Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 20
1 Bayan da rikicin ya kwanta, Bulus ya kira masu bi. Da ya ƙarfafa musu zuciya, sai ya yi ban kwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.
2 Da ya zazzaga waɗannan yankuna, ya kuma ƙarfafa masu bi sosai, sai ya kai ƙasar Hellas.
3 Ya yi wata uku a nan. Yana shirin yă shiga jirgin ruwa yă tafi ƙasar Suriya ke nan, Yahudawa kuwa suka yi masa mugun shiri. Saboda haka sai ya zaɓi yă koma ta Makidoniya.
4 Sufata ɗan Farus daga Biriya, tare da Aristarkus da Sakundus, mutanen Tasalonika, da Gayus daga Darbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimus, mutanen Asiya, suka raka shi.
5 Sun riga mu tafiya suka jira mu a Toruwas.
6 Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan Bikin Burodi Marar Yisti, muka same su a Toruwas bayan kwana biyar. A Toruwas muka yi kwana bakwai.
7 A ranar farko ta mako kuma muka taru domin mu rarraba burodin zumunci. Sai Bulus ya yi musu jawabi. Saboda yana shiri yă tafi washegari, ya yi ta jawabi har tsakar dare.
8 Akwai kuwa fitilu da yawa a gidan saman da muka taru.
9 Wani saurayi mai suna Yutikus yana zaune a kan taga, sai barci ya dame shi sosai lokacin da Bulus yake ta yin dogon jawabinsa. Har barcin ya kwashi Yutikus, sai ya fāɗi daga can hawa na uku, kuma aka ɗauke shi matacce.
10 Amma Bulus ya sauka ƙasa ya sunkuya ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, ai, yana da rai.”
11 Sai Bulus ya koma sama ya rarraba burodin zumunci muka ci. Ya ci gaba da yi musu magana har gari ya waye, saˈan nan ya tafi.
12 Sai suka tafi da saurayin da rai, suka kuwa yi murna sosai.
13 Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin ruwan, muka miƙe zuwa Asus da nufi mu ɗauki Bulus daga can. Gama dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyya yă tafi da ƙafa.
14 Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin muka zo Mitilin.
15 Daga nan kuma muka ci gaba da tafiya a cikin jirgin ruwan. Washegari kuma sai ga mu a gefen Kiyos. Washegari kuma sai ga mu a Samos, washegari kuma sai Miletus.
16 Dā ma kuwa Bulus ya sa rai ba zai sauka a Afisa ba, domin kada yă ɓata lokaci a Asiya. Yana sauri, idan zai yiwu ma yă kai Urushalima kafin ranar Bikin Fentikos.
17 Daga Miletus ne Bulus ya aika zuwa Afisa a kira masa dattawan jamaˈar masu bi.
18 Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku tun ranar da na sa ƙafata a ƙasar Asiya.
19 Ina bauta wa Ubangiji da tawaliˈu sosai har da hawaye. Na jimre gwaje-gwajen da suka zo mini ta wurin mugayen shirye-shiryen da Yahudawa suka yi mini.
20 Ban daina gaya muku kowane abu mai amfani ba, ina yi muku waˈazi da koyarwa a fili, da kuma gida-gida.
21 Na gargaɗi Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba duka game da tuba zuwa wurin Allah, su kuma ba da gaskiya ga Ubangijinmu Yesu.
22 “Ga shi kuma yanzu ikon Ruhu yana tura ni, zan tafi Urushalima, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,
23 ko da yake Ruhu Mai Tsarki yana tabbatar mini a kowane gari cewa kullewa a kurkuku, da shan tsanani suna jirana.
24 Amma ni ban mai da raina kamar wani abu ba, idan dai zan iya gama tserena, in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni, wato in shaida labari mai daɗi na alherin Allah.
25 “To, yanzu na sani dukanku ba za ku sāke ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku shelar mulkin Allah.
26 Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa ba alhakin jini ko na ɗayanku a kaina,
27 domin na sanar muku da nufin Allah duka.
28 Ku lura da kanku, da kuma dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa kuka zama masu kula da shi, ku kuma ci gaba da kiwon jamaˈar masu bi waɗanda Allah ya samo wa kansa da jinin Ɗansa.
29 “Na sani bayan na tafi waɗansu mugayen kyarketai za su shigo cikinku, ba kuwa za su bar garken ba.
30 Har ma a cikinku waɗansu za su taso su yi maganganun ƙarya, domin su jawo masu bi zuwa gefensu.
31 Saboda haka sai ku zauna da shiri, ku tuna fa, shekara uku ke nan, dare da rana, ban fasa yi wa kowane ɗayanku gargaɗi ba, har da hawaye.
32 “Yanzu kuma na danƙa ku a hannun Allah. Bari kalmar alherinsa ta kiyaye ku, ita ce za ta iya gina ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan masu tsarki.
33 Ban yi kwaɗayin kuɗi ko tufafin kowa ba.
34 Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana domin in biya bukatuna da na waɗanda suke tare da ni.
35 Cikin wannan duka na ba ku misali cewa dole ne ku yi aiki haka don mu taimaki marasa ƙarfi. Kuna tuna kuma da kalmar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Ya fi albarka a bayar da a karɓa.’ ”
36 Da Bulus ya gama faɗin haka, sai ya durƙusa ya yi adduˈa tare da su duka.
37 Sai duk suka fashe da kuka, suka rungumi Bulus suna yin masa sumba,
38 suna baƙin ciki musamman don maganar da ya yi ta cewa ba za su ƙara ganinsa ba. Daga nan suka raka shi har bakin jirgi.