Skip to content

Hausa Bible

Romawa 6

1 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba da rayuwar zunubi domin alherin Allah yă ƙaru ne?

2 Ina! Ko kaɗan! Ai, mun riga mun mutu ga zunubi. Yaya kuma za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa?

3 Ashe, ba ku sani ba dukanmu da aka yi mana baftisma zuwa cikin Almasihu Yesu, zuwa cikin mutuwarsa ne aka yi mana baftismar?

4 Wato, ta wurin baftismarmu an binne mu tare da shi, mun kuma zama ɗaya da shi cikin mutuwarsa, domin yadda aka tā da Almasihu daga matattu ta wurin ikon nan mai ɗaukaka na Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

5 Gama da yake mun zama ɗaya da shi cikin irin mutuwarsa, ba shakka za mu zama ɗaya da shi cikin tashinsa daga matattu.

6 Mun kuwa sani cewa an riga an gicciye mutuntakarmu ta dā tare da shi, domin a kawar da ikon zunubin nan da yake cikin jikinmu. An yi haka domin kada mu ƙara zama bayin zunubi.

7 Gama idan mutum ya mutu, ya sami ˈyanci daga ikon zunubi ke nan.

8 Idan mun riga mun mutu tare da Almasihu, mun ba da gaskiya za mu rayu tare da shi kuma.

9 Gama mun sani cewa an tā da Almasihu daga matattu, kuma ba zai sāke mutuwa ba, wato, mutuwa ba ta da sauran iko a kansa.

10 Mutuwar nan da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari domin yă karye ikon zunubi, amma rayuwar da yake yi, rayuwa ga Allah ne.

11 Haka ku kuma ku ɗauki kanku kamar matattu ne ga ikon zunubi, amma rayayyu ne ga Allah ta wurin Almasihu Yesu.

12 Saboda haka kada ku yarda zunubi ya yi mulki a cikin jikin nan naku mai mutuwa, har yă sa ku ku bi muguwar shaˈawarsa.

13 Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku ga zunubi su zama kayan yin aikin mugunta. Sai dai ku miƙa kanku ga Allah yadda ya dace da waɗanda aka cire su daga hannun mutuwa zuwa samun rai, ku kuma miƙa gaɓoɓinku ga Allah domin su zama kayan yin aikin adalci.

14 Gama zunubi ba zai yi mulki a kanku ba, tun da yake ba a ƙarƙashin Koyarwar Musa kuke ba, amma a ƙarƙashin alherin Allah.

15 Yaya ke nan? Wato, sai mu yi zunubi saboda Koyarwar ba ta da iko a kanmu, sai dai alherin Allah? Ina! Ko kaɗan!

16 Ba ku sani ba idan kun miƙa kanku domin ku zama masu biyayya ga wani, kun zama bayi ke nan a hannun wanda kuke yi masa biyayya? Kuna iya zama bayin zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuma bayin biyayya ga Allah, wanda yake kai ga adalci.

17 Amma godiya ta tabbata ga Allah, domin ko da yake a dā ku bayin zunubi ne, amma yanzu kam kuna biyayya da dukan zuciyarku ga irin koyarwar nan da aka sa ku a ƙarƙashinta.

18 An ˈyantar da ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga adalci.

19 Ina kuwa yi muku magana kamar yadda ɗan Adam yake magana ne, saboda kāsawarku ta mutuntaka ne. Kamar yadda a dā kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku ga bautar abubuwan ƙazanta, da kuma ga mugunta wadda take ta ƙaruwa kawai, haka kuma yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar adalci, domin ku zama waɗanda aka keɓe da tsarki ga Allah.

20 A lokacin da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

21 Wane amfani kuka samu daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ai, sakamakon waɗannan abubuwa mutuwa ne!

22 Amma yanzu an ˈyantar da ku daga bautar zunubi, kun kuma zama bayin Allah. Amfanin da kuke samuwa daga wannan shi ne ya kai ku ga rayuwa mai tsarki, wadda kuma take haifa muku rai na har abada.

23 Gama sakamakon zunubi shi ne mutuwa, amma kyautar Allah ita ce rai na har abada ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Open Bible reader