Hausa Bible
Luka 2
1 A kwanakin nan, Kaisar Augustus ya ba da umarni a ƙirga dukan mutanen da suke a ƙarƙashin mulkin Roma.
2 Wannan shi ne ƙirga ta farko wadda aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin ƙasar Suriya.
3 Dukan mutane suka koma garuruwansu domin a ƙirga su.
4 Yusuf ma ya bar garin Nazaret a cikin Galili ya je garin Betelehem a cikin yankin Yahudiya, wato garin da aka haifi Sarki Dawuda ke nan. Yusuf ya je can domin shi daga dangin Dawuda ne.
5 Ya tafi tare da Maryamu da aka yi alkawari zai aura, domin a ƙirga su tare. Lokacin nan kuwa tana da ciki.
6 Da suna can Betelehem, sai kwanakin haifuwarta suka yi.
7 Ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki, domin ba su sami ɗaki a masauki ba.
8 A wannan gefen ƙasar kuwa, akwai waɗansu makiyaya suna kwana a fili, suna lura da dabbobinsu da dare.
9 Ba labari sai ga malaˈikan Ubangiji ya bayyana gare su, kuma ɗaukakar Allah ta haskaka su. Sai suka ji tsoro sosai.
10 Amma malaˈikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro! Gama na zo muku da labari mai daɗi, wanda zai sa dukan mutane su yi farin ciki sosai.
11 A yau ɗin nan, a cikin garin Dawuda, an haifa muku Mai Ceto, Almasihu Ubangiji!
12 Wannan ne zai zama muku alama, za ku samu an naɗe jariri da zane, an kuma kwantar da shi a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki.”
13 Ba labari sai ga ƙungiyar malaˈiku daga sama sun bayyana tare da malaˈika na farin, suna yabon Allah suna cewa,
14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama! A duniya bari salama ta kasance tare da waɗanda Allah yake jin daɗinsu!”
15 Da malaˈikun suka rabu da su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa junansu, “Bari mu je Betelehem mu ga abin nan da ya faru, da Ubangiji ya gaya mana.”
16 Sai suka tafi da sauri, suka ga Maryamu da Yusuf, suka kuma ga yaron yana kwance a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki.
17 Da makiyayan suka gan shi sai suka ba da labarin abin da malaˈikan ya faɗa musu a kan yaron.
18 Dukan mutanen da suka ji wannan labari, sai suka yi ta riƙe baki suna mamakin abin da makiyayan nan suka ce.
19 Maryamu kuwa ta riƙe dukan waɗannan abubuwa, tana tunaninsu a zuciyarta.
20 Makiyayan kuma suka koma, suna ta yin waƙoƙin yabon Allah, saboda dukan abin da suka ji, suka kuma gani. Kome ya faru kuwa kamar dai yadda malaˈikan ya faɗa musu.
21 Da yaron ya yi kwana takwas, sai aka yi masa kaciya, aka kuma ba shi suna Yesu, sunan da malaˈika ya bayar tun kafin a yi cikinsa.
22 Da lokaci ya kai da Maryamu da Yusuf za su yi abin da Koyarwar Musa ta ce a yi don tsabtacewa, sai suka ɗauki Yesu zuwa Urushalima domin su miƙa shi ga Ubangiji.
23 Haka yake a rubuce a Koyarwar Ubangiji, “Duk ɗa na fari wanda aka haifa, za a keɓe shi da tsarki ga Ubangiji.”
24 Suka kuma yi hadaya kamar yadda Koyarwar Ubangiji ta faɗa cewa, “Kurciyoyi biyu ko ˈyan tattabaru biyu ne za a yanka.”
25 To, a wannan lokaci akwai wani mutumin da yake zama a Urushalima, da ake ce da shi Simeyon. Shi mutum mai adalci ne, mai bautar Allah, kuma yana jiran ranar da za a ceci Israˈila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26 Ruhu Mai Tsarki ya faɗa masa cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun da Ubangiji ya yi alkawari zai aiko.
27 Da Ruhu yana iza shi sai ya shiga Haikalin a lokacin da iyayen suka kawo Yesu Haikali domin su yi kamar yadda Koyarwar Musa ta ce a yi,
28 sai Simeyon ya karɓi yaron a hannunsa ya yi wa Allah godiya ya ce,
29 “Yanzu, ya Ubangiji, ka sallami bawanka lafiya, kamar yadda ka yi alkawari,
30 gama idanuna sun ga cetonka,
31 ceton da ka shirya a gaban dukan mutane,
32 hasken da zai bayyana ka ga waɗanda ba Yahudawa ba, yă kuma kawo ɗaukaka ga mutanenka Israˈila.”
33 Baban yaron da mamarsa suka riƙe baki, suna mamakin abubuwan nan da Simeyon ya faɗa a kansa.
34 Simeyon ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu, mamar yaron, “Allah ya zaɓi yaron nan domin yă zama dalilin fāɗuwar waɗansu, da tashin waɗansu da yawa a cikin Israˈila. Zai zama alama daga wurin Allah wadda mutane da yawa ba za su so ba.
35 Ta haka asirin zukatansu zai tonu. Abin nan kuwa zai yi miki zafi kamar takobi ne ya soki zuciyarki.”
36 Akwai wata tsohuwar annabiya mai suna Hannatu, ˈyar Fanuwel na zuriyar Asher. Ta yi zaman aure na shekara bakwai ne kawai,
37 sai mijinta ya mutu. Yanzu shekarunta tamanin da huɗu ne. Ba ta barin Haikali, tana yi wa Allah sujada dare da rana a wurin, tana adduˈa da azumi.
38 Daidai wannan lokaci, sai ta shigo, tana yi wa Allah godiya, ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke jiran Allah yă ba Urushalima ˈyanci.
39 Da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Koyarwar Ubangiji ta ce a yi, sai suka koma garinsu Nazaret a Galili.
40 Yaron ya yi girma, ya kuma yi ƙarfi, yana cike da hikima. Alherin Allah kuma yana tare da shi.
41 Kowace shekara iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.
42 Da Yesu ya cika shekara goma sha biyu da haifuwa, sai suka je bikin kamar yadda suka saba.
43 Da bikin ya ƙāre, suka kama hanya domin su koma gida, amma Yesu, ɗan yaron nan, ya tsaya a baya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.
44 Su kuma suna tsammani yana cikin jamaˈa, saboda haka suka yi ta tafiya har yini guda. Saˈan nan suka fara nemansa cikin ˈyanˈuwansu da kuma abokansu,
45 amma ba su gan shi ba. Saboda haka suka koma Urushalima domin su neme shi a can.
46 A rana ta uku suka same shi yana zama a cikin Haikali tare da malamai. Yana jinsu, yana kuma yi musu tambayoyi.
47 Dukan waɗanda suka ji shi, suka riƙe baki, suna mamakin ganewarsa da yadda yake ba da amsoshi.
48 Iyayensa kuma suka yi mamakin ganinsa a nan. Sai mamarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da babanka mun damu sosai da ba mu gan ka ba.”
49 Ya amsa musu ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku sani cewa ya kamata in kasance a gidan Ubana ba?”
50 Amma ba su gane ko mene ne yake nufi da maganarsa nan ba.
51 Sai ya tashi ya bi su, suka koma Nazaret tare, inda ya dinga biyayya ga iyayensa. Mamarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa tana tunaninsu a zuciyarta.
52 Yesu ya yi ta ƙaruwa da hikima da tsayi, ya kuma sami farin jini a gaban Allah da kuma a gaban mutane.