Skip to content

Hausa Bible

Afisawa 2

1 A dā ku matattu ne, saboda laifofinku da zunubanku

2 waɗanda dā kuke ciki saˈad da kuke bin hanyoyin duniyar nan, kuna bin sarkin mulki a sammai, wato, ruhun nan da yake zuga zuciyar mutanen da suka ƙi biyayya ga Allah.

3 Dukanmu dai haka muke a dā, muna bin shaˈawace-shaˈawacen jikinmu, muna yin abin da jiki da zuciya suke zuga mu mu yi kawai. Ta haka, bisa ga halinmu na ˈyan Adam, mu ma dā fushin Allah ya zo kanmu kamar yadda yake a kan sauran ˈyan Adam.

4 Amma Allah mai yawan tausayi ne, ƙaunarsa zuwa gare mu kuma ta yi yawa ƙwarai,

5 har tun saˈad da muke matattu ta wurin zunubanmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu. Ta wurin alheri ne aka cece ku.

6 Ya kuma tashe mu tare da Almasihu, har ta wurin Almasihu Yesu, ya ba mu wurin zama a samaniya tare da shi.

7 Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa yă nuna alherinsa a yalwace marar iyaka. Alherin nan nasa, ya nuna mana shi a cikin Almasihu Yesu.

8 Ai, ta alherin Allah ne kuka sami ceto ta wurin bangaskiya. Wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, kyauta ce ta Allah.

9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, domin kada wani yă yi taƙama.

10 Ai, mu da kanmu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu, musamman domin mu yi ayyuka masu kyau waɗanda Allah ya riga ya shirya mana tun da fari mu yi.

11 Saboda haka, ku tuna yadda kuke a dā. Ku ba Yahudawa ba ne bisa ga haifuwa. Su waɗanda suke kiran kansu “masu kaciyar” nan, sukan kira ku “marasa kaciya”. Ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu.

12 Ku tuna a lokacin ba a haɗa ku da Almasihu ba, ba ku da matsayi cikin jamaˈar Israˈila, baƙi ne ku ga dukan yarjejeniyar alkawarin nan da Allah ya yi. Ku dai a duniyar nan ba ku da bege, ba ku da Allah.

13 Amma yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, ku da dā kuke can da nisa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.

14 Gama Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya ɗauki Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, ya mai da su ɗaya. Ya rushe katangar nan da ta raba su, wato, ƙin juna da yake tsakaninsu.

15 Ya kawar da Koyarwar nan ta Musa mai umarnai da ƙaˈidodi ta wurin ba da jikinsa. Ya yi haka domin ta wurinsa yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyar nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.

16 Ya kuma yi haka domin yă shirya su duka biyu da Allah, su zama jiki ɗaya, ta wurin mutuwarsa a kan gicciye. Ta haka kawar da ƙiyayyar da ta raba su a dā.

17 Ya kuwa zo ya yi muku waˈazin labari mai daɗi na salama, ku waɗanda ba Yahudawa ba, ku da kuke nesa da Allah. Ya kuma yi wa Yahudawa haka, su da suke kusa.

18 Ai, ta wurinsa ne dukanmu biyu za mu sami damar zuwa wurin Uba ta hanya ɗaya, wato Ruhun Allah.

19 Saboda haka, yanzu ku waɗanda ba Yahudawa ba, ba baƙi ba ne kuma, ba ku rasa wurin zama ba. Ai, ku masu ˈyanci ne tare da sauran tsarkaka, ˈyan gida ne kuma kamar sauran iyalin Allah.

20 An kafa ku duka bisa tushen da manzanni da annabawa suka gina, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne dutse mafi amfani a ginin.

21 Shi ne wanda ta wurinsa dukan ginin yake haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi ta ƙara girma har yă zama haikali mai tsarkin da aka keɓe wa Ubangiji.

22 A cikinsa ne ku kuma aka gina ku da sauran domin ku zama gida inda Allah yake zama ta wurin Ruhunsa.

Open Bible reader