Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 20

1 Tun da sassafe a rana ta farko, a lokacin da gari bai gama wayewa ba, Maryamu ˈyar garin Magadala ta je kabarin Yesu, ta ga an ture dutsen da ya rufe bakin kabarin.

2 Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “Ai, an ɗauki Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.”

3 Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka kama hanya zuwa kabarin.

4 Duka biyun kuwa suka ruga da gudu, amma almajirin nan ya wuce Bitrus, ya riga Bitrus kai wurin kabarin.

5 Da ya sunkuya ya leƙa sai ya ga yadin lilin a ajiye, amma bai shiga cikin kabarin ba.

6 Saˈan nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga cikin kabarin, ya ga yadin lilin a ajiye.

7 Ya kuma ga yadin da aka naɗe kewaye da kan Yesu ajiye a wani wuri dabam da yadin lilin.

8 Sai almajirin nan da ya riga Bitrus kai wurin kabarin shi ma ya shiga. Da ya gani sai ya ba da gaskiya.

9 Amma har yanzu dai ba su gane abin da Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa ba cewa dole ne Yesu yă sāke tashi daga matattu.

10 Sai almajiran suka koma gida.

11 Amma Maryamu ta tsaya a bakin kabarin daga waje, tana ta kuka. Tana cikin kuka ke nan, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin,

12 sai ta ga malaˈiku biyu da fararen tufafi suna zaune a inda gawar Yesu take a dā. Malaˈika ɗaya yana zaune ta wajen kai, ɗayan kuma ta wajen ƙafafu.

13 Sai malaˈikun suka tambaye ta suka ce, “Uwargida, me ya sa kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauki Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”

14 Da ta gama faɗin wannan magana sai ta juya ta ga Yesu a tsaye, amma ba ta gane cewa shi ne ba.

15 Sai Yesu ya tambaye ta ya ce, “Uwargida, me ya sa kike kuka? Wa kike nema?” Tana tsammani ko shi ne mai aiki a gonar, shi ya sa ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana don in ɗauke shi.”

16 Yesu ya kira ta ya ce, “Maryamu!” Sai ta juya zuwa wajen Yesu ta ce masa da yaren Yahudawa, “Rabboni!” wato Malam.

17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin ban hau wurin Uba ba tukuna. Amma ki tafi wurin ˈyanˈuwana ki ce musu zan koma wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”

18 Sai Maryamu ˈyar garin Magadala ta je ta ce wa almajiran, “Ai, na ga Ubangiji.” Ta kuma gaya musu abin da Yesu ya faɗa mata.

19 Da yamma ta yi a ranar farko ta mako, almajiran Yesu suna wuri ɗaya. Sun kuma kukkulle ƙofofi domin suna tsoron shugabannin Yahudawa. Sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama ta kasance tare da ku.”

20 Bayan da ya faɗa wannan magana, ya nuna musu hannuwansa da wajen haƙarƙarinsa. Sai almajiransa suka yi farin ciki da ganin Ubangiji.

21 Saˈan nan Yesu ya sāke ce musu, “Salama ta kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni haka ni ma na aike ku.”

22 Da ya faɗa haka sai ya hura musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.

23 Duk wanda kuka gafarta masa zunubai, to, an gafarta masa ke nan, kuma duk wanda ba ku gafarta ba, to, ba a gafarta masa ba ke nan.”

24 Toma kuwa, ɗaya daga cikin sha biyun nan, wanda ake ce da shi ˈYan Biyu, ba ya nan tare da su a lokacin da Yesu ya zo.

25 Sai sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji.” Amma Toma ya ce musu, “In ban ga ramin ƙusoshin a hannuwansa, in sa yatsata a ramin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a gefen haƙarƙarinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”

26 Bayan kwana takwas almajiran suna tare a gidan, kuma Toma yana tare da su. Ƙofofi suna kulle, amma Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama ta kasance tare da ku.”

27 Saˈan nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan, ka dubi hannuwana. Miƙo hannuwanka ka sa a gefen haƙarƙarina. Ka daina shakka, ka ba da gaskiya.”

28 Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina, da Allahna kuma!”

29 Yesu ya ce masa, “Ai, don ka gan ni ne shi ya sa ka ba da gaskiya. Masu albarka ne waɗanda suka ba da gaskiya ba tare da sun gan ni ba.”

30 Yesu ya yi alamun ban mamaki da yawa a idanun almajiransa waɗanda ba a rubuta a wannan littafi ba.

31 Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya cewa Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah. Saˈan nan kuma, ta wurin ba da gaskiya ku sami rai a cikin sunansa.

Open Bible reader