Skip to content

Hausa Bible

Romawa 2

1 Saboda haka kai mai hukunta wani, ba ka da wata hujja, ko kai wane ne. Gama a saˈad da kake hukunta wani, kana hukunta kanka ne, domin laifin da kake ganin wani da shi, shi ne kai ma kake aikatawa.

2 Mun san cewa hukuncin Allah daidai ne a kan waɗanda suke yin abubuwan nan.

3 Kai mutum! Ga shi kuwa kai da kanka kana aikata laifin nan da kake ganin wani da shi! Kana tsammani za ka kuɓuce wa hukuncin Allah?

4 Ko kuwa kana rena yawan alherin Allah, da haƙurinsa, da rashin saurin fushin da yake yi gare ka? Ashe, ba ka sani cewa nufin alherin Allah shi ne yana jawo ka ga tuba ba?

5 Amma ta dalilin taurin kan da kake yi da taurin zuciyar da kake da shi, kana tara wa kanka hukunci wanda yake jiranka a Ranar fushin Allah, a lokacin da za a bayyana hukuncin nan da yake bisa ga adalcin Allah.

6 Allah zai sāka wa kowa bisa ga ayyukansa.

7 Akwai waɗanda suke neman ɗaukaka da daraja da rai marar ƙārewa, ta wurin naciyarsu ga aikata alheri cikin haƙuri, su ne kuma Allah zai sāka musu da rai na har abada.

8 Amma waɗanda suke masu sonkai, waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma yin mugunta, za a sāka musu da fushi da kuma haushi.

9 Azaba da wahala su ne suke jiran kowane mutum mai aikata mugunta, da farko ga Yahudawa, saˈan nan ga waɗanda ba Yahudawa ba.

10 Amma duk mai aikata nagarta zai sami ɗaukaka da girma da salama, da farko ga Yahudawa, saˈan nan ga waɗanda ba Yahudawa ba.

11 Gama Allah ba mai nuna bambanci ba ne.

12 Duk masu yin zunubi ba tare da sanin Koyarwar Musa ba, za su halaka ba tare da Koyarwar ba, amma duk masu yin zunubi cikin sanin Koyarwar, za a hukunta su bisa ga Koyarwar.

13 Gama ba jin Koyarwar kawai shi ne yakan sa mutane su zama da adalci a gaban Allah ba, amma yin biyayya da Koyarwar shi ne yakan sa a iya ce da su masu adalci.

14 Waɗanda ba Yahudawa ba ba su da Koyarwar Musa. Duk da haka wani lokaci suna yin abin da Koyarwar ta umarta, bisa ga abin da zukatansu sun ba su. Ashe kuwa, marasa Koyarwar nan suna da koyarwa tasu ke nan.

15 Ayyukansu sun nuna cewa abin da Koyarwar ta ce a yi yana nan a rubuce cikin zukatansu. A cikin tunanin zukatansu kuwa akwai shaida game da wannan, gama tunaninsu yakan same su da laifi a wani lokaci, a wani lokaci kuma ba ya samunsu da laifi.

16 Saboda haka, kamar yadda labari mai daɗin nan da nake waˈazinsa yake faɗa, haka zai zama a Ranar da Allah ta wurin Almasihu Yesu zai shariˈanta dukan abubuwan da suke a ɓoye a tunanin mutane.

17 To, kai mai ce da kanka Bayahude fa? Kana dogara ga Koyarwar Musa, kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah,

18 kana cewa wai ka san nufin Allah, kuma kana da ganewa bisa ga Koyarwar Musa yadda za ka zaɓi abin da yake daidai.

19 Ka amince kai kanka kai mai jagoran makafi ne, haske ga waɗanda suke cikin duhu,

20 mai koyar da wawaye, da kuma malami ga masu tunanin yara. Gama ka tabbata cewa a cikin Koyarwar Musa ne kana da cikakken sani da ainihin gaskiya.

21 To, kai mai koya wa waɗansu, ka koya wa kanka mana! Kai mai yin waˈazi cewa kada a yi sata, kai ba ka sata?

22 Kai mai cewa kada a yi zina, ba ka yin zina? Kai mai ƙyamar gumaka, ba ka sata daga haikalin gumaka?

23 Kai mai taƙama da Koyarwar Musa, ba ka ɓata sunan Allah ta wajen karya Koyarwarsa ba?

24 Kamar yadda yake a rubuce cikin Maganar Allah, “Saboda ku Yahudawa ake yin maganar saɓo game da sunan Allah a cikin waɗanda ba Yahudawa ba.”

25 Idan kana biyayya da Koyarwar Musa, kaciyarka tana da amfani ke nan. Amma idan rashin biyayya kake yi ga Koyarwar Musa, zai zama kamar ba a yi maka kaciya ba.

26 Ashe idan waɗanda ba masu kaciya ba suna aikata abin da Koyarwar Musa ta ce a yi, Allah ba zai ɗauke su kamar masu kaciya ke nan ba?

27 Waɗanda su ba masu kaciya ba ne a jiki amma suna aikata abin da Koyarwar ta ce a yi, za su yi maka hukunci, kai da kake da Koyarwar Musa a rubuce, mai kaciya kuma, amma kana karya Koyarwar.

28 Gama Bayahude na gaske ba mutum ne wanda yake Bayahude bisa ga jiki kurum ba, kuma kaciya ta ainihi ba bisa ga alamar jiki take ko ta yankan fata ba.

29 A maimakon haka, Bayahude na gaske shi ne wanda yake Bayahude a zuciya, kuma kaciya ta gaske ita ce kaciya ta zuciya, wato abin da Ruhu ne ya yi, ba ta wurin Koyarwar da aka rubuta ba. Irin wannan mutum kuwa Allah ne yakan yi masa yabo, ba ɗan Adam ba.

Open Bible reader