Skip to content

Hausa Bible

Luka 1

1 Mutane da yawa sun yi ƙoƙari su rubuta labarin abubuwan da suka faru a tsakaninmu.

2 Sun rubuta abin nan da muka ji daga bakin waɗanda suka ga waɗannan abubuwa da idanunsu tun farko, suka kuma yi shelar kalmar Allah.

3 Saboda haka, maigirma Tiyofilus, da yake na bincika abubuwan nan duka a hankali tun daga farkonsu, na ga ya yi kyau in rubuta maka su bi da bi,

4 domin ka san gaskiyar abubuwan nan kamar yadda aka koyar maka su.

5 A lokacin da Hirudus yake mulkin yankin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar firistoci na gidan Abiya. Sunan uwargidansa kuma Alisabatu, ita kuma ta fito daga zuriyar gidan Haruna ne.

6 Dukansu biyu, sun yi zaman adalci a gaban Allah, sun kuma bi umarnai da ƙaˈidodin Ubangiji duka kamar yadda ya ce a yi.

7 Amma ba su da ˈyaˈya domin Alisabatu ba ta haifuwa, kuma Zakariya da ita duk sun tsufa.

8 Wata rana, Zakariya yana aikinsa na firist a cikin Haikali, bisa ga tsarin da aka yi na ƙungiya domin hidima ta kowace rana.

9 Bisa ga alˈada wadda aka kafa don firistoci su bi, aka zaɓe shi ta wurin jefa ƙuriˈa domin yă shiga cikin Haikalin Ubangiji yă ƙona turare mai ƙanshi. Saboda haka sai ya shiga Haikalin,

10 mutane kuma suna waje, suna adduˈa a lokacin da yake ƙona turare mai ƙanshi.

11 Ba labari, sai ga malaˈikan Ubangiji ya bayyana masa, ya tsaya a gefen dama na bagade, inda ake ƙona turare.

12 Da ganin malaˈikan, sai gaban Zakariya ya fāɗi, tsoro kuma ya kama shi.

13 Amma malaˈikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya! Allah ya karɓi adduˈarka, kuma uwargidanka Alisabatu za ta haifa maka ɗa. Za ka sa masa suna Yohanna.

14 Za ka yi farin ciki da murna sosai, mutane da yawa kuma za su yi farin ciki.

15 Yaron nan zai zama babban mutum a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa buguwa ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki tun kafin a haife shi.

16 Shi ne zai dawo da mutanen Israˈila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.

17 Zai wuce gaban Ubangiji, yă kuma yi aikinsa da dukan ƙarfinsa da kuma ƙarfin zuciya kamar annabi Iliya. Zai kawo zaman lafiya tsakanin iyaye da ˈyaˈyansu. Zai juyo da mutane masu rashin biyayya su zama mutane masu adalci, ta haka zai shirya wa Ubangiji mutanensa.”

18 Sai Zakariya ya ce wa malaˈikan, “Yaya zan san cewa abin nan da ka faɗa haka zai kasance? Ga ni na tsufa, uwargidana kuma tana shekaru masu yawa.”

19 Malaˈikan ya ce, “Ni ne Gabriyel da yake tsaya a gaban Allah. Allah ya aiko ni in zo in faɗa maka wannan labari mai daɗi.

20 Amma ga shi ka ƙi ka yarda da saƙo wanda za a cika shi a lokacinsa. Saboda haka, tun da ka ƙi ka yarda, ba za ka ƙara iya yin magana ba, sai ranar da alkawarin nan ya cika.”

21 Mutane sun zauna suna jiran fitowar Zakariya, suna ta tunani ko mene ne ya sa ya daɗe haka a cikin Haikalin.

22 Da ya fito bai iya yin magana da baki ba, sai sun gane cewa ya ga ruˈuya a cikin Haikalin. Sai ya dinga yi musu magana da hannu, amma bai iya yin magana da bakinsa ba.

23 Da lokacin hidimarsa ya ƙāre, sai ya koma gida.

24 Bayan ˈyan kwanaki, sai uwargidansa Alisabatu ta yi ciki, sai ta ɓoye kanta har wata biyar.

25 Alisabatu ta ce, “A ƙarshe Ubangiji ya ji tausayina, ya cire mini kunya a cikin jamaˈa.”

26 Alisabatu tana cikin wata shida ke nan da samun ciki, sai Allah ya aiki malaˈika Gabriyel zuwa wani gari a cikin Galili, da ake ce da shi Nazaret.

27 Ya aike shi yă kai saƙo wurin wata yarinyar da aka yi alkawari za ta auri wani mutum mai suna Yusuf, daga zuriyar Sarki Dawuda. Sunan yarinyar kuwa Maryamu ne.

28 Da malaˈikan ya zo wurinta sai ya ce, “A gaishe ki! Ubangiji yana tare da ke, ke da kike mai samun alheri!”

29 Da Maryamu ta ji gaisuwar nan, sai ta damu ƙwarai, tana tunani ko wacce irin gaisuwa ce haka.

30 Sai malaˈikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu. Gama kin sami alheri a gaban Allah.

31 “Ga shi za ki yi ciki, za ki kuma haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu.

32 Zai zama babban mutum, kuma za a ce da shi Ɗan Mafi Ɗaukaka. Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dawuda.

33 Zai yi mulkin gidan Yakub har abada, mulkinsa kuma ba zai ƙāre ba!”

34 Maryamu ta ce wa malaˈikan, “Yaya wannan zai faru, tun da yake ban taɓa sanin namiji ba?”

35 Malaˈikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko a kanki, ikon Mafi Ɗaukaka kuma zai rufe ki. Saboda haka yaron nan da za a haifa, za a ce da shi mai tsarki, Ɗan Allah.

36 “Ga shi Alisabatu ˈyarˈuwarki, wadda ake cewa ba za ta haifu ba, yanzu ɗin nan, tana da ciki wata shida, duk da tsufarta.

37 Ai, ba abin da zai gagari Allah yi.”

38 Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai malaˈikan ya tafi.

39 A kwanakin nan Maryamu ta yi shiri ta tafi da sauri zuwa wani gari cikin tuddan yankin Yahudiya.

40 Ta shiga gidan Zakariya, ta gai da Alisabatu.

41 Da jin gaisuwar, sai Alisabatu ta ji yaron da yake cikinta ya yi motsi. Aka kuma cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki.

42 Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, yaron nan na cikinki kuma mai albarka ne!

43 Yaya wannan alheri ya zo kaina, har da mamar Ubangijina za ta zo wurina?

44 Ga shi, da na ji gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi sosai saboda murna.

45 Mai albarka ce ke da kika gaskata cewa saƙon nan da Ubangiji ya aika miki zai zama gaskiya!”

46 Maryamu ta ce, “Zuciyata tana yabon Ubangiji.

47 Raina yana murna saboda Allah mai cetona,

48 domin ya tuna da ni, ko da yake ni baiwarsa ce wadda ba kome ba! Daga yanzu dukan mutane za su ce da ni mai albarka,

49 gama Allah Mai Iko ya yi mini manyan abubuwa. Sunansa mai tsarki ne!

50 Daga tsara zuwa tsara yana jin tausayin waɗanda suke tsoronsa.

51 Da hannunsa mai ƙarfi ya aikata manyan abubuwa! Ya watsar da masu ɗaga kai da dukan abin da suke taƙama da shi a zuciyarsu.

52 Ya sauƙar da sarakuna daga mulkinsu, ya ɗaukaka waɗanda ba kome ba.

53 Ya ba masu yunwa abubuwa masu kyau, ya sallami masu arziki hannu wofi.

54 Ya taimaki bawansa Israˈila gama ya tuna yă nuna jinƙai ga mutanensa,

55 bisa ga alkawarinsa ga kakanninmu, ga Ibrahim da zuriyarsa har abada!”

56 Maryamu ta zauna da Alisabatu kamar wata uku, saˈan nan ta koma gida.

57 Da kwanakin haifuwarta suka cika, sai Alisabatu ta haifi ɗa.

58 Maƙwabtanta da ˈyanˈuwanta suka yi murna sosai da suka ji ta haifu, suka taya ta farin ciki saboda wannan albarkar da Ubangiji ya yi mata.

59 Da yaron ya cika kwana takwas, sai suka zo domin su yi masa kaciya. Dā ma sun so ne su sa masa sunan babansa, Zakariya,

60 amma mamar yaron ta ce, “Aˈa! Za a ce da shi Yohanna.”

61 Sai suka ce, “Wane ne a danginku mai wannan suna?”

62 Sai suka tambayi baban yaron da hannu yă faɗa sunan da za a kira yaron da shi.

63 Sai ya sa a kawo masa allo, sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna ne.” Sai dukan mutanen da suke wurin suka yi mamaki!

64 Nan take Zakariya ya sami bakin magana kuma, ya fara yabon Allah.

65 Tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Mutane suka ba da labarin abin nan da ya faru a koˈina a yankin tuddan Yahudiya.

66 Duka wanda ya ji wannan labarin, sai yă yi ta tunani, yana cewa, “Me yaron nan zai zama?” Domin an gane cewa hannun Ubangiji yana tare da shi.

67 Ana nan sai Ruhu Mai Tsarki ya cika Zakariya, baban Yohanna, sai ya yi annabci cewa,

68 “Albarka ta tabbata ga Ubangiji, Allah na Israˈila! Ya zo yă taimaki mutanensa, yă kuma fanshe su.

69 Ya tā da Mai Ceto mai iko dominmu daga gidan bawansa Dawuda,

70 kamar yadda ya yi alkawari tun tuni ta bakin annabawansa masu tsarki cewa,

71 zai cece mu daga hannun masu gāba da mu, da dukan waɗanda ba sa son ganinmu.

72 Ta haka ya nuna wa kakanninmu jinƙai, ta wurin tuna da yarjejeniyarsa mai tsarki,

73 rantsuwar da ya yi wa babanmu Ibrahim,

74 cewa zai cece mu daga hannun masu gāba da mu, domin mu bauta masa ba tsoro,

75 mu kasance da tsarki mu yi ayyuka masu adalci a gaban Allah dukan kwanakinmu.

76 “Kai kuma ɗan yaron nan, za a ce da kai annabi na Allah Mafi Ɗaukaka. Za ka riga Ubangiji zuwa, domin ka shirya masa hanya,

77 domin ka sanar wa mutanensa ceto ta wurin yafewar zunubansu.

78 Ta wurin yawan jinƙan nan na Allahnmu, hasken nan na ceto zai ɓullo daga sama yă haskaka mu,

79 yă haskaka masu zama a duhu, da masu zama a inuwar mutuwa, yă bi da mu a hanyar salama.”

80 Sai Yohanna ya yi girma, ya yi ƙarfi a cikin ruhaniya. Ya yi zamansa a daji sai lokacin da ya fito domin yin waˈazi ga mutanen Israˈila.

Open Bible reader