Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 27

1 Da gari ya waye, sai dukan manyan firistoci da shugabannin jamaˈa suka yi shawara su kashe Yesu.

2 Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.

3 Saˈad da Yahuda wanda ya bashe shi ya ga an yanke wa Yesu hukuncin mutuwa, sai ya yi baƙin ciki, ya dawo wurin manyan firistoci, da shugabanni, ya mayar musu da kuɗin azurfa talatin ɗin nan.

4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Amma suka ce, “Ina ruwanmu? Wannan damuwarka ce.”

5 Sai ya zubar da kuɗin azurfar nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.

6 Amma manyan firistoci suka kwashi kuɗin suka ce, “Bai kamata a sa kuɗin nan a wurin ajiyar kuɗin Haikali ba, domin kuɗin jini ne.”

7 Sai suka yi shawara, suka sayi wani fili da kuɗin. Ana ce da filin, Filin Mai Ginin Tukwane, don wurin yă zama wurin binne baƙi in sun mutu.

8 Domin haka har wa yau ana ce da filin, Filin Jini.

9 Ta haka aka cika abin da annabi Irmiya ya faɗa cewa, “Aka ɗauki kuɗin azurfa talatin, kuɗin da mutanen Israˈila suka yarda a biya a kansa ke nan.

10 Suka sayi filin mai ginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umarce ni.”

11 To, Yesu yana nan tsaye a gaban gwamna ke nan, sai gwamnan ya tambaye shi ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Kai ne ka faɗa haka.”

12 Amma da manyan firistoci da shugabanni suka zarge shi, bai ce kome ba.

13 Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji abubuwan nan da suka zarge ka a kai ba?”

14 Amma Yesu bai amsa masa ko tambaya ɗaya ba, har gwamna ya yi mamaki sosai.

15 To, a lokacin Bikin Ƙetarewa kuwa, gwamna ya saba sakar wa mutane mai laifi guda ɗaya da suke so.

16 A lokacin akwai wani sanannen ɗan kurkuku mai suna Barabbas.

17 Da Yahudawa suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sake muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake ce da shi Almasihu?”

18 Gama Bilatus ya sani saboda kishi ne suka ba da Yesu.

19 Da Bilatus ya zauna a wurin shariˈa, sai matarsa ta aiko a ce masa, “Ka fita shaˈanin marar laifin nan, domin yau na sha wahala sosai a mafarki a kansa.”

20 To, sai manyan firistoci suka zuga jamaˈa su ce a saki Barabbas, a kashe Yesu.

21 Gwamnan kuwa ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sake muku?” Sai suka ce, “Barabbas.”

22 Sai Bilatus ya ce musu, “To, me zan yi da Yesu da ake ce da shi Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”

23 Bilatus ya ce, “Saboda me? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma mutanen sun ƙara tā da murya suna cewa, “A gicciye shi!”

24 Da Bilatus ya ga ba abin da zai iya yi, kuma mutanen suna shirin tā da hankali, sai ya ɗebi ruwa ya wanke hannuwansa a gaban mutane, ya ce, “Ni dai, ba ruwana da alhakin jinin marar laifin nan. Wannan ruwanku ne.”

25 Sai mutanen duka suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa yă zauna a wuyanmu, mu da ˈyaˈyanmu!”

26 Saˈan nan ya sake musu Barabbas. Bayan ya sa aka yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.

27 Daga nan sojojin gwamna suka kai Yesu cikin fādar gwamna, suka tara dukan ƙungiyar sojojin a kansa,

28 suka tuɓe masa kaya, suka yafa masa wata jar riga irin ta sarakuna.

29 Suka yi wata hular mulki ta ƙaya, suka sa masa a kai, suka sa ya riƙe sanda a hannunsa na dama, saˈan nan suka durƙusa a gabansa suna yi masa baˈa suna cewa, “Ranka yă daɗe, Sarkin Yahudawa!”

30 Suka tottofa masa miyau, suka karɓi sandan suka bubbuge shi da ita a kai.

31 Da suka gama yi masa baˈa, sai suka cire masa jar rigar, suka sa masa rigunansa, suka tafi da shi domin su gicciye shi.

32 Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani mutumin Sayirin, mai suna Siman, suka sa shi dole yă ɗauki gicciyen Yesu.

33 Suka kai wurin da ake ce da shi Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.

34 Suka ba shi ruwan inabi haɗe da wani abu mai ɗaci domin yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.

35 Da suka gicciye shi, sai suka jefa ƙuriˈa suka raba rigunansa.

36 Bayan haka sai suka zauna a nan suna gadinsa.

37 Daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “WANNAN SHI NE YESU, SARKIN YAHUDAWA.”

38 Aka kuma gicciye waɗansu ˈyan fashi guda biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya a hagunsa.

39 Mutanen da suke wucewa suka yi ta yi masa reni suna kaɗa kai,

40 suna cewa, “Kai da ka ce za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ka ceci kanka mana! Idan kai Ɗan Allah ne, ka sauko daga gicciyen mana!”

41 Haka kuma manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa, da shugabanni suka dinga yi masa baˈa, suna cewa,

42 “Ya ceci waɗansu, ya kāsa ceton kansa. Idan shi Sarkin Israˈila ne, bari yă sauko daga gicciyen mana, saˈan nan za mu gaskata shi.

43 Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, idan yana so, gama ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”

44 Haka ma ˈyan fashin da aka gicciye su tare, su ma suka yi masa baƙar magana.

45 Tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasar duka, har zuwa wajen ƙarfe uku na yamma.

46 Wajen ƙarfe uku kuma Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”

47 Saˈad da waɗansu da suke tsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan yana kiran Iliya ne.”

48 Sai nan da nan wani ya yi gudu, ya je ya ɗauki soso, ya jiƙa shi a cikin ruwan tsami daga ˈyaˈyan inabi, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha.

49 Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

50 Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, saˈan nan ya saki ransa.

51 Sai labulen da yake cikin Haikali ya yage kashi biyu, daga sama zuwa ƙasa. Aka yi rawar ƙasa, duwatsu suka farfashe.

52 Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suka mutu suka tashi da rai

53 suka fiffito daga kaburburansu. Bayan Yesu ya tashi daga matattu, sai suka shiga birni mai tsarki, mutane da yawa suka gan su.

54 A lokacin da babban sojan Roma da sauran waɗanda suke gadin Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma duk abin da ya faru, sai suka ji tsoro sosai, suka ce, “Lallai, wannan Ɗan Allah ne!”

55 Akwai kuma waɗansu mata da yawa da suka bi Yesu tun daga Galili suna yi masa hidima. Suka tsaya daga nesa suna kallon abin da yake faruwa.

56 Cikinsu akwai Maryamu daga Magadala, da Maryamu mamar Yakub da Yusuf, da kuma mamar ˈyaˈyan Zabadi.

57 Da yamma ta yi, sai wani mai arziki, mutumin Arimatiya, mai suna Yusuf ya zo, shi ma almajirin Yesu ne.

58 Ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi gawar Yesu. Bilatus kuwa ya ba da umarni a ba shi.

59 Sai Yusuf ya ɗauki gawar Yesu ya naɗe a zanen lilin mai tsabta.

60 Ya sa shi a cikin sabon kabari nasa, wanda ya haƙa a jikin dutse. Sai ya tura babban dutse a baƙin kabarin, ya tafi.

61 Maryamu daga Magadala, da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.

62 Washegari, wato bayan Ranar Shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,

63 suka ce, “Ranka yă daɗe! Mun tuna da abin da mai ruɗin mutanen nan ya ce tun yana da rai, wai bayan kwana uku zai tashi daga matattu.

64 Saboda haka ka sa a yi gadin kabarin nan sosai har zuwa rana ta uku, domin kada almajiransa su tafi su saci gawarsa, saˈan nan su ce wa mutane ya tashi daga matattu. Ruɗin ƙarshe fa zai fi na farkon muni.”

65 Bilatus ya ce musu, “Ku ɗebi sojoji, ku je ku yi gadin shi duk yadda za ku iya.”

66 Sai suka je suka tsare kabarin, suka buga hatimin sarki a dutsen kabarin, suka kuma sa sojoji su yi gadin wurin.

Open Bible reader