Hausa Bible
Luka 22
1 To, lokacin Bikin Burodi Marar Yistin da ake ce da shi “Bikin Ƙetarewa” ya yi kusa.
2 Sai manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka yi ta neman yadda za su kashe Yesu. Sun nema su yi haka a ɓoye gama suna jin tsoron mutane.
3 Sai Shaiɗan ya shiga cikin zuciyar Yahuda wanda ake ce da shi Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajirai sha biyun nan.
4 Sai ya je ya yi magana da manyan firistoci da shugabannin masu gadin Haikali a kan yadda zai ba da Yesu gare su.
5 Suka yi murna sosai, suka shirya a kan za su biya shi kuɗi.
6 Yahuda kuwa ya yarda da haka, ya fara neman hanyar da zai ba da Yesu gare su ba da sanin mutane ba.
7 Da ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato ranar da za a yanka ɗan rago na Bikin Ƙetarewa,
8 Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna ya ce musu, “Ku je ku shirya mana abincin Ƙetarewa mu ci.”
9 Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya shi?”
10 Ya ce musu, “Da kun shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum riƙe da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.
11 Ku ce wa maigidan, ‘Malam ne ya aike mu mu ce maka, “Ina ɗakin da ni da almajiraina za mu ci abincin Ƙetarewa?” ’
12 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. A nan za ku shirya mana kome.”
13 Sai suka tafi, suka kuma sami kome daidai kamar yadda Yesu ya faɗa musu, suka kuma shirya abincin Bikin Ƙetarewa.
14 Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.
15 Sai ya ce musu, “Na yi marmari in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku kafin in sha wahala!
16 Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cin bikin nan ba, sai maˈanarsa ta cika a mulkin Allah.”
17 Sai ya ɗauki kwaf, ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ku karɓa ku rarraba tsakaninku.
18 Ina gaya muku cewa, daga yanzu ba zan ƙara shan wannan ruwan inabi ba sai mulkin Allah ya zo.”
19 Sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya shi, ya kuma ba su, yana cewa, “Wannan jikina ne wanda za a bayar dominku. Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”
20 Haka kuma, bayan jibin, ya ɗauki kwaf, ya ce, “Wannan kwaf na sabuwar yarjejeniya ce wadda aka tabbatar da jinina wanda za a zubar dominku.
21 Amma ga wanda zai bashe ni yana ci tare da ni!
22 Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka shirya, amma kaiton mutumin da ya ba da shi!”
23 Sai almajiran suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.
24 Sai gardama ta tashi a cikin almajiran a kan wane ne a cikinsu zai zama babba.
25 Yesu ya ce musu, “Sarakunan mutanen da ba su san Allah ba sukan nuna wa mutanensu iko, kuma shugabanninsu sukan ce da kansu ‘masu taimakon mutane.’
26 Amma kada yă zama haka a tsakaninku. A maimakon haka, bari babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuma yă zama kamar bawa.
27 Wane ne ya fi girma, shi wanda ya zauna yana ci ne, ko kuma shi da yake kai masu abinci? Ai, wanda ya zauna yana ci ne. Amma ga shi ina a cikinku kamar mai kai abinci ne.
28 “Ku ne kuka tsaya da aminci tare da ni a duk gwaje-gwajen da na sha.
29 Kamar dai yadda Ubana ya ba ni iko in yi mulki, haka nake ba ku,
30 domin ku ci ku sha a teburina, a can cikin mulkina. Kuma za ku zauna a kujerun mulki, ku yi mulkin zuriya goma sha biyun nan na Israˈila.
31 “Bitrus, Bitrus! Ka ji nan! Shaiɗan ya nemi izni yă gwada ku duka, yă tankaɗe ku kamar yadda ake tankaɗe alkama daga dusa.
32 Amma na yi maka adduˈa, Bitrus, kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan da ka juyo wurina, ka ƙarfafa ˈyanˈuwanka.”
33 Bitrus ya amsa, ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in je har ma kurkuku tare da kai. In ma mutuwa ce, mu mutu tare!”
34 Yesu ya ce, “Ina gaya maka, Bitrus, kafin zakara yă yi cara a daren yau, za ka ce ba ka san ni ba sau uku!”
35 Sai Yesu ya tambayi almajiransa ya ce, “A lokacin da na aike ku ba kuɗi, ba abinci, ba takalma, kun rasa wani abu ne?” Suka ce, “Aˈa!”
36 Ya ce musu, “Amma yanzu, duk wanda yake da kuɗi, ko abinci, yă ɗauka yă riƙe, kuma duk wanda ba shi da takobi, yă sayar da rigarsa yă saya.
37 Gama ina gaya muku, cewa wannan Rubutacciyar Maganar Allah da ta ce, ‘An haɗa shi cikin masu zunubi,’ dole ne ta cika a kaina. I, abin da aka rubuta a kaina yana kan cikawa.”
38 Almajiran suka ce masa, “Maigirma, ga takobi guda biyu a nan.” Yesu ya ce, “Ya isa.”
39 Yesu ya bar birnin, ya hau Tudun Itatuwan Zaitun kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.
40 Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi adduˈa fa, domin kada ku fāɗa cikin jarraba.”
41 Sai ya ci gaba ya yi ɗan nisa da su, misalin nisan jifa, sai ya durƙusa ya yi adduˈa.
42 Ya ce, “Uba, in ka yarda ka ɗauke mini wannan kwaf na wahala. Amma ba nufina ba, sai dai nufinka za a bi.”
43 Sai ga malaˈika daga sama ya bayyana gare shi yana ƙarfafa shi.
44 Yana cikin azaba mai tsanani, sai ya ƙara nacewa cikin adduˈar, har zufa tana sauka masa kamar jini.
45 Da Yesu ya tashi daga adduˈa, sai ya koma wurin da almajiran suke, ya same su suna barci saboda baƙin ciki.
46 Ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi adduˈa domin kada ku fāɗa cikin jarraba.”
47 Bai ma rufe baki ba, sai ga taron mutane suka zo. Yahuda, ɗaya daga cikin sha biyun ne, ya kawo su. Sai ya gusa kusa da Yesu domin yă sumbace shi.
48 Amma Yesu ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba ne za ka ba da Ɗan Mutum?”
49 Da almajiran da suke tare da Yesu suka ga haka, suka tambaye shi, suka ce, “Maigirma, mu yi amfani da takobin ne?”
50 Sai ɗayansu ya sari bawan babban firist, ya yanke kunnensa na dama.
51 Amma Yesu ya ce musu, “Ku bari.” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.
52 Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci da shugabannin masu gadin Haikali da shugabannin jamaˈa, waɗanda suka zo domin su kama shi, “Kun fito da takuba, da sanduna ku kama ni sai ka ce ɗan fashi?
53 Kullum ina tare da ku a Haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan ne lokacinku da na ikon duhu.”
54 Suka kama Yesu suka tafi da shi, suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya dinga binsu daga nesa-nesa.
55 Da suka hura wuta a filin gidan suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.
56 Da ɗaya daga cikin ˈyan matan da suke aiki a gidan ta gan shi zaune kusa da wutar, ta kafa masa ido ta ce, “Ai, wannan mutumin ma yana tare da Yesu!”
57 Amma Bitrus ya yi musū ya ce, “Ke! Ni ban san shi ba!”
58 Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani mutum ya gane Bitrus, ya ce, “Lallai, kai ma ɗayansu ne!” Amma Bitrus ya nace da cewa, “Kai! Ba ni ba ne!”
59 Bayan kamar awa ɗaya sai wani mutum ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma yana tare da shi, gama shi mutumin Galili ne.”
60 Amma Bitrus ya ce, “Haba! Ban ma san abin da kake faɗa ba!” Tun bai rufe baki ba, sai zakara ya yi cara.
61 Ubangiji kuma ya juya ya dubi Bitrus. Saˈan nan Bitrus ya tuna yadda Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara yă yi cara a daren yau, za ka ce ba ka san ni ba sau uku.”
62 Sai ya fita waje, ya fashe da kuka mai zafi.
63 Sai waɗanda suke gadin Yesu suka yi masa baˈa suka kuma yi masa dūka.
64 Suka ɗaure masa idanu suna tambayarsa, “Yi annabci, wa ya mare ka!”
65 Suka kuma yi ta yi masa waɗansu maganganun reni.
66 Da gari ya waye, sai shugabannin jamaˈa da manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka taru, suka kai Yesu gaban majalisarsu.
67 Suka ce, “Faɗa mana, kai ne Almasihu?” Sai ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku ba za ku gaskata ba,
68 idan kuma na yi muku tambaya ba za ku ba ni amsa ba.
69 Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”
70 Sai dukansu suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Ya amsa ya ce, “Kun faɗa, Ni ne.”
71 Sai suka ce, “Wace shaida ce kuma muke nema? Ai, mu da kanmu mun ji abin da ya ce da bakinsa!”