Hausa Bible
Markus 11
1 Da suka zo kusa da Urushalima, wato a Betafaji da Betani, wajen Tudun Itatuwan Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,
2 ya ce musu, “Ku je ƙauyen can na gabanku. Da shigarku za ku ga wani ɗan jaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kunce shi ku kawo.
3 Idan wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke haka?’ Sai ku ce masa, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma mai da shi nan da nan.’ ”
4 Sai suka tafi, suka ga ɗan jakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya. Suna kuncewa ke nan,
5 sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce musu, “Yaya? Don me kuke kunce jakin nan?”
6 Suka ba da amsa daidai yadda Yesu ya faɗa musu, sai mutanen suka bar su su tafi da jakin.
7 Da suka kawo wa Yesu jakin, suka shimfiɗa masa rigunansu, sai Yesu ya hau ya zauna.
8 Sai mutane da yawa suka shimfiɗa rigunansu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sare daga gonaki.
9 Waɗanda suke gabansa da waɗanda suke bayansa suka yi ta ihu suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa a cikin sunan Ubangiji!
10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na babanmu Dawuda. Hosanna ga Mafi Ɗaukaka!”
11 Da Yesu ya shiga Urushalima, ya tafi Haikali ya shiga ya dudduba dukan kome. Da yake rana ta fāɗi ko, sai ya fita ya koma Betani tare da almajiransa.
12 Washegari da suka tashi daga Betani, sai Yesu ya ji yunwa.
13 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je yă ga ko zai sami ˈyaˈya. Amma da ya kai wurin, bai ga kome ba sai ganye kawai, don ba lokacin ˈyaˈyan ɓaure ba ne.
14 Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa yă ƙara cin ˈyaˈyanka har abada!” Almajiransa kuwa suka ji abin da ya faɗa.
15 Da shigarsu Urushalima, Yesu ya shiga Haikali ya fara korar masu saya da sayarwa daga ciki. Ya kuma tutture teburan masu canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabaru.
16 Ya kuma hana kowa yă ɗauki wani abu yă wuce ta filin Haikalin.
17 Sai ya koya wa mutane ya ce, “A rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, “ ‘Za a ce da Gidana Gidan adduˈa na dukan alˈummai.’ Ga shi kun mai da shi ‘wurin ɓuyan ˈyan fashi.’ ”
18 Manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka ji wannan magana, suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, domin dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19 Da yamma kuwa, Yesu da almajiransa suka fita daga cikin birnin.
20 Da safe suna wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya bushe tun daga saiwarsa.
21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Malam, duba! Ɓauren nan da ka laˈanta ya bushe!”
22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah!
23 Hakika ina gaya muku, idan mutum ya gaskata da Allah, zai iya faɗa wa babban tudun nan yă tashi yă jefa kansa cikin teku. In bai yi shakka a zuciyarsa a kan abin da ya faɗa ba, za a yi masa.
24 Domin haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da adduˈa, ku gaskata cewa kun riga kun samu, zai kuwa zama naku.
25 Kuma a kowane lokacin da kuke tsayawa kuna adduˈa, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku wanda yake cikin sama shi ma yă yafe muku laifofinku.
26 Amma in ba ku yafe ba, haka Ubanku wanda yake cikin sama ma ba zai yafe muku laifofinku ba.”
27 Suka sāke shiga Urushalima. Yesu yana zagawa ke nan cikin Haikalin, sai manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa da shugabannin jamaˈa suka zo wurinsa.
28 Suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka iznin yin wannan?”
29 Yesu ya amsa ya ce, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.
30 Ku faɗa mini, iznin da Yohanna ya yi baftisma da shi, Allah ne ya ba shi, ko kuwa mutum?”
31 Sai suka fara gardama a tsakaninsu, suka ce, “Idan muka ce, ‘Daga wurin Allah ne,’ zai ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
32 Amma za mu iya cewa daga wurin mutum ne kuwa?” Suna jin tsoron abin da mutane za su yi musu, domin dukan mutane sun ɗauka cewa Yohanna annabi ne.
33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Ni ma, ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”