Hausa Bible
Galatiyawa 2
1 Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima. A wannan lokaci, na tafi tare da Barnaba da kuma Titus.
2 Allah ne ya nuna mini a cikin ruˈuya cewa in tafi. Da na kai can, sai na haɗu da waɗansu shugabannin jamaˈar masu bi, na bayyana musu yadda nake yin shelar labari mai daɗi ga waɗanda ba Yahudawa ba. Na yi musu wannan bayani, su kaɗai, kada ƙwazon da nake yi cikin aikin nan, ko ƙoƙarin da na riga na yi, su zama banza.
3 Titus abokin tafiyata ma, ko da yake shi mutumin Hellas ne, ba wanda ya sa shi dole a yi masa kaciya.
4 Maganar kaciya ta tashi ne saboda ˈyanˈuwan nan na ƙarya waɗanda suka shigo a ɓoye. Sun shigo ne domin su ɓata wannan ˈyancin da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu. Suna so su mai da mu bayi,
5 amma ko kaɗan ba mu yarda musu ba, gama muna so mu kiyaye gaskiyar labarin nan mai daɗi dominku.
6 Amma su mutanen nan da aka ɗauka cewa su manya ne, ba su ƙara kome a kan koyarwar da nake yi ba, a ganina ko su wane ne duk ɗaya ne a wurina, domin Allah ba ya nuna bambanci.
7 A maimakon haka, sun ga yadda Allah ya danƙa mini aikin waˈazin labarin nan mai daɗi ga marasa kaciya, kamar yadda ya danƙa wa Bitrus aikin waˈazi ga Yahudawa masu kaciya.
8 Gama shi Allah wanda ya yi aiki a zuciyar Bitrus domin yă zama manzo ga Yahudawa, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata domin in zama manzo ga waɗanda ba Yahudawa ba.
9 Da ganin yadda Allah ya nuna mini alherinsa haka, su Yakub, da Bitrus da Yohanna, waɗanda aka ɗora musu aikin shugabancin jamaˈar masu bi, suka karɓe mu, ni da Barnaba, da zuciya ɗaya. Mun yarda da juna cewa mu za mu je wurin waɗanda ba Yahudawa ba, su kuwa su je wurin Yahudawa.
10 Sai dai suka tuna mana cewa kada mu manta da talakawan da suke wajensu. Ni kuwa tun dā ma nake marmarin yin haka ƙwarai.
11 A lokacin da Bitrus ya zo Antakiya, sai na tsawata masa fuska da fuska domin laifinsa a fili yake.
12 Da farko, yana cin abinci tare da masu bi waɗanda ba Yahudawa ba. Amma bayan da Yakub ya aiki waɗansu zuwa Antakiya, sai Bitrus ya janye, ya ware kansa. Ya yi haka ne domin yana tsoron waɗanda suke so a yi wa waɗanda ba Yahudawa ba kaciya.
13 Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka yi munafunci kamar Bitrus, har ma suka jawo Barnaba a cikin wannan munafunci.
14 Amma da na ga ba sa yin abinsu bisa ga gaskiyar labarin nan mai daɗi, sai na ce wa Bitrus a gaban kowa duka, “Kai Bayahude ne, amma kana yin zamanka yadda waɗanda ba Yahudawa ba suke yi, ba kamar yadda Yahudawa suke yi ba. Yanzu, yaya za ka sa wa waɗanda ba Yahudawa ba dole su bi alˈadun Yahudawa?”
15 “Hakika mu Yahudawa ne bisa ga haifuwa, ba waɗanda ba Yahudawa ba ko masu zunubi ba,
16 mun sani cewa mutum ba zai sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa ba, sai dai idan ya ba da gaskiya ga Yesu Almasihu. Saboda haka mu ma mun ba da gaskiya ga Almasihu Yesu. Mun yi haka domin mu samu zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Almasihu ba ta wurin yin ayyukan Koyarwar Musa ba. Gama babu wanda yakan sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa.
17 In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Almasihu, saˈan nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, to, wannan zai nuna Almasihu yana hidimar zunubi ke nan? Aˈa, ko kusa!
18 “Amma idan na tashi ina sāke gina abubuwan da dā na rushe na zama mai karya Koyarwa ke nan.
19 Ai, ta wurin Koyarwar Musa na zama matacce ga Koyarwar, domin in rayu ga Allah.
20 An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne ina rayuwa ba, amma Almasihu ne yake raye a zuciyata. Wannan rayuwa ta jikin da nake yi, rayuwa ce ta wurin dogara ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.
21 Ba zan yi banza da alherin Allah ba. Amma idan mutum yana iya samun zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa, wannan ya nuna cewa mutuwar Almasihu ta zama banza ke nan.”