Hausa Bible
Galatiyawa 5
1 Domin zaman ˈyanci shi ne dalilin da Almasihu ya ˈyantar da mu. Saboda haka sai ku tsaya da ƙarfi, kada ku sāke miƙa kanku ga gungumen bauta.
2 To, ku ji ni. Ni Bulus ina gaya muku, in kun yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba shi da amfani gare ku ke nan.
3 Ina sāke tuna muku cewa duk wanda ya yarda ya bi dokar yin kaciya, to, ya zama dole yă bi dukan Koyarwar Musa ke nan.
4 Ku da kuke ƙoƙarin samun zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa, kun riga kun fid da kanku daga bin Almasihu ke nan. Kun kauce wa alherin Allah.
5 Gama ta wurin Ruhu da kuma ta wurin bangaskiya, muna jira tare da sa zuciya a kan samun adalci.
6 Gama in muna cikin Almasihu Yesu, ko da kaciya, ko da rashin kaciya ba wani abu ba ne a gare mu. Amma abin da muka fi kula da shi, shi ne bangaskiya wadda take nuna kanta ta wurin ƙauna.
7 Da farko kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku yin biyayya da gaskiya?
8 Lallai ruɗin da aka yi muku bai zo daga wurin Allah wanda ya kira ku ba.
9 Kamar yadda akan faɗa, “Ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa babban burodi yă kumbura.”
10 Saboda zumuncinmu cikin aikin Ubangiji, na tabbata ba za ku bi wani raˈayi dabam da nawa ba. Kuma shi wanda yake tā da hankalinku zai sha hukunci, ko shi wane ne.
11 ˈYanˈuwa, idan har yanzu ina waˈazin yin kaciya ne, to, don me har yanzu mutane suke tsananta mini? Idan haka ne, ai, maganata game da mutuwar Almasihu a kan gicciye ba za ta zama abin tuntuɓe ga kowa ba!
12 Ai, masu tā da hankalinku ɗin nan, gwamma su ci gaba su mai da kansu bābānni gaba ɗaya!
13 ˈYanˈuwana, ku dai an kira ku musamman domin ˈyanci. Amma ku lura kada ˈyancin nan naku yă zama hujjar bin halin mutuntaka. Maimakon haka bari ˈyancin nan yă kai ku ga yi wa juna bauta cikin ƙauna.
14 Gama dukan Koyarwar Musa an haɗa ta a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
15 Amma in kuna faɗa da juna, kuna cizo, kuna cinye juna kamar namomin daji, ku mai da hankali fa, kada dukanku gaba ɗaya ku halaka!
16 Nufina shi ne, ku yi rayuwa yadda Ruhu ya bi da ku. Idan kun yi haka, ba za ku bi halin mutuntaka ba.
17 Don halin mutuntaka ba ya yarda da Ruhu, Ruhu kuma ba ya yarda da halin mutuntaka. Waɗannan halayen biyu suna gāba da juna. Shi ne ya sa ba ku iya yin abin da kuke so ku yi.
18 In Ruhun Allah ne yake bi da ku, to, ba a ƙarƙashin Koyarwar Musa kuke ba.
19 Ayyukan da halin mutuntaka yake haifar suna nan a fili. Su ne iskanci, da halin lalata, da halin neman jin daɗi na rashin kunya,
20 da bautar gumaka, da maitanci, da ƙin juna, da faɗa, da kishin juna, da fushi, da sonkai, da rabuwa, da yin tawaye,
21 da kishi, da buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da kuma sauran irin abubuwa kamar haka. Ina yi muku gargaɗi, kamar yadda na riga na yi a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa ba za su sami gādo a mulkin Allah ba.
22 Amma halin da Ruhun Allah yake haifar shi ne ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,
23 da tawaliˈu, da kuma shan ƙarfin shaˈawar jiki. Ai, babu dokar da ta hana waɗannan abubuwa.
24 Kuma dukan waɗanda suke na Almasihu Yesu sun gicciye halin mutuntaka da mugayen abubuwa iri-iri da jiki yake marmarinsu.
25 Tun da yake Ruhu ne ya ba mu rai, bari Ruhu yă bi da mu kuma cikin dukan zamanmu.
26 Kada mu zama masu girman kai ko masu tā da hankalin juna, ko masu jin kishin juna.