Hausa Bible
Matiyu 25
1 “Saˈan nan za a kwatanta mulkin sama da ˈyan mata goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka tafi su karɓi ango.
2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima ne.
3 Lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu ba su riƙe mai domin ƙari ba.
4 Masu hikimar nan kuwa sun riƙe kwalaba masu mai tare da fitilunsu.
5 Angon kuwa bai zo da wuri ba, sai dukansu suka yi ta jin barci har barci ya kwashe su.
6 “Can da dare sosai, sai aka ji kira ana cewa, ‘Ga ango! Ku fito ku karɓe shi.’
7 Sai ˈyan matan nan goma suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.
8 Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar nan, ‘Ku ɗan ba mu manku kaɗan mana. Fitilunmu suna mutuwa.’
9 Amma masu hikimar suka ce musu, ‘Aˈa, ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo naku.’
10 Da suka tafi domin su sayo man, kafin su dawo sai angon ya iso. Waɗanda suke a shirye kuwa suka shiga wurin biki da shi, aka kuma rufe ƙofa.
11 “Daga baya sai sauran ˈyan matan suka zo, suka ce, ‘Maigirma, Maigirma, ka buɗe mana!’
12 Amma angon ya amsa musu ya ce, ‘Hakika ina gaya muku, ban san ku ba.’
13 “Domin haka sai ku zauna da shiri, gama ba ku san ranar, ko a ƙarfe nawa ne ba.”
14 “Mulkin Allah zai zama kamar mutum ne wanda zai yi tafiya, sai ya kira bayinsa, ya danƙa dukiyarsa a hannunsu.
15 Ya ba ɗaya zinariya dubu biyar, ɗaya kuma zinariya dubu biyu, ya ba wani kuma zinariya dubu ɗaya, kowa daidai da ƙarfinsa. Saˈan nan ya tafi.
16 Wanda ya karɓi zinariya dubu biyar ɗin nan, nan da nan ya je ya yi kasuwanci da kuɗin, har ya yi ribar dubu biyar.
17 Haka ma wanda ya karɓi zinariya dubu biyu ɗin nan, ya yi ribar dubu biyu.
18 Amma wanda ya karɓi zinariya dubu ɗin nan ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin maigidansa.
19 “Da aka daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo domin yă daidaita lissafin abin da suka yi da kuɗin.
20 Sai wanda ya karɓi zinariya dubu biyar ɗin ya zo gaba ya kawo waɗansu zinariya dubu biyar ya ce, ‘Maigida, ka ba ni zinariya dubu biyar. Ga shi kuma na yi ribar dubu biyar.’
21 Sai maigidansa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci! Ka yi aminci a kan ƙaramin abu. Zan ba ka aikin da ya fi wannan. Ka zo ka yi murna tare da ni.’
22 “Sai wanda ya karɓi zinariya dubu biyun nan kuma ya zo gaba, ya ce, ‘Maigida, ka ba ni zinariya dubu biyu. Ga shi kuma na yi ribar dubu biyu.’
23 Sai maigidansa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan ƙaramin abu. Zan ba ka aikin da ya fi wannan. Ka zo ka yi murna tare da ni.’
24 “Saˈan nan wanda ya karɓi zinariya dubu ɗaya shi ma ya zo gaba ya ce, ‘Maigida, na san kai kana da wuyar shaˈani, kana girbi a inda ba ka yi shuka ba. Kai kuma mai son na banza ne.
25 Shi ya sa na ji tsoro na je na tona rami na ɓoye zinariyarka. Karɓi abinka.’
26 “Sai maigidansa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa mai ƙyuya! Ashe, ka sani ina girbi inda ban shuka ba, nakan kuma tattara daga inda ban baza iri ba.
27 Ai, da ka sa mini kuɗina a banki, saˈad da na dawo kuma in karɓi abina har da riba!
28 Domin haka sai ku karɓi zinariya dubu ɗayan nan daga wurinsa ku ba mai dubu goman nan.
29 Gama duk wanda yake da abu, za a ƙara masa, har yă samu da yawa. Wanda ba shi da abu kuwa, ko ɗan kaɗan ɗin da yake da shi ma, za a karɓa daga gare shi.
30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon haƙora.’ ”
31 “Lokacin da Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakarsa tare da malaˈiku duka, saˈan nan ne zai zauna a maɗaukakin kujerar mulkinsa.
32 Za a tara duk mutanen duniya a gabansa, zai rarraba su dabam-dabam, kamar yadda makiyayi yake raba tumaki da awaki.
33 Zai sa tumaki a hannun damansa, awaki kuwa a hagunsa.
34 Saˈan nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi muku albarka! Ku karɓi mulkin da Allah ya shirya muku tun farkon duniya.
35 Gama saˈad da nake jin yunwa kun ba ni abinci. Da nake jin ƙishin ruwa, kun ba ni ruwa na sha. Ina baƙo, kuka karɓe ni.
36 Ba ni da riga, kuka ba ni riga. Ba ni da lafiya, kuka lura da ni. Ina kurkuku, kuka ziyarce ni.’
37 “Saˈan nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ubangiji, yaushe ne muka gan ka kana jin yunwa muka ba ka abinci? Ko kuwa kana jin ƙishin ruwa muka ba ka ruwa ka sha?
38 Kuma yaushe ne muka gan ka baƙo muka karɓe ka? Ko kuwa ba ka da riga muka ba ka riga?
39 Kuma yaushe ne muka ga ba ka da lafiya ko kana kurkuku muka ziyarce ka?’
40 Sarkin zai amsa musu yă ce, ‘Hakika ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ˈyanˈuwana mafi ƙanƙanta, ai, kun yi mini ke nan.’
41 “Saˈan nan zai ce wa na hagunsa, ‘Ku rabu da ni, ku laˈanannu, ku shiga wutar da ba za ta taɓa mutuwa ba har abada, wadda aka shirya wa Shaiɗan da malaˈikunsa.
42 Gama saˈad da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Ina jin ƙishin ruwa, ba ku ba ni ruwa na sha ba.
43 Ina baƙo, ba ku karɓe ni ba. Ba ni da riga, ba ku ba ni riga ba. Na yi rashin lafiya, kuma ina kurkuku ba ku ziyarce ni ba.’
44 “Saˈan nan su ma za su amsa su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka kana jin yunwa, ko ƙishin ruwa, ko kana baƙunci, ko ba ka da riga, ko kana rashin lafiya, ko kana kurkuku, ba mu kula da kai ba?’
45 Saˈan nan zai amsa musu yă ce, ‘Hakika ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ba ku yi mini ba ke nan.’
46 Waɗannan za su shiga azaba marar ƙārewa, masu adalci kuwa su shiga rai na har abada.”