Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 18

1 Bayan haka Bulus ya bar Atina ya tafi Korinti.

2 A can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, ɗan garin Fontus. Akila da matarsa Biriskila ba su daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, don Kalaudiyus ya yi doka cewa dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.

3 Da yake sanaˈarsu iri ɗaya ce da tasa, wato, ta ɗinkin tenti, sai ya yi zama tare da su. Suka yi ta aiki tare.

4 Kowace Ranar Hutu ta Mako kuwa Bulus ya dinga muhawara a majamiˈa, yana ƙoƙari yă rinjaye Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba.

5 Saˈad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya ba da dukan lokacinsa a kan yin waˈazi, yana tabbatar wa Yahudawa cewa, Yesu shi ne Almasihu.

6 Amma suka yi masa musū, suna zaginsa. Domin haka sai ya kakkaɓe tufafinsa ya ce musu, “Alhakin jininku a wuyanku! Ni dai ba ni da laifi. Daga yau wurin waɗanda ba Yahudawa ba za ni.”

7 Sai ya tashi daga wurin ya tafi gidan wani mutum mai suna Titiyus Yustus, mai bautar Allah, gidansa kuwa yana kusa da majamiˈa sosai.

8 Sai Kirisbus, shugaban majamiˈa ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da mutanen gidansa duka. Waɗansu Korintiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus, suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.

9 Wata rana da dare, Ubangiji ya nuna wa Bulus ruˈuya, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro. Ka yi ta yin waˈazi, kada ka yi shiru,

10 gama ina tare da kai. Ba wanda zai sa hannu yă yi maka wani abu, don ina da mutane da yawa a wannan birni.”

11 Bulus ya zauna a wurin har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar musu kalmar Allah.

12 Amma lokacin da Galiyo yake mulkin ƙasar Akaya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kai shi gaban masu shariˈa.

13 Suka ce, “Wannan mutum yana ƙoƙari yă sa mutane su bauta wa Allah ta hanyar da Koyarwa ta hana.”

14 Bulus yana shirin yă yi magana ke nan, sai Galiyo ya ce wa Yahudawa, “Da ma wani laifi ya yi, ko mugun laifi, da sai in ji ku.

15 Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma koyarwarku, ai, sai ku ji da shi da kanku. Ni kam, ban yi niyyar yin shariˈa kan irin waɗannan abubuwa ba.”

16 Sai ya kore su daga ɗakin shariˈar.

17 Sai dukansu suka kama Sostanus shugaban majamiˈar, suka yi masa dūka a gaban ɗakin shariˈa. Amma Galiyo bai ko kula ba.

18 Bayan wannan sai Bulus ya ƙara ˈyan kwanaki a Korinti. Saˈan nan ya yi wa masu bi ban kwana. Ya shiga jirgin ruwa tare da Biriskila da Akila suka kama hanya zuwa Suriya. Amma kafin su tashi Bulus ya aske kansa a Kankiriya gama ya ɗauki wata rantsuwa.

19 Da suka kai Afisa, a can ne Bulus ya bar Biriskila da Akila, shi kuwa ya shiga majamiˈa ya yi muhawara da Yahudawa.

20 Sai suka roƙe shi yă ɗan ƙara zama a wurinsu, amma bai yarda ba.

21 Amma da zai bar su, ya ce, “Zan dawo wurinku idan Allah ya yarda.” Saˈan nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

22 Da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da jamaˈar masu bi, saˈan nan ya tafi Antakiya.

23 Bayan ya ɗan daɗe kaɗan a wurin, sai ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ƙasar Firijiya, yana bin gari-gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.

24 Ana nan sai wani Bayahude mai suna Afollos ya zo Afisa. Shi kuwa ɗan garin Alekzandiriya ne, mai iya magana, ya kuma san Rubutacciyar Maganar Allah sosai-sosai.

25 An koyar da shi cikin hanyar Ubangiji. Yakan nuna ƙwazo sosai cikin magana, yana kuma koyar da ainihin gaskiya game da Yesu. Amma fa baftismar Yohanna kaɗai ne ya sani.

26 Sai ya fara waˈazi babu tsoro a majamiˈa. Da Biriskila da Akila suka ji maganarsa, sai suka ɗauke shi suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai-sosai.

27 Da Afollos ya so yă ƙetare zuwa ƙasar Akaya, masu bi suka taimake shi. Suka rubuta wa masu bi na Akaya wasiƙa domin su karɓe shi hannu biyu-biyu. Da ya kai can kuwa ya zama da taimako sosai ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Allah,

28 gama ya yi nasara cikin magana da Yahudawa ƙwarai a gaban jamaˈa, yana tabbatar musu daga cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa Yesu shi ne Almasihu.

Open Bible reader