Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 5

1 Amma wani mutum mai suna Hananiya, tare da matarsa Safiratu, ya sayar da wani abin da yake da shi.

2 Sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin da sanin matarsa, ya kawo sashe kawai ya ajiye a gaban manzanni.

3 Sai Bitrus ya ce, “Kai Hananiya, ta yaya ka bar Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga cikin kuɗin gonar?

4 Kafin ka sayar ba taka ba ce? Bayan da ka sayar ma, ba a sa ka dole ka ba da kuɗin ba. Ta yaya ka yi wannan tunani a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.”

5 Da jin wannan maganar kuwa, Hananiya ya fāɗi ya mutu. Mutanen da suka ji kuwa, tsoro ya kama su sosai.

6 Samari suka tashi suka naɗe jikinsa da yadi, suka ɗauke shi zuwa waje suka binne.

7 Bayan kamar awa uku, matar Hananiya ta shigo, ba ta san abin da ya faru ba.

8 Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, wannan shi ne iyakacin kuɗin da aka biya ku a kan gonar nan?” Sai ta ce, “I, iyakacin kuɗin ke nan.”

9 Amma Bitrus ya ce mata, “Yaya kuka haɗa baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Ga shi, ki ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki su fitar da ke.”

10 Nan take ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da samarin suka shigo suka same ta ta mutu, sai suka ɗauke ta, suka fitar da ita, suka binne ta ta gefen mijinta.

11 Sai babban tsoro ya kama dukan jamaˈar masu bi, da duk waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.

12 To, an yi alamu da ayyukan mamaki masu yawa cikin mutane ta wurin manzanni. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Zauren Solomon a filin Haikali.

13 Amma a cikin sauran mutane, ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, ko da yake jamaˈa suna ba su girma.

14 Duk da haka masu ba da gaskiya ga Ubangiji suka yi ta ƙaruwa da jamaˈa masu yawan gaske ne, maza da mata.

15 Har ma ya kai ga mutane suna fito da marasa lafiya titi-titi, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi. Suna fata cewa idan Bitrus ya zo wucewa, ko inuwarsa ma ta bi ta kan waɗansunsu.

16 Mutane da yawa kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda ƙazaman ruhohi suke ba su wahala, dukansu kuwa aka warkar da su.

17 Sai babban firist tare da dukan waɗanda suke tare da shi, wato ˈyan ƙungiyar Sadukiyawa, sun ji kishin manzannin sosai.

18 Saboda haka suka taso suka kama manzannin, suka sa su a kurkuku.

19 Amma da dare sai wani malaˈikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,

20 “Ku je ku tsaya cikin Haikali ku faɗa wa mutane dukan maganar wannan sabon rai.”

21 Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa. Saˈad da babban firist da waɗanda suke tare da shi suka taru, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Israˈila, suka aika zuwa kurkuku a kawo manzannin.

22 Amma da masu gadin Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce,

23 “Mun sami kurkukun a kulle sosai, masu gadi kuma suna gadin bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka samu ba kowa a ciki.”

24 Da shugaban masu gadin Haikali da manyan firistoci suka ji haka, suka rikice sosai, suna tunanin abin da wannan zai kawo.

25 Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna tsaye a Haikali, suna koyar da jamaˈa.”

26 Sai masu gadin Haikalin tare da shugabansu suka je suka kawo manzannin, amma fa ba da ƙarfi ba, don shugabannin suna tsoro kada jamaˈa su jejjefe su da duwatsu.

27 Da suka kawo manzannin, suka sa suka tsaya a gaban majalisa. Sai babban firist ya tambaye su,

28 ya ce, “Mun ja muku kunne sosai kada ku ƙara yin koyarwa cikin sunan nan, amma ga shi kun cika Urushalima duk da koyarwarku, har ma kuna nema ku tura mana alhakin jinin mutumin nan.”

29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mu yi wa mutum.

30 Allahn kakanninmu ya tā da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin gicciye shi a kan gungumen itace.

31 Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa yă zama Shugaba da kuma Mai Ceto, domin yă buɗe wa Israˈila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.

32 Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba masu yi masa biyayya.”

33 Da shugabannin suka ji haka, sai suka ji fushi sosai, har suka so su kashe manzannin.

34 Amma wani Bafarisiye mai suna Gamaliyel, malamin Koyarwar Musa, wanda dukan jamaˈa suna ba shi girma, ya tashi tsaye cikin majalisa, ya ba da umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.

35 Saˈan nan ya ce wa ˈyan majalisa, “Ku ˈyanˈuwa Israˈilawa, ku kula fa da abin da kuke so ku yi wa mutanen nan.

36 Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, mai suna Tudas, ya ɗauki kansa kamar wani abu. Wajen mutum ɗari huɗu suka bi shi, amma aka kashe shi, aka kuwa watsar da masu binsa, wannan kuwa ya zama ƙarshensu.

37 Bayan wannan kuma, wani mai suna Yahuda, mutumin Galili ya ɓullo, lokacin da ake ƙirgar mutane, ya sa mutane suka bi shi. Shi ma ya halaka, masu binsa ma duka aka watsar da su.

38 To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita daga hanyar mutanen nan, ku bar su. Idan dai niyyarsu, ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe.

39 Amma idan aikin nan na Allah ne, ba za ku iya hana mutanen nan ba. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.” Sai suka yarda da shawararsa,

40 suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu bulala, suka ja musu kunne kada su ƙara yin magana cikin sunan Yesu. Saˈan nan suka sake su.

41 Manzannin suka tashi daga gaban majalisar suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulaƙanci saboda sunan Yesu.

42 Kowace rana kuwa, ko a Haikali, ko a gida, ba su daina koyarwa da ba da labari mai daɗi na cewa Yesu shi ne Almasihu ba.

Open Bible reader