Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 28

1 Bayan da muka tsira sai muka ji, ashe, sunan tsibirin nan Malta ne.

2 Mutanen wurin kuwa sun yi mana alheri ƙwarai da gaske. Sai suka karɓe mu duka, suka hura mana wuta gama ana ruwa ana kuma sanyi.

3 Bulus ya tattaro itace yana sawa a wutar, sai wani maciji mai dafi ya fito saboda zafin wutar, ya cafke hannun Bulus.

4 Da mutanen wurin suka ga macijin yana lilo a hannun Bulus, sai suka ce wa junansu, “Lallai mutumin nan mai kisan kai ne! Ga shi, ko da yake ya tsira daga teku, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”

5 Bulus kuwa ya jijjiga hannunsa ya jefa macijin cikin wuta, bai kuwa ji ciwo ba.

6 Suna tsammani zai kumbura ko yă fāɗi nan take yă mutu, amma da suka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke tunani suka ce shi wani allah ne.

7 Nan kusa kuwa akwai filaye na shugaban tsibirin nan, mai suna Fubiliyus. Shi ne ya karɓe mu, ya ba mu masauki mai kyau, har kwana uku.

8 Baban Fubiliyus kuwa yana kwance yana fama da zazzaɓi da atini. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi masa adduˈa, ya sa hannu a kansa, mutumin kuwa ya warke.

9 Da haka ya faru, sai dukan sauran marasa lafiya a tsibirin suka dinga zuwa ana warkar da su.

10 Suka yi mana kyauta mai yawa. Da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka tattara mana duk abubuwan da muke bukata.

11 Bayan wata uku, muka tashi daga tsibirin Malta cikin jirgin Alekzandiriya wanda ya ci damina a wannan tsibiri. An kuwa yi masa alamar siffar tagwayen alloli.

12 Da muka zo Sirakus muka yi kwana uku a wurin.

13 Daga nan kuma muka tafi, sai ga mu a Rigiyum. Bayan kwana ɗaya, iska ta taso daga kudu, washegarin kuma muka kai Futiyoli.

14 A nan muka sadu da waɗansu ˈyanˈuwa masu bi, suka roƙe mu mu yi kwana bakwai tare da su. Da haka dai muka kai Roma.

15 Da masu bi na Roma suka ji labarinmu, sai suka zo su marabce mu har a Kasuwar Affiyus, da kuma wurin nan da ake ce da shi Masauki Uku. Da Bulus ya gan su kuwa ya yi godiya ga Allah, ya kuma ƙara samun ƙarfin gwiwa.

16 Da muka shiga Roma aka yarda wa Bulus yă je yă zauna a gidan haya tare da sojan da yake gadinsa.

17 Bayan kwana uku, Bulus ya kira manyan Yahudawa. Da suka taru sai ya ce musu, “Ku ˈyanˈuwa, ko da yake ban yi wa jamaˈarmu wani laifi ba, ko laifi game da alˈadun kakanninmu, duk da haka an kama ni a Urushalima aka ba da ni ga Romawa a ɗaure.

18 Su kuwa da suka bincike ni, suna so su sake ni, domin ba su same ni da wani laifin da ya isa a kashe ni ba.

19 Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙarata zuwa gaban Kaisar, ko da yake ba wai ina ƙarar jamaˈarmu ba ne.

20 Shi ya sa na nemi in gan ku, in kuma tattauna da ku tun da yake dai saboda da shi wannan da Israˈilawa suke sa zuciyar zuwansa ne aka ɗaure ni da sarƙar nan.”

21 Sai suka ce masa, “Mu dai ba mu sami wata wasiƙa daga yankin Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗanˈuwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗa wata magana marar kyau game da kai.

22 Amma muna so mu ji raˈayinka daga bakinka, domin abin da muka sani dai shi ne, sabuwar ƙungiyar ƙaryar nan kowa yana muguwar magana a kanta.”

23 Da suka sa ranar da za su haɗu, sai suka zo masaukinsa, sun kuwa zo da yawa sosai. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yi musu bayani yana shaida musu a kan mulkin Allah, yana ƙoƙarin yă jawo su zuwa wurin Yesu ta hanyar Koyarwar Musa da littattafan annabawa.

24 Waɗansu suka yarda da abin da ya faɗa, amma waɗansu ba su gaskata ba.

25 Saboda haka ba su yarda da juna ba. Kafin su bar wurin sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki ya faɗa gaskiya, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin annabi Ishaya cewa,

26 “ ‘Ka je wurin jamaˈar nan, ka ce, ji kam, za ku dinga ji, amma ba za ku fahimta ba sam, gani kam, za ku dinga gani, amma ba za ku gane ba sam.

27 Don zuciyar jamaˈar nan ta yi tauri, sun toshe kunnuwansu, sun rufe idanunsu, domin kada su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su kuma gane da zuciyarsu, har su juyo wurina in warkar da su.’

28 “To, sai ku sani fa, Allah ya aika da labarin ceto har zuwa ga waɗanda ba Yahudawa ba. Su kuwa za su saurara.”

29 Da ya faɗa haka, sai Yahudawa suka tashi daga wurin suna gardama mai zafi a tsakaninsu.

30 Bulus ya zauna a wannan gidan da yake haya har shekara biyu, yana karɓar duk waɗanda suka zo wurinsa.

31 Da yake ba a hana shi waˈazi ba, ya yi ta yin waˈazin mulkin Allah, yana koyarwa a kan Ubangiji Yesu Almasihu babu tsoro.

Open Bible reader