Skip to content

Hausa Bible

Romawa 12

1 Saboda haka ina roƙonku, ˈyanˈuwa, saboda yawan jinƙan nan na Allah, ku miƙa kanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki, da kuma abin karɓa ga Allah. Wannan kuwa ita ce hanyar da za ku yi wa Allah hidima ta ainihi.

2 Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan yă bi da hankalinku, amma ku yarda Allah yă canja ku yă sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.

3 Bisa ga alherin nan da aka yi mini, ina yi wa kowane ɗayanku gargaɗi cewa kada kowa yă ɗauki kansa da girma fiye da yadda ya kamata yă yi. A maimakon haka kowa yă mai da hankali game da yadda yake ganin kansa, wato yă dinga ganin kansa daidai gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.

4 Muna da gaɓoɓi da yawa cikin jiki guda, kuma duk gaɓoɓin nan suna da aikinsu dabam-dabam.

5 Haka kuma, mu da muke mutane masu yawa, mun zama jiki ɗaya cikin Almasihu, kowane ɗayanmu kuwa gaɓar ɗanˈuwansa ne.

6 Da yake muna da baye-bayen nan iri-iri daidai gwargwadon alherin da Allah ya yi mana, to, sai mu yi amfani da su. Idan baiwarmu ta yin annabci ce, sai mu yi annabci daidai gwargwadon bangaskiyarmu.

7 Idan baiwarmu kuwa ta yin hidima ce, sai mu yi hidima. Idan ta yin koyarwa ce, mu yi koyarwa.

8 Idan ta ƙarfafawar juna ce, bari mu kasance masu ƙarfafawa. Idan kuma baiwarmu ta biyan bukatar ˈyanˈuwa ce, sai mu yi haka ɗin hannu sake. Idan ta shugabanci ce, sai mu yi shi da ƙwazo. Idan ta nuna tausayi ce, sai mu yi haka da farin ciki.

9 Ya kamata ƙaunarku ta zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu, amma ku riƙe abin da yake mai kyau da ƙarfi sosai.

10 Ku ba da kanku ga juna da ƙauna irin ta ˈyanˈuwa. Kowa yă yi saurin girmama wani fiye da kansa.

11 Kada ku taɓa zama da rashin ƙwazo, amma ku ɗauki niyya sosai a zukatanku kuna yi wa Allah hidima.

12 Ku yi farin ciki a cikin sa zuciyarku, ku yi haƙuri a cikin azaba, ku yi aminci kuma a cikin adduˈarku.

13 Ku dinga raba abin da kuke da shi da tsarkakan Allah waɗanda suke da bukata. Ku dinga karɓar baƙi hannu biyu-biyu.

14 Ku sa wa waɗanda suke tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku laˈanta su.

15 Ku yi farin ciki tare da masu farin ciki, ku yi kuka tare da masu kuka.

16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna halin ɗaga kai, amma ku mai da kanku abokai ga waɗanda ba a ɗauke su a bakin kome ba. Kada ku ɗauki kanku kamar kun fi sauran mutane wayo.

17 Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.

18 Ku yi iyakar ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.

19 Kada ku zama masu ramuwa, ˈyanˈuwana, sai dai ku bar wa Allah yă rama muku da fushinsa. Don kuwa a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, “Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji Ubangiji.”

20 Rubutacciyar Maganar Allah ta sāke cewa, “Idan abokin gābanka yana jin yunwa, sai ka ba shi abinci. Idan yana jin ƙishin ruwa, sai ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka kana tara garwashin wuta a kansa ne.”

21 Kada ku bar mugunta ta yi nasara a kanku, a maimakon haka ku yi nasara a kan mugunta ta wurin aikata abin da yake mai kyau.

Open Bible reader