Hausa Bible
Ibraniyawa 6
1 Saboda haka, bari mu ci gaba a kan koyarwar nan ta farko wadda muka karɓa game da Almasihu, domin mu zama masu cikakken ganewa. Kada yă zama cewa har yanzu muna kafa tushen koyarwa a kan ba da gaskiya ga Allah, da ta tuba daga ayyukan da za su kai ga mutuwa,
2 da koyarwa a kan baftisma, da ta sa hannun albarka, da ta tashin matattu, da ta shariˈar ranar ƙarshe.
3 Ci gaba kam za mu yi, idan Allah ya yarda.
4 Gama waɗanda suka juya baya daga bangaskiyarsu, ba zai yiwu a sāke jawo su ga tuba ba. Waɗanda dai an taɓa kawo su cikin hasken Allah, sun ɗanɗana baye-baye irin na sama, sun sami rabonsu cikin Ruhu Mai Tsarki,
5 sun kuma ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikon zamani mai zuwa.
6 Duk da haka, sun juya baya daga bangaskiyarsu! Ba zai yiwu a sāke jawo su ga tuba ba, tun da yake suna sāke gicciye Ɗan Allah ne, suna kuwa ba shi kunya a fili.
7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yakan fāɗi a kanta kullum, tana kuma ba da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda suke nomanta, wannan ƙasa ce mai karɓar albarkar Allah.
8 Amma idan ƙasa tana fitar da ƙaya da muguwar ciyawa, ba ta da amfani ke nan. Wannan ƙasa kuwa Allah ya kusa yă laˈanta ta. A ƙarshe kuma ƙone ta za a yi.
9 ˈYanˈuwanmu ƙaunatattu, ko da yake muna yin irin wannan magana, ba mu da shakka a kan cewa ku kam kuna a kan hanya mafi kyau wadda za ta kai ku ga ceto.
10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa saˈad da kuke taimakon tsarkaka ba, kamar yadda kuke yi har yanzu.
11 Muna so kowannenku yă ci gaba da yin ƙwazo haka har zuwa ƙarshe, domin ku sami cikawar abubuwan nan da kuka sa zuciya a kansu.
12 Kada ku zama masu ƙyuya, amma ku bi misalin waɗanda suka ba da gaskiya, suka yi haƙuri har suka karɓi abin da Allah ya yi alkawari zai ba su.
13 Saˈad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, ya yi alkawarinsa tare da rantsuwa. Ya yi rantsuwar da Sunansa tun da yake ba wanin da ya fi Allah girma da Allah zai rantse da shi.
14 Allah ya ce, “Hakika, zan sa maka albarka, zan kuma sa zuriyarka ta zama mai yawa sosai.”
15 Bayan da Ibrahim ya jimre da haƙuri sosai, sai ya karɓi abin da aka yi masa alkawari.
16 Mutane sukan yi rantsuwa ne bisa ga wanda ya fi su girma. Rantsuwar kuwa takan tabbatar da alkawarin ta wurin hana yin musū.
17 Haka kuma, da Allah ya so yă nuna wa waɗanda za su gāji alkawarinsa cewa, ba shakka, nufinsa marar canjawa ne, sai ya tabbatar da alkawarinsa ta wurin rantsuwa.
18 To, akwai abubuwan nan guda biyu waɗanda suke marar canjawa, waɗanda ba zai yiwu Allah ya yi rashin aminci game da su ba. Da yake wannan abin ƙarfafa zuciya sosai ne gare mu, mu da muka gudu zuwa mafaka, ya kamata mu riƙe abin nan da muka sa zuciya a kai da ƙarfi sosai.
19 Wannan sa zuciyar nan tamu tabbatacciya ce mai tsayar da hankalinmu, ba tare da jin tsoro ko yin shakka ba. Ita ce take shiga ciki-ciki, har bayan babban labulen nan na haikalin sama.
20 Yesu kuwa wanda shi ne na farkon da ya shiga wannan wuri, ya shiga a madadinmu, da yake ya zama Babban Firist na har abada bisa ga tsarin Melkizedek.