Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 28:23

Da suka sa ranar da za su haɗu, sai suka zo masaukinsa, sun kuwa zo da yawa sosai. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yi musu bayani yana shaida musu a kan mulkin Allah, yana ƙoƙarin yă jawo su zuwa wurin Yesu ta hanyar Koyarwar Musa da littattafan annabawa.

Open Bible reader