Skip to content

Hausa Bible

Luka 10

1 Bayan haka, Ubangiji ya kuma zaɓi waɗansu mutum sabaˈin da biyu, ya aike su biyu-biyu su yi gaba zuwa garuruwa da wuraren da shi kansa ya shirya zai je.

2 Sai ya ce musu, “Girbin yana da yawa, amma masu aikin kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi mai gonar yă aiko da masu aiki su yi masa girbi.

3 Sai ku tafi. Ga shi, ina aikanku kamar tumaki cikin kyarketai.

4 Kada ku ɗauki kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa a kan hanya.

5 Duk gidan da kuka shiga, ku fara cewa, ‘Salamarku mutanen gida!’

6 Idan akwai ɗan salama a gidan, to, bari gaisuwarku ta salama ta kasance tare da shi. In kuwa babu, sai gaisuwarku ta salama ta komo muku.

7 Ku zauna a wannan gida, ku ci, ku sha duk irin abin da aka ba ku, domin ya kamata a biya wa mai yin aiki hakkinsa. Kada ku bi gida-gida.

8 Duk garin da kuka shiga, in an karɓe ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.

9 Ku warkar da marasa lafiya da suke a garin, ku kuma faɗa wa mutanen cewa, ‘Mulkin Allah ya zo kusa da ku.’

10 Amma duk garin da kuka shiga, aka ƙi karɓarku, ku bi titi-titi, kuna cewa,

11 ‘Ko ƙurar garinku da ta manne mana a ƙafafu ma, mun kakkaɓe muku. Amma ku sani cewa mulkin Allah ya zo kusa da ku!’

12 Ina dai gaya muku, a Ranar Ƙarshe, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan gari.

13 “Kaitonki, Korasin! Kaitonki, Betsaida! Gama, da ayyukan ban mamaki da aka yi a cikinku ne aka yi a Taya da Sidon, da sun tuba tun tuni, sun sa tsummoki, sun zauna, suna zuba wa kansu toka.

14 A Ranar Shariˈa, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku.

15 Ke kuma Kafarnahum! Kina tsammani ɗaukaka ki za a yi zuwa sama ne? A ina! Ƙasƙantar da ke za a yi har zuwa wurin zaman matattu!

16 “Duk wanda ya ji ku, ni ne ya ji. Duk wanda kuma ya ƙi ku, ni ne ya ƙi. Duk wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”

17 Mutum sabaˈin da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har aljanu ma suna jinmu idan mun umarce su cikin sunanka!”

18 Yesu ya amsa musu, ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗo daga sama kamar walƙiya.

19 Ku ji nan! Na ba ku ikon da za ku taka macizai da kunamai, ku kuma sha kan dukan ikon masu gāba, babu kuma abin da zai faru da ku.

20 Duk da haka kada ku yi murna don aljanu sun ji ku, ku yi murna dai domin an rubuta sunayenku a sama.”

21 A wannan lokaci, Yesu cike da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da duniya, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ˈyan yara. Haka ne ya Uba, gama wannan shi ne abin da ya yi maka kyau.

22 “Ubana ya ba ni dukan abu. Ba wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban kaɗai, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai shi Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so yă bayyana masa.”

23 Sai ya juya wurin almajiran, ya ce musu a ɓoye, “Ku masu albarka ne da waɗannan abubuwa suka faru a idanunku!

24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa, sun so su ga abin nan da kuke gani amma ba su sami dama ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba!”

25 Sai ga wani malamin Koyarwar Musa ya miƙe tsaye domin yă gwada Yesu. Ya tambaye shi ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai na har abada?”

26 Yesu ya amsa masa ya ce, “Me Koyarwar Musa ta ce? Yaya kuma kake fassarta ta?”

27 Mutumin ya ce, “An ce, ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka’.”

28 Yesu ya ce masa, “Ka faɗa daidai. To, ka yi haka, za ka rayu.”

29 Amma malamin Koyarwar ya so yă nuna cewa ba shi da laifi. Saboda haka sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”

30 Yesu ya amsa masa ya ce, “An taɓa yin wani mutum wanda ya tashi daga Urushalima yana gangara zuwa Yeriko. Sai ya haɗu da ˈyan fashi, suka ƙwace masa kayansa, suka yi masa mugun dūka, suka bar shi a wurin bakin rai da mutuwa.

31 Ana nan sai ga shi wani firist ya biyo kan wannan hanya. Da ya ga mutumin nan a kwance, sai ya bi ta gefe ya wuce abinsa.

32 Haka ma wani mutumin zuriyar Lawi, da ya zo wurin ya gan shi a kwance, shi ma ya bi ta gefe, ya wuce abinsa.

33 Ana nan dai, sai hanya ta kawo wani mutumin Samariya inda yake. Da ya ga mutumin nan, sai tausayi ya kama shi.

34 Ya je wurinsa, ya zuba mai da ruwan inabi a mikinsa, saˈan nan ya ɗaɗɗaura su. Ya ɗauke shi, ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauki, ya yi jinyarsa.

35 Washegari, sai ya ɗauki yawan kuɗin da lebura zai samu a kwana biyu ya ba mai masaukin, ya ce, ‘Ka lura mini da wannan mutum, idan na dawo, zan biya ka duk abin da ka kashe a kansa bayan wannan.’ ”

36 A ƙarshe, sai Yesu ya tambayi malamin Koyarwar nan ya ce, “A ganinka wane ne a cikin mutanen nan uku ya nuna halin maƙwabci ga mutumin nan da ya fāɗi a hannun ˈyan fashi?”

37 Malamin Koyarwa ya ce, “Wannan da ya ji tausayinsa.” Yesu ya ce masa, “Sai kai ma ka tafi ka yi haka.”

38 Yesu da almajiransa suna cikin tafiya ke nan, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta karɓe shi a gidanta.

39 Ita Marta tana da ˈyarˈuwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna kurkusa da Ubangiji tana jin maganarsa.

40 Marta kuwa aikin abinci ya ɗauke mata hankali, sai ta je wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ˈyarˈuwata ta bar mini yin abinci ni kaɗai ba? Faɗa mata ta zo ta taimake ni mana.”

41 Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kin kuma damu a kan abubuwa da yawa.

42 Amma abu ɗaya tak ake bukata. Maryamu ta riga ta zaɓi abu mai kyau, wanda ba za a iya karɓe mata ba.”

Open Bible reader