Hausa Bible
Markus 9
1 Ya kuma ce musu, “Gaskiya, ina gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaye a nan waɗanda ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
2 Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakub, da Yohanna, ya kai su kan wani babban tudu mai tsawo inda suka kasance su kaɗai. Ana nan sai kamanninsa ya canja a gabansu,
3 rigunansa kuma suka yi fari fat suna ƙyalli, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya.
4 Sai ga annabi Iliya da annabi Musa suka bayyana a gare su, suna magana da Yesu.
5 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Malam, ya yi kyau da muke nan, bari mu yi bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin annabi Musa, ɗaya kuma domin annabi Iliya.”
6 Ya rasa abin da zai faɗa ne, domin shi da sauran almajiran sun ji tsoro ƙwarai.
7 Sai ga wani girgije ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna. Ku saurare shi!”
8 Ba labari, da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.
9 Da suna cikin gangarowa daga tudun, sai Yesu ya ja musu kunne kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai Ɗan Mutum ya tashi daga matattu tukuna.
10 Domin haka suka bar wannan maganar, suna tambayar juna ko mene ne Yesu yake nufi da “tashi daga matattu”.
11 A ƙarshe suka tambaye shi suka ce, “To, don me malaman Koyarwar Musa suke cewa sai annabi Iliya ya fara zuwa, saˈan nan Almasihu yă zo?”
12 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne annabi Iliya zai fara zuwa domin yă shirya kome. Amma an kuma rubuta a cikin Maganar Allah cewa Ɗan Mutum zai sha wuya iri-iri, za a kuma wulaƙanta shi. Ko ba haka ba?
13 Ai, Iliya ya riga ya zo, mutane suka kuma yi masa duk abin da suka ga dama, kamar dai yadda aka rubuta zai faru.”
14 Da Yesu da almajiran nan uku suka koma wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su. Malaman Koyarwar Musa kuma suna gardama da su.
15 Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka tashi da gudu suka je suka gaishe shi.
16 Yesu ya tambayi almajiransa ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”
17 Sai wani mutum daga cikin taron ya amsa masa, ya ce, “Malam, ga shi na kawo maka ɗana, wanda yake da ruhu na zaman bebe a cikinsa. Ruhun yana hana shi magana.
18 Duk lokacin da abin ya tashi, yakan jefar da shi a ƙasa. Yakan sa shi yă fid da kumfa a baki, yana kuma cizon haƙora, jikinsa kuma yă miƙe da ƙarfi. Na yi wa almajiranka magana su fitar da shi, amma sun kāsa.”
19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku mutanen zamanin nan, marasa bangaskiya, har zuwa yaushe zan zauna tare da ku? Har yaushe kuma zan jimre da ku? Ku kawo mini yaron.”
20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya bugi yaron, jikinsa yana rawa, ya fāɗi yana ta birgima, bakinsa kuma yana ta fid da kumfa.
21 Sai Yesu ya tambayi baban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Baban ya ce, “Tun yana ƙarami.
22 Yakan jefa shi a wuta da cikin ruwa, don dai ya kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
23 Yesu ya ce masa, “Don me kake tambaya ko zan iya? Ai, dukan abu mai yiwuwa ne ga wanda yake ba da gaskiya.”
24 Nan da nan sai baban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya, ka taimake ni in ƙara gaskatawa!”
25 Da Yesu ya ga mutane suna ta zuwa da gudu, sai ya tsawata wa ƙazamin ruhun ya ce masa, “Kai ruhu mai hana yaron nan yin magana, na umarce ka ka fita daga cikinsa, kada ka sāke shiga cikinsa kuma.”
26 Aljanin kuwa ya yi ihu, ya kuma jijjiga yaron sosai, saˈan nan ya fita. Yaron kuma ya kwanta kamar gawa, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu.”
27 Amma Yesu ya kama hannunsa ya ɗaga shi, ya kuwa tashi a tsaye.
28 Da Yesu ya shiga cikin gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Don me mu muka kāsa fitar da ruhun?”
29 Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, irin wannan ruhun ba ya fita sai da adduˈa.”
30 Sai Yesu da almajiransa suka bar wurin, suka ci gaba da tafiya, suka wuce ta cikin Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
31 domin yana koya wa almajiransa cewa, “Za a ba da Ɗan Mutum ga hannun mutane, za su kuwa kashe shi. Bayan kwana uku kuma zai tashi.”
32 Amma ba su gane da abin da yake nufi ba, suna kuma jin tsoro su tambaye shi.
33 Suka kai Kafarnahum. Da Yesu ya shiga gida sai ya tambayi almajiransa ya ce, “A kan me kuke gardama a hanya?”
34 Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi gardama a kan ko wane ne mafi girma a cikinsu.
35 Sai Yesu ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Duk wanda yake so yă zama na fari, dole ne yă zama na ƙarshe duka, yă zama mai yi wa kowa hidima kuma.”
36 Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. Saˈan nan ya ɗauke shi ya rungume shi, ya ce musu,
37 “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ne ya karɓa. Wanda ya karɓe ni kuma, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
38 Ana nan, sai Yohanna ya ce masa, “Malam, mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka, muka kuwa hana shi, domin shi ba ya cikinmu.”
39 Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai, ba wanda zai yi wani aikin ban mamaki a cikin sunana yă kuma yi baƙar magana a kaina nan da nan.
40 Ai, duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
41 Ina gaya muku gaskiya, duk wanda ya ba ku ruwan sha, ko kwaf ɗaya, domin ku na Almasihu ne, gaskiya ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.”
42 “Zai zama abin tausayi ga wanda ya sa ɗaya daga cikin yara ƙananan nan masu ba da gaskiya gare ni yă yi zunubi. Zai fi masa kyau a ɗaura masa babban dutsen niƙa a wuya, a jefa shi cikin teku.
43 Idan kuwa hannunka yana sa ka ka yi zunubi, sai ka yanke shi mana! Ya fi kyau ka shiga rai na har abada da hannu ɗaya, da ka bar dukan hannuwanka ka shiga gidan wuta da hannu biyu. Wutar kuma ba za a iya kashe ta ba.
44 A wurin kuwa, tsutsotsin da suke cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba za a iya kashe ta ba.
45 Idan kuma ƙafarka tana sa ka ka yi zunubi, sai ka yanke ta mana! Ya fi kyau ka shiga rai na har abada da ƙafa ɗaya, da ka shiga gidan wuta da ƙafa biyu.
46 A wurin nan dai tsutsotsin da suke cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba za a iya kashe ta ba.
47 Idan kuma idonka ne yana sa ka ka yi zunubi, sai ka cire shi. Ya fi kyau ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka gidan wuta da ido biyu.
48 A wurin, “ ‘Tsutsotsin da suke cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba za a iya kashe ta ba.’ ”
49 “Za a tsabtace kowa da wuta, kamar yadda ake tsabtace hadaya da gishiri.
50 “Gishiri abu ne mai kyau, amma idan gishiri ya rabu da daɗinsa, da me za ku gyara shi? Sai ku kasance da gishiri a cikinku, ku yi zaman lafiya da juna.”