Skip to content

Hausa Bible

Markus 15

1 Da sassafe manyan firistoci da shugabanni, da malaman Koyarwar Musa, da dukan sauran ˈyan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, gaban Bilatus.

2 Bilatus kuwa ya tambaye shi ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai ne ka faɗa haka.”

3 Sai manyan firistoci suka yi ta zarginsa a kan abubuwa da yawa.

4 Sai Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ga shi fa, ana zarginka a kan abubuwa da yawa, ba za ka ba da amsa ba?”

5 Amma har yanzu, Yesu bai ƙara yi wata magana ba, har abin ya dami Bilatus.

6 Abin da sarki ya saba yi a lokacin Bikin shi ne, yakan sakar musu ɗan kurkuku ɗaya wanda mutanen suka roƙa.

7 To, akwai wani mai suna Barabbas wanda yake a ɗaure a kurkuku, tare da ˈyan tawaye da suka kashe mutum a lokacin da aka yi tawaye.

8 Sai taron jamaˈa suka zo suka fara roƙon Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.

9 Bilatus ya amsa musu ya ce, “Kuna so in sakar muku sarkin Yahudawa?”

10 Gama ya gane cewa saboda kishi ne ya sa manyan firistoci suka ba da Yesu a hannunsa.

11 Amma manyan firistoci suka zuga jamaˈa su ce yă saki Barabbas a maimakon Yesu.

12 Sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi sarkin Yahudawa?”

13 Suka tā da murya suka ce, “A gicciye shi!”

14 Bilatus kuwa ya ce musu, “Don me? Wane laifi ne ya yi?” Sai suka ƙara tā da murya suna cewa, “A gicciye shi!”

15 Da yake Bilatus yana so yă faranta wa jamaˈa zuciya, sai ya sakar musu Barabbas. Bayan da ya sa aka yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi domin a gicciye shi.

16 Sojojin suka tafi da Yesu a zauren bariki, wato fādar gwamna wanda ake ce da shi “Firetoriyum”. Suka tara dukan sauran sojojin.

17 Suka sa masa wata riga irin ta sarakuna mai kalar jar garura, suka kuma yi wata hular mulki ta ƙaya, suka sa masa a kai.

18 Sai suka fara yi masa gaisuwa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!”

19 Suka kuma yi ta bugunsa a kai da sanda, suna tottofa masa miyau. Saˈan nan suka durƙusa wai suna yi masa ban girma.

20 Da suka gama yi masa baˈa haka, sai suka cire masa rigar mulki, suka sa masa nasa riguna. Saˈan nan suka kai shi waje domin a gicciye shi.

21 Suna cikin tafiya, sai ga wani mutum yana wucewa, mai suna Siman, mutumin Sayirin, baban Alekzanda da Rufus, yana zuwa daga ƙauye, suka sa shi dole yă ɗauki gicciyen Yesu.

22 Suka kai Yesu wani wuri mai suna Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.

23 A wurin suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.

24 Sai suka gicciye shi. Suka kuma rarraba rigunansa a tsakaninsu, suka yi ƙuriˈa a kansu domin su ga abin da kowa zai samu.

25 Da ƙarfe tara na safe ne suka gicciye shi.

26 A gungumen itacen kuwa an rubuta sanarwar zargin da aka yi masa cewa, “SARKIN YAHUDAWA.”

27 Suka kuma gicciye ˈyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a hannun damansa, ɗaya kuma a hannun hagunsa.

28 Wannan shi ne cikar annabcin da ya ce, “An lissafta shi a cikin masu laifi.”

29 Mutanen da suke wucewa suka yi ta yi maganganun reni, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! Kai da za ka rushe Haikali, za ka kuma gina shi cikin kwana uku,

30 to, ka ceci kanka ka sauko mana!”

31 Haka kuma manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka yi ta yi masa baˈa a tsakaninsu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma bai iya ceton kansa ba!

32 Bari wannan Almasihu, wai sarkin Israˈila, yă sauko yanzu daga gicciyen nan, don mu gani mu ba da gaskiya!” ˈYan fashin da aka gicciye tare da shi ma suka yi masa baƙar magana.

33 Da tsakar rana, sai duhu ya rufe dukan ƙasar, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

34 Saˈan nan da ƙarfe uku, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?”Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”

35 Da waɗanda suke tsaye a wurin suka ji haka, suka ce, “Ga shi, yana kiran annabi Iliya.”

36 Sai ɗayansu ya gudu, ya jiƙa soso da ruwan tsami daga ˈyaˈyan inabi, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu domin yă sha, ya ce, “Ku tsaya dai! Bari mu gani ko annabi Iliya zai zo yă sauko da shi.”

37 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, saˈan nan ya ja numfashinsa na ƙarshe sai ya mutu.

38 Sai labulen da yake cikin Haikali ya yage kashi biyu tun daga sama har ƙasa.

39 Lokacin da soja wanda yake tsaye a gaban Yesu ya ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Ba shakka, wannan mutum Ɗan Allah ne!”

40 Waɗansu mata kuma suka tsaya can da nesa suna kallo. Cikinsu kuwa akwai Maryamu daga Magadala, da Maryamu mamar Yakub ƙarami da Yusuf, da kuma Salomi.

41 Tun daga Galili ne waɗannan mata suka biyo shi suna yi masa hidima. Waɗansu mata kuma da yawa waɗanda suka zo tare da shi a Urushalima suna wurin ma.

42 Da yamma ta yi, ana shiri gama gobe Ranar Hutu ta Mako ce.

43 Sai wani mutum mai suna Yusuf daga Arimatiya ya zo. Shi ɗan majalisa ne, mai mutunci kuwa, wanda yake marmarin mulkin Allah yă zo. Ya yi ƙarfin hali ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

44 Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira soja ɗin ya tambaye shi ko gaskiya ne Yesu ya riga ya mutu.

45 Da ya tabbatar daga bakin sojan nan, sai ya ba Yusuf jikin.

46 Yusuf kuwa ya sayo yadin lilin, ya sauko da jikin Yesu, ya nannaɗe shi a yadin lilin, ya sa shi a kabarin da aka haƙa a jikin dutse. Saˈan nan ya gangaro da wani dutse ya rufe bakin kabarin.

47 Maryamu daga Magadala da Maryamu mamar Yusuf suna kallo, suka ga inda aka kwantar da jikin Yesu.

Open Bible reader