Skip to content

Hausa Bible

Kolosiyawa 3

1 Tun da yake Allah ya tā da ku da rai tare da Almasihu, sai ku sa ido a kan abubuwan nan da suke sama, inda Almasihu yake, yana kuwa a zaune a hannun dama na Allah.

2 Ku sa tunaninku a kan abubuwan da suke na sama, kada ku damu da abubuwan duniyar nan.

3 Gama kun riga kun mutu, ranku kuwa yana a ɓoye tare da Almasihu cikin Allah.

4 Saˈad da Almasihu, wanda shi ne ran naku, ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi cikin ɗaukakarsa.

5 Saboda haka, sai ku kashe halin shaˈawace-shaˈawacen duniya a zuciyarku, wato iskanci, da aikin lalata, da muguwar shaˈawa, da mugun hali, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.

6 Saboda irin halayen nan ne fushin Allah yake saukowa a kan marasa biyayya.

7 Dā ku da kanku kuna tafiya a cikin waɗannan halaye, saˈad da kuke rayuwa a cikinsu.

8 Amma yanzu dole ne ku rabu da dukan irin halayen nan. Ku bar yin fushi, da zafin rai, da ƙiyayyar zuciya, da ɓata suna, da maganar ƙazanta daga bakinku.

9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun riga kun kawar da halinku na dā da ayyukansa,

10 har kun ɗauki sabon halin nan, wanda ake sabuntawa ga sani bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

11 Da yake kun sami sabon hali, babu sauran bambanci tsakaninku ke nan, da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, da mai kaciya da marar kaciya, da mai ɗanyen hali, da mutumin ƙauye, da bawa da mai ˈyanci, dukansu ɗaya ne gama Almasihu shi ne kome, shi ne kuma yake cikinmu duka.

12 Allah ya zaɓe ku domin ku zama mutanensa masu tsarki waɗanda yake ƙauna ƙwarai. Saboda haka, sai ku ɗauki hali na jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawaliˈu da sauƙin kai da jimrewa,

13 kuna ta yin haƙuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa, kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku zunubanku, haka ma ku ma ku gafarta wa juna.

14 Fiye da waɗannan, ku ɗauki halin ƙauna, gama ƙauna ce take ɗaura dukan kome cikin cikakkiyar ɗayantaka.

15 Bari salama ta Almasihu ta yi mulki a zuciyarku, gama saboda salamar nan ce Allah ya kira ku cikin jiki ɗaya, ku kuma kasance masu godiya.

16 Bari maganar Almasihu ta kasance a zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, kuna rera waƙoƙin zabura da na yabon Allah, kuna rera waƙoƙin da Ruhu ya ƙirƙiro, kuna rerawa da godiya a zuciyarku.

17 A kowane abin da kuke yi, cikin magana ko ayyuka, ku yi shi a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

18 Ku matan aure, ku miƙa kanku ga mazanku kamar yadda ya dace cikin Ubangiji.

19 Ku maza kuma ku ƙaunaci matanku. Kada ku nuna musu hali marar tausayi.

20 Ku yara, ku yi wa iyayenku biyayya cikin kowane abu, gama wannan yakan faranta wa Ubangiji rai.

21 Ku ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, domin kada su fid da zuciya.

22 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome. Kada ku yi aikin ganin ido kamar masu son faranta wa mutane rai, a maimakon haka, ku yi aiki da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.

23 Duk abin da kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku kamar ga Ubangiji ne kuke yi wa, ba ga mutum ba,

24 tun da yake kun sani cewa Ubangiji zai ba ku gādo wanda yake ladanku. Gama Ubangiji Almasihu ne kuke bauta wa!

25 Mai aikin mugunta kuwa, zai sami ladan muguntarsa, gama babu nuna bambanci.

Open Bible reader