɗanta, domin ɗan baiwar nan ba zai raba gādo tare da ɗan nan da mace mai ˈyanci ta haifa ba.”
31 Saboda haka ˈyanˈuwa, mu ba ˈyaˈyan baiwa ba ne, mu dai ˈyaˈyan macen da take mai ˈyanci ne.