Hausa Bible
Galatiyawa 2:16
mun sani cewa mutum ba zai sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa ba, sai dai idan ya ba da gaskiya ga Yesu Almasihu. Saboda haka mu ma mun ba da gaskiya ga Almasihu Yesu. Mun yi haka domin mu samu zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Almasihu ba ta wurin yin ayyukan Koyarwar Musa ba. Gama babu wanda yakan sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa.
Open Bible reader