Hausa Bible
Yakubu 5
1 To, ku saurara ku masu arziki! Ku yi kuka da ihu saboda azabar da take zuwa a kanku.
2 Arzikinku duka ruɓaɓɓe ne, kuma ƙwari sun cinye tufafinku.
3 Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar nan da suka yi ita ce za ta zama shaida a kanku, za ta kuma cinye naman jikinku kamar wuta. Kun dai tara wa kanku dukiya a kwanakin nan na ƙarshe.
4 Gama albashin maˈaikatan gonakinku, waɗanda kuka ƙi biyansu saboda halin cutarku, yana kuka ga Allah. Haka nan kukan masu yi muku girbi a gonakinku ya kai kunnen Allah Ubangiji Mai Runduna.
5 Kun yi zama a duniya cikin jin daɗi, kuna ci da sha na ganin dama. To, kun yi wa kanku kiwo ne kuna zaman jira ranar yanka.
6 Kun hukunta marasa laifi, kuka kuma kashe su, ba su kuwa yi gāba da ku ba.
7 Saboda wannan, ˈyanˈuwa, ku yi zaman haƙuri har sai Ubangiji ya dawo. Ku dubi irin haƙurin da manomi yakan yi lokacin da yake jira gonarsa ta ba da amfani mai kyau. Da yawan haƙuri yakan jira ruwan shuka da ruwan ƙarshe.
8 Sai ku ma ku kasance da haƙuri. Ku ƙarfafa zuciyarku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa.
9 ˈYanˈuwa, kada ku yi gunaguni da juna, domin kada a hukunta ku. Ga shi, mai shariˈa ya kusan zuwa, har yana a bakin ƙofa.
10 ˈYanˈuwa, ku lura da annabawan da suka yi magana da sunan Ubangiji. Ku bi gurbi na jimrewarsu cikin wahala.
11 Ga shi, waɗanda suka jimre mukan ce da su masu albarka ne. Kun dai ji irin jimrewar da Ayuba ya yi, kun kuma san yadda Ubangiji ya albarkace shi a ƙarshe. Gama Ubangiji mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.
12 Fiye da kome dai, ˈyanˈuwana, kada ku yi rantsuwa ko kaɗan. Kada ku yi rantsuwa da sama, ko da ƙasa, ko a kan wani abu. Sai dai ku ce, “I” kawai, ko kuwa ku ce, “Aˈa” kawai domin kada ku shiga hukuncin Allah.
13 Ko akwai wani mai shan wahala a cikinku? To, sai yă yi adduˈa. Ko akwai wani mai murna? To, sai yă yi waƙoƙin yabo.
14 Ko akwai wani mai rashin lafiya a cikinku? Sai yă kira dattawan jamaˈar masu bin Yesu su yi masa adduˈa, suna shafe shi da mai a cikin sunan Ubangiji.
15 Irin wannan adduˈar da aka yi cikin bangaskiya, za ta warkar da marar lafiyar. Ubangiji kuma zai warkar da shi. In kuma ya yi zunubi, za a gafarta masa.
16 Saboda haka ku furta wa juna laifofinku, kuna yi wa juna adduˈa domin a warkar da ku. Adduˈar mai adalci tana da ƙarfin aiki da iko sosai.
17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya nace sosai cikin adduˈa domin kada a yi ruwan sama, sai kuwa ba a yi ruwa a ƙasar ba har shekara uku da wata shida.
18 Bayan haka ya sāke yin adduˈa, sai sama ya ba da ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
19 ˈYanˈuwana, idan ɗaya daga cikinku ya rabu da hanyar gaskiya, waninku kuma ya dawo da shi kan hanya,
20 sai yă sani fa duk wanda ya dawo da mai zunubi a kan hanya ya ceci ran mai zunubin daga mutuwa, kuma wannan zai zama hanyar gafarta zunubai masu ɗumbun yawa.