Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 9

1 Yesu yana wucewa ke nan, sai ya ga wani mutum wanda tun haifuwarsa makaho ne.

2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Malam, zunubin wane ne ya sa an haifi wannan mutum makaho? Zunubinsa ne, ko zunubin iyayensa?”

3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba wai saboda mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba ne, amma an haife shi makaho ne domin a nuna ikon aikin Allah a kansa.

4 Dole ne mu ci gaba da yin aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare yana nan zuwa, a lokacin da ba wanda zai iya aiki.

5 Muddin ina nan a duniya, ni ne hasken duniya.”

6 Da ya faɗa haka sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa ƙasa da shi, sai ya ɗebi ƙasar nan da ya kwaɓa, ya shafa a idanun mutumin.

7 Ya ce wa mutumin, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Tafkin Siluwam.” Wannan kalma kuwa tana nufin “Aika”. Sai mutumin ya je ya wanke ido, ya dawo idanunsa suna gani.

8 Maƙwabtansa da waɗanda suka saba ganinsa yana bara a dā, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”

9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “Aˈa, sun dai yi kama ne kawai.” Amma mutumin da kansa ya ce, “Ai, ni ne mutumin.”

10 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”

11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake ce da shi Yesu ne ya kwaɓa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka ka wanke ido a ruwan Siluwam.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”

12 Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Sai ya ce, “Ban sani ba.”

13 Sai mutanen suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.

14 To, a Ranar Hutu ta Mako ne Yesu ya kwaɓa ƙasa ya buɗe wa mutumin ido.

15 Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda aka yi ya sami gani. Sai mutumin ya ce, “Ya kwaɓa ƙasa ne ya shafa mini a idona, na wanke, yanzu ina gani.”

16 Waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga wurin Allah ya fito ba, don ba ya kiyaye Ranar Hutu ta Mako.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin alamun ban mamaki haka?” Sai raˈayinsu ya rabu.

17 Sai suka sāke tambayi mutumin suka ce, “Mene ne raˈayinka game da wannan mutum, tun da yake kai ne ya buɗe maka ido?” Mutumin ya amsa musu ya ce, “Ai, annabi ne shi.”

18 Shugabannin Yahudawan kam, ba su ba da gaskiya ba cewa mutumin nan makaho ne a dā, kuma yanzu yana gani. Saboda haka suka aika aka kira iyayensa.

19 Suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne? Kun ce an haife shi makaho? To, ta yaya ya iya gani yanzu?”

20 Sai iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, kuma an haife shi makaho ne.

21 Amma mu kam, ba mu san yadda aka yi yana gani yanzu ba, ba mu ma san wanda ya buɗe masa ido ba. Ku tambaye shi, ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22 Iyayensa sun faɗa haka ne domin tsoron shugabannin Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun shirya cewa duk wanda ya ce Yesu ne Almasihu, za a kore shi daga majamiˈa.

23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24 Sai Farisiyawan suka sāke kira mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka faɗa gaskiya don ka ɗaukaka Allah. Mu kam, mun san mutumin nan da ya warkar da kai mai zunubi ne.”

25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”

26 Suka tambaye shi kuma suka ce, “Me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?”

27 Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ni ba ne. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”

28 Sai suka zagi mutumin suka ce, “Kai ne dai almajirinsa, amma mu kam, almajiran Musa ne.

29 Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum kam ba mu san inda ya fito ba.”

30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe mini ido!

31 Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma yana sauraron duk wanda yake yi masa sujada, yana kuma yi masa biyayya.

32 Tun farkon duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.

33 Ai, da mutumin nan ba daga wurin Allah ya fito ba, da ba zai iya yin kome ba.”

34 Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haife ka cikin zunubi, kana ƙoƙari ka koya mana ne?” Sai suka kore shi.

35 Yesu ya ji labari cewa sun kori mutumin. Da ya same shi, sai ya tambaye shi ya ce, “Ka ba da gaskiya ga Ɗan Allah?”

36 Mutumin ya amsa ya ce, “Maigirma, wane ne shi? Ka faɗa mini don in ba da gaskiya gare shi.”

37 Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.”

38 Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na ba da gaskiya.” Ya kuma yi masa sujada.

39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyar nan ne domin in yi shariˈa, domin waɗanda ba sa gani su sami gani, waɗanda suke gani kuma su zama makafi.”

40 Da Farisiyawan da suke kusa da shi suka ji haka, sai suka ce masa, “Wato, kana cewa mu ma makafi ke nan?”

41 Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da alhakin zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, alhakin zunubanku yana nan daram.

Open Bible reader