Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 4
1 Lokacin da Bitrus da Yohanna suke cikin yin magana da jamaˈa, sai firistoci da shugaban masu gadin Haikalin da Sadukiyawa suka zo wurinsu.
2 Sun yi fushi domin almajiran suna koya wa jamaˈa cewa matattu za su tashi da rai kamar yadda Yesu ya tashi.
3 Sai suka kama su, suka kulle su sai washegari, don yamma ta yi.
4 Amma da yawa daga cikin mutanen da suka ji waˈazin suka ba da gaskiya. Sai duk yawan masu bi ya kai wajen mutum dubu biyar.
5 Washegari shugabanninsu da dattawansu, da malaman Koyarwar Musa nasu suka taru a Urushalima.
6 Hannana, babban firist, yana nan tare da Kayafa, da Yohanna, da Alekzanda, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.
7 Suka sa Bitrus da Yohanna suka tsaya a tsakiyarsu, sai suka tambaye su suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne kuka yi wannan?”
8 To, Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya tambaye su ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jamaˈa,
9 a yau, kuna tambayarmu a kan alherin da aka yi wa wannan gurgun ne? Kuna kuma so ku sani wanda ya warkar da shi ne?
10 To, muna so ku sani, ku da dukan mutanen Israˈila, cewa a cikin sunan Yesu Almasihu Banazaret nan da kuka gicciye, wanda Allah ya tā da shi daga matattu, da sunansa ne wannan mutumin yake tsaye lafiyayye a gabanku.
11 Wannan Yesu, shi ne wanda aka rubuta game da shi a cikin Maganar Allah cewa, “ ‘Dutsen nan da ku masu gini kuka ƙi, shi ne kuwa ya zama mafi amfani a gini.’
12 “Ba kuma samun ceto ga wani, gama cikin dukan sunayen da aka ba mutane a ƙarƙashin sama, ba wani suna dabam da aka bayar wanda lallai ta wurinsa ne za mu sami ceto.”
13 To, da shugabannin suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna, suka kuma gane su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki, suka kuwa gane cewa dā manzannin suna tare da Yesu.
14 Amma tun da shugabannin suka ga mutumin nan da aka warkar ɗin yana tsaye tare da manzannin, sai suka rasa abin da za su ce.
15 Suka umarci manzannin su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna
16 suka ce, “Me za mu yi da mutanen nan? Don lallai dukan mazaunan Urushalima sun san cewa an yi wani babban aikin ban mamaki ta wurin mutanen nan, ba kuwa yadda za mu ce, ‘Ba haka ba ne.’
17 Amma domin kada abin yă bazu a cikin mutane, sai mu ja musu kunne, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan sunan.”
18 Sai suka kirawo manzannin, suka ja musu kunne, kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa cikin sunan Yesu.
19 Amma Bitrus da Yohanna suka amsa musu suka ce, “To, ko daidai ne a wurin Allah mu fi jin maganarku fiye da maganar Allah? Sai ku duba ku gani.
20 Don mu kam, ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.”
21 Da suka ƙara jan musu kunne, suka sake su. Sun kuwa rasa yadda za su yi su hore su, domin mutane duka suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya faru.
22 Mutumin nan kuwa da ya sami warkewa na ban mamaki, ya fi shekara arbaˈin da haifuwa.
23 Da aka sake Bitrus da Yohanna, sai suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin dukan abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.
24 Su kuwa, da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, kai ne ka halicci sama da ƙasa, da teku, da kuma dukan abubuwan da suke cikinsu.
25 Ta wurin Ruhu Mai Tsarki ka yi magana ta wurin bawanka wato, kakanmu Dawuda, ka ce, “ ‘Don me waɗanda ba Yahudawa ba suka yi fushi? Kabilu kuma suka yi tunanin alˈamuran wofi?
26 Sarakunan duniya sun yi shirin yaƙi, shugabanninsu kuma sun haɗa kai, suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’ ”
27 “Gama hakika a birnin nan Sarki Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai tare da waɗanda ba Yahudawa ba, da jamaˈar Israˈila, suna gāba da Bawanka Yesu mai tsarki, wanda ka mai da shi Almasihu.
28 Sun taru domin su aikata duk abin da ka ƙaddara zai faru, bisa ga ikonka da nufinka.
29 “Yanzu kuma, ya Ubangiji, ka dubi yadda suke ƙoƙarin hana mu aiki. Ka ba bayinka ƙarfin halin faɗin kalmarka babu tsoro.
30 Ka dinga miƙa hannunka na warkewa, ka kuma yi alamu da ayyukan ban mamaki ta wurin sunan Bawanka, Yesu mai tsarki.”
31 Da suka yi adduˈa, sai wurin da suka taru ya girgiza. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗin kalmar Allah babu tsoro.
32 To, duk taron masu bi kuwa nufinsu ɗaya ne, raˈayinsu ma ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da yake da shi nasa ne, sai dai nasu ne tare.
33 Da iko mai girma manzannin kuma suka ba da shaida a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa ya kasance a kan kowane ɗayansu,
34 har ba wanda ya rasa wani abu a cikinsu. Domin duk masu gonaki ko gidaje suka dinga sayar da su, suna kawo kuɗin,
35 suna ajiye a gaban manzannin, ana kuwa rarraba wa kowa bisa ga bukatarsa.
36 Haka wani mai suna Yusuf ya yi. Shi mutumin zuriyar Lawi ne, asalinsa mutumin Sayifurus ne, wanda manzannin suke ce da shi Barnaba, wato, mai ƙarfafa zuciya.
37 Barnaba kuwa ya sayar da wata gonarsa, ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.