Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 13

1 Ana nan tun kafin Bikin Ƙetarewa yă yi, Yesu kuwa ya riga ya sani cewa lokacinsa ya yi da zai bar wannan duniya yă koma wurin Uba. Da yake Yesu ya ƙaunaci mutanensa da suke a duniya, ya kuma nuna musu ƙaunarsa har zuwa ƙarshe.

2 A lokacin da Yesu da almajiransa suke cin abincin dare, Shaiɗan kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuda Iskariyoti ɗan Siman yă bashe Yesu.

3 Yesu kuma ya san cewa Uban ya sa dukan kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma.

4 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya tashi ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗauko tawul ya ɗaura kewaye da jikinsa.

5 Saˈan nan ya zuba ruwa a kwano, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana share ƙafafunsu da tawul wanda ya ɗaura kewaye da jikinsa.

6 Sai Yesu ya zo wurin Bitrus. Bitrus kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, kai ne za ka wanke mini ƙafa?”

7 Yesu ya amsa masa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka gane.”

8 Sai Bitrus ya ce masa, “Sam! Ba za ka taɓa wanke mini ƙafa ba.” Yesu ya amsa masa ya ce, “To, in ban wanke maka ba, ba ka da rabo a wurina.”

9 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai za ka wanke ba, amma ka wanke har da hannuwana da kaina ma.”

10 Sai Yesu ya ce, “Bayan da mutum ya yi wanka, jikinsa ya tsabtace ke nan. Ba ya bukata wanka kuma sai dai yă wanke ƙafafunsa kawai. Gama kuna da tsabta, amma ba dukanku ba.”

11 Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne kuna da tsabta ba.”

12 Bayan da ya wanke ƙafafunsu, ya sāke sa rigarsa, sai ya koma wajen zamansa ya zauna. Sai ya tambaye su ya ce, “Kun gane abin da na yi muku?

13 Kuna ce da ni Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, domin haka nake.

14 Tun da yake ni da nake Ubangijinku da Malaminku na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma ya kamata ku wanke wa juna.

15 Gama na nuna muku misali ne domin ku ma ku yi yadda na yi muku.

16 Hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin maigidansa, ɗan aika kuma ba ya fin wanda ya aike shi.

17 Yanzu da kun san waɗannan abubuwa za ku zama masu albarka idan kun yi su.

18 “Ba a kanku duka nake magana ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa domin a cika abin da yake a cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tayar mini.’

19 Ina gaya muku wannan ne yanzu kafin yă faru, domin lokacin da ya faru ku ba da gaskiya cewa ni ne shi.

20 Hakika, ina gaya muku, wanda ya karɓi duk wanda na aika da zuciya ɗaya, ya karɓe ni ne. Wanda kuma ya karɓe ni da zuciya ɗaya, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.”

21 Bayan da Yesu ya yi wannan magana, abin ya dame shi sosai a zuciya. Sai ya faɗa a fili cewa, “Gaskiya, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22 Sai almajiransa suka duddubi juna, don ba su san almajirin da Yesu yake magana a kansa ba.

23 Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana zaune kurkusa da Yesu.

24 Sai Bitrus ya yi masa magana da alamar hannu cewa yă tambayi Yesu yă gaya musu wanda yake magana a kansa.

25 Sai almajirin nan ya matso kusa da Yesu ya tambaye shi ya ce, “Wane ne shi Ubangiji?”

26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Zan tsoma gutsurin burodin nan a kwano. Wanda na ba shi, shi ne mutumin.” Da Yesu ya ɗauki gutsurin burodin ya tsoma, sai ya ba Yahuda ɗan Siman Iskariyoti.

27 Da ya karɓi gutsurin burodin sai Shaiɗan ya shiga cikinsa nan da nan. Sai Yesu ya ce wa Yahuda, “Abin nan da za ka yi, ka yi shi da sauri.”

28 Amma cikin waɗanda suke cin abincin, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.

29 Tun da Yahuda ne yake riƙe da jakar kuɗinsu, sai waɗansu daga cikin almajiran suka yi tsammani Yesu yana faɗa masa yă sayo abin da ake bukata a bikin ne, ko kuma ya ba talakawa wani abu.

30 Shi kuwa da ya karɓi gutsurin burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.

31 Bayan da Yahuda ya fita, Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa.

32 Idan Allah ya karɓi ɗaukaka ta wurinsa, to, Allah zai ba Ɗan ɗaukaka ta wurin kansa, nan da nan kuwa zai sami ɗaukaka.

33 “Ya ku ˈyaˈyana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.

34 “Sabon umarni nake ba ku, ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna.

35 Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”

36 Siman Bitrus ya tambayi Yesu ya ce, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.”

37 Sai Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”

38 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musūn sanina sau uku.”

Open Bible reader