Skip to content

Hausa Bible

Markus 6

1 Yesu ya bar wurin ya koma garinsa, almajiransa kuwa suka tafi tare da shi.

2 Da Ranar Hutu ta Mako ta yi, sai ya fara koyarwa a majamiˈa. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce aka ba shi haka har yana yin abubuwan ban mamaki?”

3 “Wannan ba shi ne kafintan nan ba, ɗan Maryamu, ɗanˈuwan su Yakub, da Yusuf, da Yahuda, da kuma Siman? ˈYanˈuwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa daraja, sai dai a garinsa, da cikin ˈyanˈuwansa, da kuma mutanen gidansa.”

5 Yesu bai iya yin wani aikin ban mamaki a can ba, sai dai ya warkar da waɗansu marasa lafiya kaɗan ne kawai ta wurin taɓa su.

6 Ya yi mamaki saboda rashin bangaskiyarsu. Sai Yesu ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

7 Sai ya kira sha biyun nan, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan ƙazaman ruhohi.

8 Ya umarce su cewa, “Kada ku ɗauki wani abu domin tafiyar, ko abinci, ko jaka, ko kuɗi ma a aljihunku, sanda kawai za ku riƙe.

9 Amma ku sa takalmi, kada kuma ku riƙe wata riga ban da wadda take jikinku.

10 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a wurin har lokacin da za ku bar wannan garin.

11 Duk inda ba a karɓe ku ba, aka kuma ƙi jinku, in za ku tashi, sai ku kakkaɓe ƙurar ƙafafunku domin yă zama shaida a kansu.”

12 Haka fa suka tashi, suna waˈazi cewa mutane su tuba.

13 Suka fitar da aljanu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuma warkar da su.

14 Sai Sarki Hirudus ya ji labarin, saboda sunan Yesu ya bazu koˈina. Har waɗansu suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne aka tā da shi daga matattu, shi ya sa yake da ikon yin waɗannan ayyukan ban mamaki.”

15 Amma waɗansu suka ce, “Annabi Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Aˈa, wani annabi ne dabam, daga cikin annabawan dā.”

16 Da Hirudus ya ji maganar, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, wanda na cire masa kai, aka tā da shi daga matattu!”

17 Gama dā Hirudus da kansa ya ba da umarni aka kamo Yohanna, ya ɗaure shi a kurkuku. Hirudus ya yi haka saboda Hirudiya, matar ɗanˈuwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.

18 Don dā Yohanna ya yi ta gaya wa Hirudus cewa, “Bai kamata ka auri matar ɗanˈuwanka ba.”

19 Ashe, ita Hirudiya kuwa tana jin fushin Yohanna a zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami dama ba,

20 gama Hirudus yana tsoron Yohanna. Ya sani shi mutum mai adalci ne, mai tsarki kuma, shi ya sa Hirudus ya riƙe Yohanna da kyau. Yakan damu da yawa duk lokacin da Yohanna yake magana da shi, amma duk da haka yakan ji daɗin jin maganarsa.

21 A ƙarshe dai ta sami zarafi. A ranar haifuwar Hirudus, ya yi biki domin hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan Galili.

22 Da ˈyar Hirudiya ta shigo ta yi rawa a gaban Hirudus da baƙinsa, suka ji daɗi ƙwarai. Sai ya ce, “Me kike so? Kome da kika roƙa, sai in ba ki”.

23 Har da rantsuwa, sarki ya ce wa yarinyar, “Duk abin da kika roƙa zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24 Sai ta fita ta ce wa mamarta, “Me zan roƙa?” Mamar ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”

25 Nan da nan ta gudu ta koma wurin sarki ta ce, “Ina so yanzu-yanzu ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin kwano.”

26 Da jin wannan, sarki ya damu ƙwarai, amma saboda rantsuwar da ya riga ya yi, da kuma baƙinsa, bai so yă hana mata ba.

27 Sai ya aiki dogarinsa da umarni yă kawo kan Yohanna. Mutumin kuwa ya tafi ya cire kan Yohanna a kurkuku.

28 Ya kawo a cikin kwano, ya ba yarinyar, ita kuwa ta ba mamarta.

29 Da almajiran Yohanna suka ji labarin, sai suka zo suka ɗauki gawarsa, suka binne.

30 Manzannin da Yesu ya aika a dā suka komo wurinsa, suka faɗa masa dukan abubuwan da suka yi, da abin da suka koyar.

31 Ga shi kuwa mutane da yawa suna ta kaiwa da kawowa, har manzannin ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin da ba kowa, don ku ɗan huta.”

32 Sai suka shiga jirgin ruwa suka tafi wurin da ba kowa, sai su kaɗai.

33 Amma da suke barin wurin, waɗansu mutane da yawa suka gan su, suka kuma gane su. Sai suka bi tudu suna ta gudu da ƙafa daga garuruwa duka, suka riga su zuwa.

34 Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin suna kamar tumakin da ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.

35 Kusan fāɗuwar rana sai almajiransa suka zo wurinsa, suka ce masa, “Wannan wuri fa ba kowa. Ga shi kuwa rana ta kusan fāɗuwa.

36 Ka sallami mutanen su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su saya wa kansu abin da za su ci.”

37 Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku dai, ku ba su wani abu su ci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo abinci na kuɗin da ake biyan lebura yini ɗari biyu, mu ciyar da su?”

38 Ya ce musu, “Burodi nawa kuke da su? Ku je ku duba.” Da suka bincika suka ce, “Burodi biyar ne, da kifi biyu.”

39 Saˈan nan Yesu ya sa almajiransa su sa mutanen su zauna ƙungiya-ƙungiya a ɗanyar ciyawa.

40 Sai suka zauna ƙungiya-ƙungiya, waɗansu ɗari-ɗari, waɗansu kuma hamsin-hamsin.

41 Da ya ɗauki burodi biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi godiya ga Allah, ya rarraba, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa mutanen. Ya kuma raba wa dukan mutanen kifin nan biyu.

42 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi,

43 har suka tattara gutsattsarin burodin da kifin, aka sami kwando goma sha biyu cike.

44 Yawan mutanen da suka ci wannan abinci kuwa maza dubu biyar ne.

45 Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa su riga shi hayewa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.

46 Bayan da ya sallame su, sai ya hau wani tudu domin yă yi adduˈa.

47 Da rana ta fāɗi, jirgin yana tsakiyar teku, Yesu kuwa yana nan a kan tudu shi kaɗai.

48 Da ya ga suna fama da tuƙi, domin iska tana gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare, sai ga shi yana zuwa wurinsu, yana takawa a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su.

49 Amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu,

50 domin duk sun gan shi, suka firgita. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Kada ku damu! Ni ne, kada ku ji tsoro!”

51 Saˈan nan ya shiga cikin jirgin da su, iskar kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai,

52 saboda ba su san mene ne maˈanar ciyar da mutane dubu biyar nan ba, gama zuciyarsu ba ta fahimci maˈanar ba.

53 Saˈad da Yesu da almajiransa suka ƙetare tekun, suka sauka a yankin Janisarat, suka ɗaure jirgin a bakin tekun.

54 Da fitarsu daga jirgin ruwan, sai nan da nan mutane suka gane, ashe, Yesu ne.

55 Suka yi ta gudu daga koˈina a cikin yankin, suka yi ta kawo marasa lafiya a kan abin kwanciyarsu zuwa duk inda suka ji Yesu yake.

56 Duk inda ya tafi kuma, birni ko ƙauye ko filayen ƙauye, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi yă yarda marasa lafiyar su taɓa ko da bakin rigarsa ma. Dukan waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

Open Bible reader